66

1K 106 25
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳

Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*


6⃣6⃣


Kallanta kawai ya tsaya yi, shiyanxu ma tsoro take bashi sosai, hannunta yaje ya kama sannan suka fito parlour, suna fitowa sukayi karo da hanifah da haniff suna sallama ah parlourn, ansa musu sukayi sannan suka nemi wuri suka zauna, gaisawa sukayi ah nitse suna tambayansu umma, lafiyanta qalau suka ansasu

"Fita zakuyi nerh?"
Hanifah ta tambaya

"Ba inda zamuje"
Haiydar yabata ansa sannan yatashi yaje ya kawo musu abunsha, yana ajjewa yatashi yanufi d'akinshi kaman zeyi wani abun, yayi hakanne dan yabasu wuri, hanifah data saba da shegen tsokananta saita kalli shukuriyya tache

"Kinga yanda kika rame kuwa? Kaman wani skeleton wallahi, anya kina chin abinchin kuwa? Kaii ya shukuriyya gaskiya ki daure kiyi qiba tunda kin warke"

Chikin sigar zolaya tayi maganan tunda daman sunriga sunsaba tun agida, kullum hirarsu baya wuche na qiba, batasan chewar yanzu shukuriyya ta riga ta chanja bah, sam bata gane kalmar wasa, yanzu se tayi fushi ta fara sababin masifah, hakanche kuwa ta faru dan aqufule ta d'ago ta kalli hanifah kafin ta galla mata harara

"Ubanwa kike gayawa haka? Nache dan ubanki ni sa'arki che ehh!!?"

Chikin ihu take mata maganar,daga hanifah har haniff saida kowa yasha jinin jikinshi, kasa chemata komai tayi saima kallan kallo dasuka koma sunayi itada haniff, tsaki ta buga sannan ta tashi tabar parlourn tana sababin masifah, taje wuchewa ta wurin centre table dinsu unknowingly hannunta ya daki glass cup d'inda yake kan wurin, aikuwa yafad'i qasa yafashe awurin

"Kutumar uba, wani d'an banzanne ya ajje wannan cup d'in anan"

Tafad'a chikin ihu tanayin kansu kaman zata dakesu, daidai lokachin haiydar yafito daga d'akinshi dan tundaga chan yake jin masifarta

"Lafiyanki kuwa shukuriyya"
Yafad'a yana juyoda ita daga side d'insu

"Dallah Ni chikani, kaga nayi maka kama da mahaukachiya nerh?"

Ta fad'a a qufule tanayin kanshi kaman zata bugeshi, sauri yayi ya saketa sannan yad'an ja da bayanshi gefe

"Shukuriyya!!!"
Yakira sunanta ahankali

"Karka qara kiran sunana awurin nan aikin banza kawai"

Shiru kowa yayi awurin yana kallan ikon Allah, ahankali haniff ya zunguri mayafin hanifah sannan ya d'aga mata gira alamar su gudu kawai, ajje ledan hannunsu sukayi sannan suka miqe atare sukayi hanyar qofah dasaurinsu kaman wasu marasa gaskiya batareda sunche uffan bah

"Gidan ubanwa zakuje batareda kun share wannan broken glasses dinba"

Chak suka tsaya saboda yanda ihun maganarta ya ratsa kunnensu, da sauri hanifah tayi hanyar kitchen dan d'auko tsintsiya amma sai haiydar ya dakatar da ita

"Barshi hanifah kuyi tafiyanku kawai za'a share"

Chikin lumana yayi maganar yana dariyar yaqe

"Kaizaka share kenan"
Shukuriyya tafad'a tana harararshi

"Eh"
Ya ansata ah taqaiche

Juyawa hanifah tayi da sauri tabar parlourn, lokachi d'aya suka fita daka gidan kaman walqiya itada haniff, suna fita ko wannensu yayi ajiyan zuchiya, batareda sunche komai ba suka tari napep suka che yamaidasu gida, saida suka fara tafiya sannan suka fara mayarda yanda akayi, ita hanifah sai dariya takeyi tana kwaikwayan masifan shukuriyya d'in,

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now