93: "best siblings"

994 72 18
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳

Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH

9⃣3⃣

Aikua hakanche ta faru, dan saida su Abba suka dawo akaje gidansu Sophie akayi maganar aurensu tukunna shukuriyya ta yarda zata bar KD, harda su abuu da abiii akaje akayi fixing date din, wata d'aya sukaso asaka kaman yanda shukuriyya tache amma sai gidansu Sophien sukache abarshi zuwa two months kawai, hakanan sukayi concluding akache ranar daurin aure ya kama 30th December kenan, bayan sun dawo daka saka ranar shukuriyya tabi su abuu suka koma kano, achewarta koda bata dawo anan kusa ba zata aiko musu da kayan daza su saka ah bikin, dan chewa umma tayi ko mayafi karta siya, zata siya musu komai daga Kano na bikin wanda zasu saka, inyaso saita aiko dashi, itakuma saita biyo kayan daka baya, achewarta tun biki saura sati d'aya zata taho KD, daga haka sukayi sallama da kowa suka tafi......

Tunda ta tafi gidan yazama so silent, sati dayan datayi saiya musu kamar ta dawo gidanne da zama, they're badly missing her, memories dinda suka samu na wannan lokachin sundade basu samu kamar shiba

"Ya shukuriyya is the best!! I want to be like her"

Shine abunda hanifah take yawan maimaitawa duk seconds idan ta tuna wani abun na shukuriyya....

Shukuriyya bayan ta koma Kano ta sanar da siblings d'inta komai gameda saka ranar mashkur, kowa saida yayi hamdala dajin labarin, domin shukuriyya tuntuni ta damesu da maganar auren mashkur d'in, saika rantse irin yakai 40 dinnan nerh beyi aure bah, achewarta ana gamawa dana mashkur saura nasu, sudai dariya kawai suka dunga mata, suna ganin sufah aure ba yanzu ba tukunna,,, zarah che tache

"To aike wannan date din da akayi fixing beyi ba kenan indai hakane, saboda am very sure indai baki haihu ba lokachin to kin kusa, kokuma dai yazama baki dad'e da haihuwa bah"

"It doesn't matter zarah!! Raban wani baya hana na wani zuwa, kinga idan hakan yafaru ma aimu dadi zamuji, rabo biyu ah lokachi d'aya, koya kukache"

"Hakane kam"
Suka had'a baki wurin fad'a, haka dai suka chigaba da hirarsu har kowa ya watse

The next day shukuriyya na tareda ummi ah parlour tana tayata tsinke zogalai, shukuriyya tache

"Ummi!! Daman I suggest in hadawa ya mashkur lefe nerh, koya kika gani?"
Ta tambaya

"It's a very nice idea shukuriyya, nima nayi tunanin hakan, if that is the case zanyiwa abuu dinki magana, saiya bada kudi aje asiyo, in yaso sai ah kai mishi, kinga banasan kidunga zirga zirga dayawa"

"Shikenan ummi! Nagode"

Shukuriyya tafad'a tana gyara zamanta, daidai lokachin usiii yashigo parlourn, sannu da jiki ya mata sannan ya kar6i zogalan ah hannunta ya chigaba da gyarawa, ummi che take fad'a mishi suggestions dinda shukuriyya tayi, shima backing din maganar yayi, harma yake chewa basai an tambayi abuu kudi bah, shi zai bata kudi idan yaso sai aje asiyo kawai, sosai shukuriyya taji dad'in zanchen usiii, tasan idan yafi hakane ma ze iya yimata, tasani tunba yau ba kuma bawai dan ze bata kudi bah, yana daga chikin mutanen dasuke matuqar qaunarta ah duniya, shiyasa itama take ji dashi.....

Nan take dai ummi da usiii suka gama lissafin kudin lefe, dan haka usiii yache zai kawowa ummi 2M idan yaso sai taje ta siyo kawai, haka dai suka gama magana akan the next day zaije ya kawo kudin....


Akwatunan lefe fal da kaya achiki haka aka jeresu ah parlourn ummi, gobe suke tunanin za'a kaisu KD, daman shukuriyya tayi waya da mashkur tache karya siya kayan lefe ya jinkirta tukunna, yau almost two weeks kenan da akayi fixing date dinsu, that was 6weeks to their wedding, kowa sai sambarka yakeyi da lefen, lefen yagama hadewa to the core, haiydar nerh ya radawa shukuriyya magana ah kunnenta wanda ya sakata yin dariya sosai, shima dariyar ya dunga yi awurin fiyeda ma yanda takeyi, kallansu kowa yakeyi awurin alamar tambaya, nanfa haiydar yafara basu labarin lefen dayayiwa shukuriyya dakuma yanda kayan suke, kowa awurin saida yayi dariya me chikeda tausayi, tabbas haiydar yasha wahala, bayan ma sun tsagaita da dariyar nerh shukuriyya take basu labarin yanda mashkur ya chika mata akwati da kayan sawa masu tsada, sannan yakaiwa Teller ya dunka mata wasu kayan wanda aka kaita gidan mijinta dasu, harma take sanar dasu chewar asalin kayan lefenshi nerh yafara tarawa, sai kawai ya d'auka duka ya bata, tundaga lokachin kuma be qara ajje komai na lefen nashi bahh...

Jikin kowa yayi sanyi awurin, sosai kuma ah fili suka fahimchi irin qaunar da mashkur yayiwa shukuriyya dakuma irin yarda ya kula da ita dakuma rayuwarta, tabbas kome zasuyi bazasu ta6a biyanshi bah.....

Bayan doguwar hirarsu aka rufe akwatunan aka barsu ah wurin, da nufin washe gari zasu kaisu KD, amma banda shukuriyya za'a je, abuu yache ta zauna dai agida tukunna ta rage up and down......

Da sassafe suka kama hanyar KD sukaje suka kai kaya, sannan suka sanar musu chewar shukuriyya che tache ah kawo, mamaki ya ishi kowa awurin, shi mashkur beyi tunanin hakan ba ma, yana zaune yana zuba godiya harda guntun qwallarshi message yashigo wayanshi, shukuriyya che, bud'e message din yayi dan yaga abunda yake chikinshi

Tnk u so much for everything, sakallahu khairan

Yana gama karantawa ya rufe wayar ya mayar aljihu, yakasa samun wadatacchen bakin godiya......

Bayan sun dauki wasu hours achikin gidan suka juyo Kano, da farko ma umma chewa tayi ko za'a kai gidansu Sophien nerh kawai tareda su, sai ummi tache ah ah, abari idan bikin ya rage saura two weeks zasu dawo sai aje akai, that was 4weeks to come kenan, ahaka sukabar zanchen suka dawo Kano.....

Dinki shukuriyya takeyi babu kama qafan yaro, dashike chikin jikinta yanada girma sai tache ah gwada size d'inta da zarah, tunda size dinsu kusan daya nerh, aikua haka aka mata dinkuna kala goma na fitar bikin, ayanda tache idan aka fara events ko tsayawa baza'ayi ba har sai angaji, yanda tayi nata haka tayiwa hanifah, haka ma sauran y'an gidan qannenta kenan sukayi, shima haniff bata barshi ah baya bah, duk dinkunan dasu usiii sukayi na bikin sai data yi mishi irin nasu, dukda ma usii nerh yake biyan kudin kayan dakuma kudin dinkin, haka ma tayiwa umma laces manya masu tsada wanda zatayi fitar bikin dashi, kaya dai ta dunga dunkawa harda na hauka, tana ganin bikin mashkur ya wuche haka ma awurinsu.....

Ah one month dinda akache xa'a koma akai lefe baqaramun kaya shukuriyya ta dunka bah, tasa an musu turaren kabbasa an ninke an zubasu ah akwati, sai data chika trolley uku da kaya, kayanta, na haniff, hanifah, umma da kuma Abba, harta mayafan dazata yafa dakuma sarqa da dan kunne sai data zuba achikin trolley d'in, nufinta idan bikin yazo ita kadanta zata tafi batareda ta d'auki komai bah, tunda kayanta sun rigata zuwa KD din.










MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now