28

1.4K 88 6
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘




2⃣8⃣



*two dayx later*

_Sunday morning_

Haiydar na hango achikin gidan kaka shida shukuriyya sunata hira abunsu chikin kwanchiyar hankali, kana ganin fuskarsu kasan suna chikin farinchiki, haiydar nerh ya d'ago ya kalli fuskar shukuriyya sannan yache

_"Idan nache xan aureki xaki iya aurena ?"_

Tamkar saukar aradu haka shukuriyya taji saukar maganar haiydar ah kunnenta, saboda bata tab'a tunanin xai fad'a mata maganar bah alokachin, har chikin zuchiyarta ta dad'e da fahimtar chewar tanasan haiydar, kuma ta dad'e tana mafarkin yache yana Santa, saidai fad'amata d'un dayayi yau saitaji maganar batazo mata ayarda take tunani bah, hawaye masu zafi nerh suka fara zubo mata ah qunchinta, wanda suke d'auke da manufofi da dama, kasa mashi magana tayi, saima kukan data chigaba dayi, kallanta yayi chikin son gano dalilin kukan nata, tunani yakeyi ah ranshi ba'ta so nane, kokuwa tana kallon maganata ah matsayin raini nerh, kokuwa dai tana ganin tafi qarfina nerh shiyasa take yin kukan, duk wannan tunanin ahchikin xuchiyarsa yakeyi, amma ah fili sai ya dubeta yache

"Menene abun kuka shukuriyya?, nima nasan chewar nibah tsaranki bane bah, amma banida za6i nerh, shiyasa kikaga nafad'a miki, ban fad'a da nufin raini bah, saidai sonki yayimun yawa achikin zuchiyata, harbana iya motsi batareda najiki ah chikin tunani nah bah, ki duba lamarina dan Allah, ina matuqar sanki, kuma aurenki xanyi, xan riqeki da amana, kiyarda dani, arziqi nufin Allah nerh, idan Allah yayi nufin azurtani zayyi hakan daga baya, keda kanki kinsan chewar zafin nema baya kawo samu, da hakan tana faruwa da tuni na dade dayin arziqi, xan baki lokachi kiyi tinani, amma kafin tunaninki inaso kituna chewa ni marayan Allah nerh, kidaure kishigo chikin rayuwata, la'allah kisamu daman cheton rayuwar maraya, kisamu ladan da wasu suka kasa samu, banta6a jin son wata ah zuchiyata bah sai ah kanki, kiduba lamurana dan Allah,"

Yana gama fad'in haka ya miqe yayi waje, yayinda shukuriyya ta miqe ah sulale jiki babu qwari ta nufi dakinta, kaka dake tsaye ajikin window ta koma ta zauna akan katifarta, bayan ta gamajin zanchen haiydar achikin kunnenta, tausayin yaran nerh yaqara rufeta, ah lokachi d'aya kuma tana mejin tausayin jikartata, tunanin maganar haiydar d'in takeyi, ko kadan bashida abun daxa'a qishi, kuma duk maganarsa gaskiya che achikinta, ko wache uwa xataso ache 'yarta ta dache da mijin kwarai irin haiydar, saidai tasan ba lallai shukuriyya taso haiydar bah, saboda shid'in yakasanche mutumin qauye nerh, tunani kala-kala kaka ta dunga yi ah ranta, tana me matuqar jin tausayin yarda suka tsinchi rayuwarsu, kafin daga bisani ta kishingid'a ta kwanta

Ita kuwa shukuriyya tana shiga daki ta kifah kanta akan gado tafara rusa kuka, kukan tausayin kanta kawai takeyi, badaban kartayi sa6o bah, dasai tache rayuwa batayi mata adalchi bah, amma hakan hukunchin Allah nerh, tuno Kamal d'inta kawai tayi, nan take memories d'in suka fara dawo mata, tana tuna lokachin daya furta mata yana santa, tana tuna yanda sukayi Lurv dinsu, da yanda aka rusa mata rayuwarta, da yanda sukayi aure chikin soyayya da kuma yanda mutuwa tayi masu yankan qauna, tana tuna qan-qanin lokachin dasukayi spending ah rayuwar aurensu, tana tsoron kar abubuwan dasuka faru da Kamal d'inta su faru da haiydar, or vise-verser..

"baxan qara aurebah"
Tafad'a ahakali da chusashuyar muryarta, hawaye na zubo mata ah fuska,
"Tabbas baxan qara aurebah, xan rayu ni kad'ai har zuwa sanda tawa mutuwar xata xo ta daukeni, baxan so wani yaji pain d'in danaji bah, baxanso hakan bah"

Taqarasa maganar chikin kuka, yayinda wani irin tari ya sarqafeta, tarin takeyi babuko qaqqautawa, har qasa saida takai saboda azaba, saida kaka dake bacchi kamar achikin mafarki tajiyo tarin nata, shine ta fito da saurinta ta miqo mata maganin dataga tana sha idan tana tarin, sai bayan tasha sannan taji tarin yafara lafa mata, da haka bacchi ya d'auketa awurin....

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now