36

1K 63 0
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘




3⃣6⃣

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah shekaru sun tafi Aliyu haiydar yanada shekaru hudu kenan a duniya, yayi wayo abunshi sosai yayinda mahaifiyarshi nene Allah ya qara azurta ta da samun wani cikin, har yad'an fara fitowa tayarda mutane suna iya ganinshi, wanda befi aqallah wata shida bah.

Ta 6angaren ummi ma Allah ya azurtata da chiki wanda yanxu yakai kimanin wata tara, dan zama da qyar takeyi tashi da qyar, babu wanda yayi tunanin zata kai wannan lokachin ma bata haihu bah.

Saidae duk wannan shekarun mutuniyarku wato Nene tana nan da mugun halinta, ba abunda ya chanja daga kalolin rashin mutuncin da take wa kowa agidan, sai abunda ya ninka na baya mah, kunsan ance daman mai hali sae Allah.

Nene Sam tayi watsi da zaman lafiyar dake familyn hisham, duk wannan shekarun an d'ibesu ne babu jituwa cikin iyalin, bata ragawa kowaba har wanda ya ajiyetan bale wata uwar mijinta, ummi kuwa kusan se muce duk tsanar a kanta ta qare ita da haiydar, a cewar ta shi haiydar ai su ta haifawa, duk wata tsanar duniya da tsangwama ta tattareta akan haiydar, yaron da be San komai ba sae qaunar mahaifiyarshi da bibiyarta, yaro dan shekaru hudu kachal aduniya, idan nene tana qare masa zagi sai kace da wanni babba mai hankalin ta ke.

Mafi yawan lokachi abiii yakanso ganar da ita kuskuren datake aikatawa amma abun ya faskara yana yawan zaunar da ita da nasiha yace

"Kiji tsoran Allah ki sauqaqa wa yaron nan abunda kika dauka kika d'orama kanki dalili ne mara tushe, wannan yaron danki ne bashi da wadda tafi ki, kece uwarsa kuma bazaki ta6a chanja hakan ba."

amma ina!! nene tariga tayi nisa saidai abita da addu'a, lokuta marasa adadi ma idan yana mata maganar ba saurararshi take ba, kokuma ta fara yimishi masifa da rashin kunya kamar ba mijinta ba.....

🌳🌺😘

Haka ce dai take ta faruwa komai sai a hankali achikin gidan, rayuwar babu dad'i, tsantsar jahilci da rufewar ido sun hana nene fahimtar komai, tana sani amma take takewa tana abunda taga dama, har yanzun halin da ake ciki Nene ko wanka bata ta6a yiwa haiydar bah, saidae ummi ta masa, dariya ma wannan ba yi masa take ba, dazarar ya matso kusa da ita zata hankad'ashi da masifa kamar tana qyamarsa, saidae goggo ko ummi su ja shi jiki amman shikam be san dadin uwa ba komae ummi ke masa, wani abun haushin sai yadda haiydar zeyi abu nene ta zage k'wanji ba imani ta makeshi kamar ba yaro dan shekaru hud'u ba, abun babu dad'in gani, amma sai me?, sai haiydar yana bacci daga shi sai ita sai kaga tana shafa shi tana ta kallonsa, sau tari cikin dare zaku same ta a zaune tana kallon d'anta, wani lokutan harda k'wallarta, ba wanda kuma yasan tanayin hakan, koshi haiydar d'in kuwa, uwa da d'a sai Allah.....

_*Ni dai nace a banxa Nene, ki tashi ki rungumi d'anki shine magana....*_

🌳🌺😘

Yau da farar safiya gari be ko gama wayewa ba, banbamin Nene kawai kakeji agidan tana zage-zage a d'aki wai haiydar ya mata fitsarin kwance, haka duk sanyin garin da ake sanadiyyar garin damina ne be hana Nene hankad'a shi waje ba bayan ta gama dukanshi, kasancewar abiii bayanan dan shi idan ya tafi masallaci daga sallar asuba baya dawowa zama yake yayi ta karatu har safiya.
ga fitsarin jikinshi ga kuma sanyin gari ga dukan da yasha amman Nene babu imani ko ruwa bata sa masa ba saima koroshi waje da tayi, haiydar da zafin duka dakuma sanyin gari ya isheshi yazage iya qarfinshi yana kuka, kuka yake sosae yana bin ta tana tafiya, sam be damu da abinda tayi masa ba dan haiydar ya kasance cikin irin yaran nan masu q'ulafucin uwarsu, da abun ya qular da ita sai ta turashi da iya qarfinta ji kuke qumm! Ya bugu da bango ta goshinsa sosai amman ba abunda ya shafe ta kamar ba abunda ya faru, ai kuwa haiydar ya qara zabura da wani kukan wanda yafi wanda yakeyi da qarfi

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now