106 "KULU"

890 62 17
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳


Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH



1⃣0⃣5⃣

"Ke har yanxu bakisan aikinki ba koh?, I wonder how stupid you are, ni dallah matsa daga kusa dani, banza jaka qazama"

"they employ everyone mtsee! Allah wadaran wannan hali"

Sim sim sim me aikin tabar d'akin, ta tsani ma tazo d'akin tunda tazo gidan, gashi ita akasa take kulada d'aki da toilet d'in kulu, ita wannan Abu ya isheta, tunda take aduniya bata ta6a ganin masiffafiyar yarinya me tsiwa irinta ba, wani lokachin harji takeyi ko zata bar aikin nerh, amma idan ta tuna shine madogararta saita haqura, hakanan take jure masifun kulu na kullum, dan kullum setayi mata babu fashi.......

Tashi kulu tayi ta nufi toilet tayi wanka, tana wanka tana ganin dairy d'inda ta karanta jiya ah idanunta, saitake ji kamar yanxu take karan ta shi, komi data karanta dawo mata yakeyi ah kwanyar ta, daqyar ta qarasa wankan ta fito ta shirya, riga da wando ta saka sannan ta fito daga d'akin, dinning table ta wuche wanda yake d'auke da abin Karin kumallo akai, tunda me aikin wurin ta hango kulu ta taho tayi saurin barin gurin da sauri, gudun karta mata masifa, yayinda wadda ke gugar wurin bata kulada itaba hakan yasa bata motsa daka wurin ba, sosai wadda ta tafi ta tausaya mata dan tasan indai kulu ta ganta awurin tata ta qare.....

Itako kulu tana zuwa wurin dining zama tayi Sannan ta dibi abinchi ta zuba ah plate, she's the kind of food first, kome zatayi abinchi nerh ah farko kafin komai, she never greet anyone kafin breakfast, kullum haka take, zata fara chin abinchin kenan ta ajje spoon d'in ta kwashe da dariya, dariya take sosai harda hawaye, uncle d'inta ta tuna from her mother's diary, usiii "uncle usiii" he never say no to food, gashi da San abinchi, da alama shita gado, saida tayi dariya sosai sannan ta chi abinchin tabar gurin.....

Fitarta keda wuya daga wurin ta had'u da me aikin goggo "kakar mahaifinta" ta tsaneta tsantsar tsana, duk chikin masu yi musu hidima tafi tsanarta fiyeda ko wacche, itama me aikin ganinta yasa tayi qoqarin chanja hanya amma ta dakatar da ita

"Ke! ke! ke!"
Ta kirata kamar batasan sunanta ba

Qin juyowa tayi dan batasan fitinar kulu, dan bayau ta fara mata wulaqanchi chikin gidan ba, dukda ma saurin datakeyi bata ankara ba taji kulu ta janyo mata riga ta baya wanda yasa wuyanta shaqewa, ah sukwane ta juyo tana gyara wuyan rigar Tata

"Dan uwarki kinaji ina kiranki kikayi banza dani?"
Kulu ta fad'a ah masife

Ja da baya yarinyar tayi yanda zata daina jin numfashin kulu, dukda ma ba yarinya bache sosai dan ta girmi kulu sosai nesa ba kusa ba

"Kiyi haquri bansan dani kike ba"
Tana gama fad'a tayi sauri ta juya tabar wurin

Kafin ma tayi taku na uku kulu ta qara janyo ta, juyowar daxatayi kulu ta tsinka mata Mari

"Ke kin isa dan uwarki ina magana kina magana, sannan kibar wurin nan batareda na sallameki ba"

Shiru yarinyar tayi tana huchi, tayi niyyar mayar mata da martani amma tuno makomarta yasa tayi Shiru, dan tsaf mahaifin kulu na iya sallamarta daga aiki wanda baxatayi farinchiki da hakan ba, lokachi d'aya hawayen baqin chiki ya wanke mata ido

"Kiyi haquri"
Tafad'a muryarta na rawa, sakinta kulu tayi sannan chikin garagad'i tache

"Karki kuskura ki qara biyowa ta hanyata achikin gidannan, idan kika kuskura muka qara had'uwa baze miki dad'i ba qarshen, banza qazama, get lost"

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now