15

1.6K 90 5
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘



1⃣5⃣


*Washegari*

kasanchewar ta ranar asabar kamal baya zuwa aiki, amma hakan be hana shukuriyya tashi da wuri tayi musu breakfast bah ta tsaftache ko ina, saida tagama komai na aikin gidan tayi wanka sannan taje ta koma bacchi, kamal mah bacchinshi yakeyi kaman babu gobe musamman mah yarda yagaji jiya.

sai wurin qarfe biyu na rana sannan ya tashi daga bacchi, yana farkawa yashiga toilet yayi wanka, yayi shirinsa na gida kamar kullum, gajeran wando da shirt dinsa, sannan yadauko system da wayarshi yafito parlour, ah parlour ya ajje su sannan ya qarasa dakin shukuriyya, yana shiga yaganta ah gefen gado tana bacchi abunta, qarasawa yayi yazauna akan bed side drawer din dakin yana qare mata kallo, kullum kyau take qara masa, ahankali yasa hannunshi yana shafar fuskarta izuwa gashinta, yadade ahaka kafin ta farka, ahankali ta bude idonta ta saukesu akansa, murmushi yasakar mata, ahankali tayi masa murmushin itama sannan ta tashi zaune, toilet ta koma ta qarayin brush ta wanke fuskarta sannan tafito, yana nan inda ta barshi gaisheshi tayi sannan ta zauna ah gefen gadon.

" yau munsha barchi"
chewar shukuriyya

" nasha bacchi dai zakiche"
chewar kamal,
"Dan naga alamar kin tashi kinyi aiki komawa bacchin kikayi, bawai yanxu nerh tashinki na farko bah"

murmushi tayi tache
"ai bawani dadewa nayi bah nakoma bacchin, breakfast kawai na hada mana"
murmushi yayi yache
"toh mungode,,,, yanxu dai tashi muje muyi breakfast din dan yunwa nakeji"

haka suka tafi tare sukayi breakfast din, suna gama breakfast suka tafi compound din gidan...

yaukam banda wasanni babu abunda sukeyi, daman shukuriyya sarkin wasa da yara, babu kalar wasan da bata iyaba wanda yara sukeyi, haka kamal yabiye mata suka dunga wasanni, sun dauki tsahon lokachi suna abu daya, shikam yagama gajiya kawai daurewa yakeyi, kallan shukuriyya kawai yakeyi dan gani yayi kamar an qara mata qarfi, ko alamar gajiya babu atare da ita, neman guri yayi ya zauna akan wani sofah dake kusada qofan shiga parlour din, ganin yazauna nerh yasa shukuriyya ta ankara dashi, da gudunta ta nufo inda yake

" _Yaya yaka zauna kuma?,_ "

"nagaji nerh,,, kixo mu huta"
kamal ya bata ansa, bakinta ta turo gaba sannan tache

"nifah ban gaji bah kwata-kwata, kaxo muyi na qarshe toh saimu tashi,"

ajiyar zuchiya kamal yayi dan yayi matuqar gajiya, yamanta rabanshi dayayi irin wadannan wasannin danshi ko playing ball mah bedameshi bah, bayayi kwata-kwata, dago ido yayi ya kalleta

"wanne nerh na qarshen dazamuyi toh?,"
kamal ya tambaya yana haki saikache wanda yayi gudu

" _Yaya,, gudu zamuyi_ "
Daga wanchan wall din zuwa wanchan wall din"
Ta nuna Wall din da dan yatsan ta
" idan na chinyeka xaka bani gift idan ka chinyeni ni zan baka,"

tafada tana dariya, kallanta kawai yatsaya yanayi yanda take zayyano zanche, "wato bata gaji bah mah kenan, shine take kira masa wani gudu anan wajen,"

gani tayi yaqi magana kuma yaqi tashi ya tsaya yana kallanta, sai kawai takama hannunshi duka biyu tana ja da qarfi, ita ah lallai saita tasheshi daga kan kujerar, dariya ta bashi sosai, ganin yarda ta dage saita dagashi,
da hannunshi data riqe take ja ya fusgota ta fado jikinshi, aikuwa sai gata akan qirjinshi, idonta ah chikin idonshi suna kallan juna numfashinsu yana haduwa , kasa jurewa yanayin nasu tayi sai kawai ta dafa chikinshi da hannunta da niyyar miqewa amma sai yaqara dawoda ita jikinshi tareda qanqameta ajikinshi, lips dinta yakamo yafara tsotsa ahankali, wani irin yanayi yakeji me dadi ah taredashi har wani ajiyar zuchiya yakeyi, itakuwa gaba daya ah takure take, tureshi tafara yunqurinyi amma sam takasa, tuntanayi da qarfinta harta haqura ta gyaleshi, yadade yana mata abu daya harsaida yagaji sannan ya kyaleta, yana sakinta ta tashi dagudu kamar wadda xa'a kama, bata tsaya ah ko ina bah sai chikin dakinta harda saka mukulli sannan tafada kan gado tana mayarda numfashi.

tafi minti talatin ahaka sannan tajiyo kiran sallar maghriba, haka taja jikinta tatafi bandaki, wanka tayi tashirya sannan tayi sallah, sai ah lokachin ta fito parlour, tana fitowa kamal yana shigowa gidan yadawo daga masallachi, qoqarin juyawa takeyi takoma daki, dan kunyar abunda yafaru daxu ah tsakaninsu takeyi,
riqo hannuta yayi da sauri yache

"ina zakije kuma?, yunwa nakeji fah sosai, duk kin rarakemun chiki na saboda guje-gujen dakika sani nayi dazu"
yafada yana dariya...

" _laaa;;;_ Yaya!! namanta ai, ko abinchi fah ban dafa bah,"
tafada tana dariya, ido yabude waje

" mezanchi toh yanxu, saidai in dafaki inchinye kuwa yafada yana dariya, dariyar itama tayi tache
"bari inje indaura mana toh,"

hannun nata yaja yache
"muje intayaki toh,".
yafada yana kwai-kwayar muryarta, dariya sukayi duka sannan suka kama hanyar kitchen din, indomie suka dafa, saboda shi kamal ah lallai fah yunwa yakeji baxai iya tsayawa ah dafa abinchi me wahala bah, haka suka zuba ah plate daya sannan suka dawo parlour suka zauna akan carpet suka fara chi, amma me?, gyememe Kamal yaqi chin abinchin saboda wai daxu dasuna wasa shukuriyya ta tureshi yafadi, saboda haka ya dage mata akan chewar joint din hannunshi chiwo yake yi mishi idan ya daga hannun sama, saboda haka baxai iya chin abinchin bah, saidai ta bashi ah Baki, itakam ta yarda, batasan chewa plan nerh kawai irin na kamal bah, haka shukuriyya ta dunga bashi abinchin harsuka gama chi....

bayan sun gama chi nerh wayar kamal ta fara ringing shukuriyya che taje ta dauko mishi ta miqa masa,
_barrister ahmad_
yagani akan screen din da fara'arshi yadaga wayar
"barrister!!! barister!!!"
Kamal yafada, abunda aka qara fada ah daya bangaren kenan, sukayi dariya gaba dayansu, gaisawa sukayi chikin girmamawa sannan barister ahmad yachewa kamal

"Ku tsammachemu gobe kaida madam din taka, zamuxo nida iyalina inshaAllah,"

kamal yaji dadin maganar zuwansu domin akwai magana mai mahimmanchi dayakeso suyi da barrister din, sallama sukayi sannan kowa ya ajje wayar, juyowa yayi ya kalli shukuriyya yache
" munada baqi gobe fah, wannan abokin nawa nerh barrister ahmad zasuxo shida matarsa gobe idan Allah ya kaimu",

" Allah ya kaimu"
tafada tana dariya

" kinga gobe babu barchin safe kenan,"

" mexai hana barchin safe kuma?," shukuriyya ta tambaya,

"baqin daxamuyi mana,"
ya kwaikwayi muryarta yabata ansa,
dariya tayi tache

" Allah nidai ka daina kwaikwayar muryata,"
tafada chikeda shagwaba,

" shikenan toh zan daina kwaikwayar muryarki",
yaqara kwaikwayarta, dunqule hannuta tayi tamasa dukan wasa ah hannunshi

"Auuuchhh!!!! Zaki qarasa karyamun hannun nawa"
yafada yana riqe hannun kamar gaske, dasauri ta riqe hannun tana yimishi sannu,,,,,

"kasanme Yaya?"
"ah'ah saikin fada"

" gobe din bah, kayi kwanchiyarka kawai kayi bacchinka ni zanji da komai kafin zuwan baqin naka, tinda kaga kai baka fiya samun bacchi bah Indai ba weekend din bah,"

" karkidamu zan tashi intayaki aiki, idan ba haka ba aikin zeyi miki yawa"
chewar kamal

shareshi tayi kaman bata jishi bah sannan tache
" mexa'ah dafa musu toh?,"

"kidafa musu komai kika gadama, komai naki me dadi nerh, "

murmushi tayi dan jin dadin yanda ya yabeta,

" dukda haka Yaya kafadamun abunda kasan yanaso sai in dafa mushi,"

"kimishi moimoi, dan yana Santa sosai, saboda sanda muke makaranta kullum ita yake siya ah cafeteria,"

dariya tayi tache
" kaikuma dambu koh?,"
taqarasa maganar tana dariya, dariyar yayi yache

"wato baki manta bah koh?,"

" yaxa'ai in manta tafada tana dariya, "

"Yaya akwai sanda umman hamza fah tayi dambu aka chinye ba'a ajje maka bah, kadawo daga makaranta kayita fada, har dukan su humaira kayi ranar basuyi maka komai bah, kawai saboda fushin an chinye dambu, "

dariya yayi ya lakache hanchinta yache wato bakya mantuwa koh?, dariya sukayi duka, ahaka suka chiigabada hirarsu har lokachin barchinsu yayi kowa yatafi dakinshi ya kwanta...........




*MEERAH*

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now