30

1.7K 79 5
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘



_This page is wholeheartedly dedicated to u, yeah I mean u!! *cuttieenovels group* y'all know dat I luv u, no need of saying much,,,, keep slaying cutties,, bunch of kisses..._ 😘 😘 😘 😘 😘



3⃣0⃣



Umma da tayi wa abba maganar zuwan haiydar ba qaramun jin dadi abba yayi bah, daman he's eager yaga yaran yaxo ya sameshi, ko mashkur ba'a fad'awa zuwan haiydar bah, saboda har yanxu fushi yakeyi dasu, dan haka suma suka tattarashi suka watsar, ko sabgarshi suka daina shiga suma...

Shukuriyya bayan ta gama waya da hanifah saita rubutawa haiydar text message, kwatanchen gidansu nerh taqara mishi ah message dun, dikda daman already tayimishi ah baya, tana gama rubuta mishi message din saitayi switching phone d'in nata off, saboda ba taso haiydar d'in yakirata, haiydar dake kwanche yaga message d'in shukuriyya, bayan yagama karantawa sai kawai yayi dialing numban nata, but its switch off, yasan zata aikata kashe wayan daman, dan haka sai ya gyara kwanchiyarshi akan matacchiyar katifarsa, yana tunanin yanda tafiyarsa zata kasanche gobe...


Tunda yayi sallar asuba bai koma bacchi bah, wanka yayi sannan ya dauko kayan shi na qasan akwati, kayan da sukafi kowanne kyau achikin kayanshi, wanda sukasha guga sosai yasaka, yadin bawani mai tsada bane bah, kana kallanshi kasan arhache tsuranta, amma kuma duk da haka he looks gued, fitowa yayi yayiwa innarshi sallama sannan yakama hanyar KD.

Ah gidansu shukuriyya kuwa tun asuba dasuka tashi basu koma barchi bah, daman dai haka suka saba, sun tsaftache ko'ina kamar kullum, saidai nayau d'in ya banbanta, hanif da hanifah dakansu suka fita suka share compound d'in gidan, sai zufah sukeyi saboda gajiya, mashkur kuwa yana zaune ah dakinshi yana kallon shige da fichen kowa, jikinshi nerh yabashi lallai akwai abunda yake shirin faruwa agidan, amma ya zuba musu ido yana kallan gudun ruwan su, umma dakanta tad'an had'awa baqon nasu snacks, saida komai ya kammalu sannan mutanen gidan sukayi wanka sukayi breakfast, suka zauna zaman jiran baqonsu.

Tunda shukuriyya ta tashi daga bacchi gabanta yake fad'uwa, jikinta yana bata akwai wani abun daya faru, kokuma yake shirin faruwa, itada kanta tasan tanada baiwar jin abubuwa atattareda ita idan zasu faru, itadai addu'ah kawai tayi Allah yasa koma menene yazo da sauqi, haka ta dunga aikin gidan ah takure har tagama duka sannan tayi wanka taxuba breakfast d'inta tafara chi, kaka dake gefe azaune tana saqarta ta kalli shukuriyya dake chin abinchi tache

"Nasan yanxu haiydar yakai mararraba"

Dariya sosai shukuriyya takeyi, idan zata iya tunawa wannan shine karo na biyar da kaka tayi magana akan tafiyar haiydar tunda gari ya waye, da mintuna kad'an sun qaru saita kintachi wuri tache tasan haiydar yakai wannan gurin, tun abun yana bata haushi harya fara bata dariya

"Menene kuma abun dariya?, akan na fad'i inda yake, ko tantama banayi yanxu yana inda nafad'a"

Murmushi kawai shukuriyya tayi sannan tache
"Allah ya kaishi lafiya"

Dariya kaka tayi sannan tache
"ja'irar yarinya, anaso ana kaiwa kasuwa"

Shiru tayimata ta chigaba dachin abinchinta, dan idan batayi wasa bah zata iya sawa ta shage, ahaka tagama chin abinchin, takai kwanan kitchen sannan tanufi daki ta kwanta, sotakeyi ta kira haiydar taji yana ina, amma tana ganin kamar zeyi tunanin tana zumud'in zuwanshi gidansu nerh, dan haka sai kawai ta qyaleshi zuwa duksanda yakirata d'un.

Haiydar yanashiga garin Kaduna be wuche gidansu shukuriyya bah, saidaya fara zuwa gurin wani abokinshi da sukanyi aiki tare wani lokachin, saboda daman yana yawan zuwa KD shidin, saida yaje yahuta yayi breakfast agidan, sukad'an yi hira da friend d'in nashi sannan yamishi sallama yatafi, batareda ya fad'a mishi abunda yakawoshi garin bah, tunda shid'in daman bamai yawan surutu bane bah.

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now