75: "tragedy"

990 103 7
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*



    Dis page is urs asma'u!! Tnkx for been there always💫

💕💕💕i lurv u so much my followers, words can't express how much u mean to me, more especially WhatsApp fllwrs,,, I Lurv u

7⃣5⃣


            Shukuriyya kezaune akan one seater ah parlourn ta tanata karkad'a qafarta, tun jiya da daddare taketa masifah da bala'i achikin gidan, ta inda tashiga batanan take fita bah, yanayin yanda take masifar ma saika rantse da Allah dukan haiydar zatayi, tun yana zaune yana jinta har yatashi ya koma d'aki, ganin zata biyoshi d'akin yasashi ya kulle da mukulli, saboda zuchiyarshi tafara tunzurashi aikata abunda yake ba daidai bah, shiyasa ma yabar mata wurin, zamanta kenan akan kujerar tana maida numfashin masifar datayi, akan kawai wata ta kira haiydar jiya da daddaren akan maganar ankonsu dasuke siya awurinshi, batareda ta tsaya ta fahimchi wacheche ta kirashi bah kawai ta fara masifu agidan, shikam daya riga yasaba da yanayinta ko kulata beyiba bare yayi qoqarin yimata bayani....

      Wurin sati uku kenan ahaka suke zaune achikin gidan, masifar yau daban na gobe daban, she have changed gaba d'ayanta, he says it saveral times wannan ba shukuriyyan shi bache, shukuriyyan shi is very simple and quite, yarinyar da magana ma be dameta bah, yarinyar da takeda yawan biyayya agareshi, amma yanzu komai ta chanjashi daga halinta, sosai yake bada gudummawar yimata uzuri saboda yana ganin chikin dake jikinta nerh yake sakata fitine-fitinen datakeyi, saboda sukan tattauna matsaloli irin haka da wani makwafchinshi ah kasuwa, mutumin yagirmeshi and yana yawan fad'a mishi yanda mata suke kasanchewa idan sunada juna biyu, harma yasanar dashi yanda kowa take zuwa danata salon, hakan yasa yake mata uzuri sosai.

      Ko shiga harkarta bayayi yanxu sosai, wani lokachin ma sai chan dare idan ya daidaichi tayi bacchi sannan ze shigo chikin gidan, dan kuwa wani lokachin yana shigowa zata fara qirqiro masifu tana mishi, abinchi kuwa an dad'e da shafe babinshi achikin gidan, danshi yamanta rabanda yachi abinchin ta, ita dakanta ma bata dafa wanda zatachi bah bare ta dafa mishi, sauda dama saidai yashiga yadafa mata kafin ta tashi daga bacchi ya ajje mata sannan yayi sauri yabar gidan, na rana nerh dai besan ya takeyi tachi bah, saina dare wani lokachin dayake siyo mata, wani lokachin kua seya dawo sannan ya dafa.....

    Ahaka dai suke tayin rayuwarsu achikin gidan, gashi har ynxu taqi yarda taje taga likita, chikinta yanxu sati na 13 kenan amma taqi yarda suje asibiti, achewarta lafiyarta qalau baze kaita asibiti ya nakastata bah, kafin ma yasamu ta ansashi akan maganar asibitin seya dad'e, ahakan ma baxesamu ansa me dad'i bah.....

        Jin ta daina masifun nata yafahimchi chewar tayi bacchi, ahankali yabud'e qofar d'akin nashi yafito parlourn, tana zaune ah qaramar kujera ta takure jikinta tana bacchi, zuwa yayi yazauna ah kujerar gefenta ahankali sannan yafara tofa mata addu'oi akanta, yadad'e yana mata addu'ah kafin yabari sannan yaja gefe ya jingina da kujerar dayake kai yana qare mata kallo, kaso 80 na zuchiyarshi yana karanta mishi chewar shukuriyya aljanu nerh da ita, wataqila da chan basu bayyana bane, amma ya tabbatar wada zuchiyarshi aljanune ke damunta sosai kuma masu qarfi, da alama aure sukeso suhanata zama....

Yakai minti 30 yana qare mata kallo, ta rame sosai ta koma kamar wata tsinke, saika rantse batachin abinchi, wanda shi shaidane abinchin datake chi yanxu ko'a dachan bata chinshi, ga qurajen dasuka fito mata kullum qara fitowa sukeyi gaba d'aya sun 6ata mata fuska, she's becoming someone different, yanxu ya lura har ah qirjinta da bayanta qurajen suke, tunani yayi yakamata suke suga likita akan qurajen sannan kuma suje wurin malaman ruqiyya, ya dad'e yana wannan tunanin amma ya rasa ta inda ze 6ullo mata, tunda yanxu gaba d'aya bata bashi tym nashi bare suyi wata magana me dad'i, kuma ah yanda take dashi bazata saurareshi ba ko kad'an,,,

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now