61

1K 75 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*




6⃣1⃣

                       
            Suna fitowa suka sami adaidaita sahu abakin titi suka hau, tunda suka fara tafiya bawanda yache komai achikinsu, ta lura bayasan mata magana nerh shiyasa ma ta qyaleshi, tasan sarai saboda taje gidansu humairah yake wannan chin maganin....

     Suna zuwa gida ta fad'a toilet, wanka tayi sannan ta fito ta shirya tayi sallar maghriba dan anyi kira tun suna hanya, tana idarwa taje ta shirya centre table dinsu da flask d'in data zo dashi daka gida, wainar shinkafa che da miyar taushe achikin flask d'in wanda yaji naman kasuwa, tunawa datayi sunada sauran orange ah fridge yasa ta d'auko tayi sauri ta matse mishi tamishi orange juice, dan haiydar akwai san chin abinchi da lemo musamman orange one, saidata ajje sannan ta nufi d'akin nashi danta lura tunda suka dawo be fito bah,,,,,

Da sallamarta tashiga ta sameshi akan abun sallah yana addu'ah, da alama yanzu ya idar da sallar,zama tayi agefen gadon dake d'akin tana jiran ya idar da addu'ar,,,,,,
     Yana idarwa yajuyo ya kalleta, kallan dayayi mata nerh yasa taji wani iri amma dae batache komai bah, tashi yayi yafita daga d'akin sai kawai ta bi bayanshi da kallo, itafah haiydar wani bin seyayi mata kamar me aljanu, tasan dai lafiya lafiya suka rabu yau da safe har yana mata kamar karta fita, meye kuma yake damunshi yanxu? tunani tayi qila bachin ran kasuwa nerh sai kawai ta tashi ta bishi parlourn,,,,

    Azaune tasameshi akan kujerar ya qurawa TV kallo, rashin sanin abun fad'amishi yasa tayi shiru musamman yanda taga yanata shan kunu, abinchin taje ta zuba mishi ah plate da drinks d'in ah cup sannan taja mishi table d'in gabanshi, "bisimillah" ta furta tana kallanshi, beche mata komai bah ya juyo ya fara chin abinchin, ganin yafara chi yasa tafara mishi hira me dad'i kad'an- kad'an, ganin yana responding nata yasa tachigaba, sata yayi lallai ta dawo kusada shi suka chigaba dachin abinchin, aranta tana mamakin hali irinnashi, suna gama chi taqara musu suka chigaba,,, saida suka gama ta kwashe kayan sannan ta wuche d'aki, 20k d'in da hamza yabata ta d'auko ta nuna mishi, ranshi in yayi dubu saida ya6achi, ita da kanta saida taji dama bata nuna mishi bah, ita takasa fahimtar adawar haiydar da mutanen gidansu kamal, at least ai kamal ya riga ya mutu, kishin namenene toh?, dan tasan da wanine yabata sam baxesa kansa akai ba balle yayita masifa, amma hakanan yadunga shiga yana fita yana masifah mara tushe, ganin ranta yana qoqarin 6achi akan masifar dayakeyi yasa ta tashi tabar mishi parlourn,,,,,,

     D'akinta ta nufa tayi kwanchiyarta akan gado, bataso ta sabarwa idanta zubarda hawaye akan haiydar, Allah yasan bataso tayi exceeding hawayenta akan baqin chikin shi, domin mafi yawan hawayen data zubar arayuwarta silar baqin chikin haiydar nerh, so she just feel that to be enough, yakamata tayi reserving tears d'inta, domin akwai very gued day d'inda zaizo wanda zasu mata amfani,,,,,,
  
      Tashi tayi ta nufi toilet tayi alwala sannan ta dawo tayi sallar issha, tana idarwa ta d'auko kayan bacchi tasaka tafeshe jikinta da perfumes masu sanyi as usual sannan tabi lafiyar gado,.....

    Haiydar kuwa ah parlour yachika yayi fam, anashi ganin danme shukuriyya zata tafi ta barshi yana masifa, ai yakamata ta jira yagama sannan ta tafi, kokuma tayita bashi haquri harsai ya haqura kamar yanda ta saba, yadad'e yana jiranta ah parlour yana tunanin zata dawo, ganin baxata dawo d'in bah yasa ya tashi yaje yayi nashi sallar, bayan ya idar yazauna yachigaba da kallanshi ah parlour, sai wurin twelve yagama kallan Indian film dinda yake kallo me taken "TIGER" sannan ya nufi d'akin nata,,,,,

     ganin yanayin bacchin nata yasa ya tabbatar tun shigowarta tayi bacchin, qarasawa kusada ita yayi yana kallan beauty face d'inta, is lyk she even luks more beudiful in tana bacchi, shafa face d'inta yayi ko zata farka amma bata tashiba, hakan yasa ya tabbatar chewar bacchinta yayi nisa, ji yayi kaman jikinta akwai zafi amma bachan sosai bah, sai kawai yayi ignoring, daman chan shi bame damuwa da abubuwa bane, kusada ita yakoma ya kwanta tareda janyota jikinshi sannan ya rufesu da bargo....

     Da safe tun bayan idarda sallar asuba ta koma bacchi, yana dawowa daga masallachi yaganta tana bacchi ba kamar kullum daxaiga ta fara gyaran gida ko shirin yin breakfast bah, hakan yasa yayi tunanin qila har yanxu fushi takeyi dashi, guntun murmushi yayi wanda be kai zuchiya ba sannan ya kwanta gefenta, be farka ba sai wurin 8 na safe, still yaganta tana bacchi, abunma se yaso yabashi dariya, yaukuma tahaka ta 6ullo da fushin nata kenan, tashi yayi yaje yayi wanka yayi shirin fita kasuwa, be iyayin girki ba bare yayi musu, dan haka ruwan tea kawai ya had'a ya sha sannan yayi fichewarshi kasuwa.

      Tunda yatafi kasuwa hankalinshi yana kanta, har wurin azahar hankalinshi yakasa kwanchiya, hakanan yaji hankalinshi be kwanta da barinta dayayi tana bacchi ba, tunawa yayi jiya da daddare jikinta da zafi, se yayi tunanin qila batada lafiya nerh shiyasa taketa bacchi haka, babu shiri ya tashi ya had'a tarkachenshi ya rufe shagon ya nufi gida.......

      Shukuriyya kam tun bayan sallar asuba takejin jiri na d'ibarta hakan yasa takoma bacchi abunta, ga wani zazza6i datakeji achikin qashin jikinta......
    Daqyar wurin qarfe goma ta farka daga bacchin, daman tasan haiydar bazebi takanta bah, so tasan definitely ya tafi kasuwa, daqyar taja jikinta tashiga toilet, wani irin kasala takeji ajikinta da zazza6i, daqyar tayi wanka ta fito daga toilet d'in, ikon Allah nerh kawai yakawota kan gadonta daga toilet d'in, saboda wani irin jiri daya d'ibeta, lokachi d'aya kuma ganinta yad'auke tafara ganin wani irin duhu, tana kwanchiya akan gadon tafara maida numfashi, sai kuma ahankali duhun dake idanta yafara d'aukewa tafara gani kamar da, wani irin zafi takeji ah qashin jikinta gawani irin week da jikinta yayi, yunwa takeji achikin ta kamar zata chi babu amma takasa motsawa daga wurin da take ballantana ta samarwa kanta abunda zatachi, takaichin hakan yasa idanunta suka fara fidda ruwa, kafin wani lokachi kuma bacchi ya d'auketa awurin.

      Yana zuwa gidan yasaka key d'in dake hannushi yabud'e qofan, yana shigowa parlourn yaga yarda yatafi yabarshi haka ya dawo ya sameshi, gabanshi nerh yayi mummunar fad'uwa yanufi d'akinta da sauri, ganinta yayi tana kwanche akan gado qafafunta aqasa, dasuri yaqarasa inda take ya tallafota ta dawo jikinshi sannan yafara kiran sunanta "shukuriyya!! Shukuriyya!!"
Yafad'a yana tapping face d'inta, dagyar ta bud'e idanta ta saukesu akansa, saika rantse giya tasha yanda taketa maye, d'agota yayi ta zauna sosai ajikinshi kafin yace

   "Lafiyanki kuwa?, meke damunki"
Arud'e yayi maganar dan yanxu jikinnata babu zafi

  Bud'e idanta tayi ahankali ta saukesu akanshi, ita batasan ma meyake fad'a bah, all she know is that yunwa takeji, daqyar ta iya bud'e bakinta tache "abinchi"
Ajjeta yayi dasauri yaje ya had'o mata tea yakawo mata, nufinshi abinchin yaxama daka baya, tunda babu enough time d'in da za'a dafa mata indai yunwan takeji kaman yanda tafad'a...

    yana shigowa d'akin yayi kanta da sauri ya d'agata daga kan pillow d'in yazaunar da ita daga gefenshi ya rungumota, tea d'in yafara bata ahankali dan daman saida yazuba ruwan sanyi achiki, ahankali yake qoqarin bata amma tasaka hannuwanta guda biyu ta rarumo cup d'in, dukda chewar daqyar ta d'aga hannayen nata, cup d'in ta tura bakinta tadunga shan tea d'in kamar wadda ta kwana uku bata chi abinchi bah, mamaki yahana haiydar magana saima kallanta dayakeyi, yana ganin ta shanye yaje ya qaro mata, haka tashanyeshi tas tana mishi nuni da hannu alamar yaqaro mata, dukda atsorache yake da yanayin nata amma hakan bai hana yatafi ya qaro mata bah, yana dawowa ya zauna kusada ita ya janyota jikinshi, kafin ma yakai mata cup d'in bakinta tafara mishi amai ajikin shi, haka ta dunga amai har saida ta amayar da tea d'in datasha duka, harda abinchin datachi jiya, azaune tayi aman duka ko yunqurin motsawa takasayi, haiydar sai sannu yakeyi mata harta gama sannan ya d'auketa yakaita toilet yagyara mata jikinta sannan yadawo da ita ya ajje, yana ajjeta ta malale akan gadon ta chigaba da maida numfashi.....

   Wurin ya gyara tsaf sannan yadawo kusada ita yazauna, yarasa me zeyi mata ma gaba d'aya, wani irin numfashi yaji tana fitarwa ahankali wanda yake jin kamar daqyar take fisgoshi, d'agota yayi zaune yajata jikinshi amma se yaji tafara tari, tarin tadungayi wanda takai wurin 30 minutes tanayi amma yaqi tsayawa, gashi daqyar takeyin tarin, Zuma yadauko ya lasa mata abakin nata sannan chikin ikon Allah tarin ya tsaya, doguwan rigar abaya ya d'auko yasaka mata sannan ya kamata suka fita asibiti...

                   🌳🌺😘








*MEERAH*

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now