95: "labour"

878 61 2
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*


9⃣5⃣

Sai bayan fitarsu sannan ummi ta sauko take fad'awa mashkur chewan shukuriyya che batajin dadi gasuchan ma suntafi asibiti, lokachi d'aya hankalin mashkur ya tashi, itama ummi bawai hankalinta yana kwanche bane bah, kawai qarfin hali nerh irin nata

"Toh mubisu asibitin mama ummi!"
Mashkur yafad'a chikin neman izini

"Ai bawai rashin lafiya bane sosai, qila ma yanzu kaga sun dawo"
Ummi ta fad'a tana yaqe

"To ko dai zazza6in datayi nerh be gama warkewa bah?, kokuma dai haihuwa nerh ma?"
Chewan mashkur

"Bari suje asibitin nasan zasu kira ae, amma bana tunanin haihuwa nerh ma, qila dai zazza6in"
Ummi tafad'a tana zama ah kujera

Hankalinta Sam ba'a kwanche yakeba, but she keep pretending as usual, daman ita haka take, aranta kuwa tunani takeyi abunda yafaru, daga chewa Nene babu lafiya se ah tafi asibiti, badai rashin lafiyanta nerh ya motsa bah?, tunani kala kala ummi keyi achikin zuchiyarta, kukan zuchi kawai takeyi dan zuchiyarta namata saqe-saqe da yawa........

🌳🌺😘

Sai bayan wurin 30minutes sannan Nene ta kira ummi ah waya, ummi da tun daxu take jira ah kirata tayi karaf ta d'aga...

"Ummi!"
Nene ta kira sunanta

"Na'am!"
Ummi ta ansa chikin qarfin hali da dakewar zuchiya, dan ji takeyi kaman zuchiyanta ze fashe

"Sun kwantar da ita nerh fah, sunche ma haihuwa nerh, kikawo akwatin haihuwanta"
Nene ta fad'a chikin sanyi sannan tayi hanging

Dukda muryarta be nuna alamun akwai matsala ba saida ummi ta tsorata

"haihuwa kuma wani iri? Thought EDD d'inta bema kusa zuwa bah?"

Ummi ta fad'a ah fili thinking that ah zuchiyanta tayi maganar, Mashkur da tunda ta d'aga wayan yake kallanta ya fahimchi inda maganan ya dosa, dasauri yache

"Ummi mu tafi mana"

Shine ma yadawo da ita daga tunanin da take, da sauri tayi dialing numban haiydar danjin inda akwatin nata yake, dan itache ta had'a mata kayan da kanta watarana ta kai mata, sannan tache ta zubasu achikin akwati chikin akwatunan datake dasu, to her suprise se haiydar yache mata ai kayan suna nan chikin cupboard d'inta, batama sakasu achikin trolley dinba, dashike ya fad'a mata inda kayan suke sai kawai ummi tayi hanging call din ta hau sama ta nufi d'akin ta, trolley ta d'auko nata sannan ta nufi side dinsu haiydar d'in, tana zuwa ta duba inda ya fad'a saiga kaya ah zube ah wurin, mamakin shukuriyya nerh ya ishi ummi sosai, tas fa ta had'a kayan biki da kuma na zaman jego da zatayi, harma tasa ankaisu KD an ajje, amma bata had'a kayan dazataje haihuwa dasu bah, wani bin shirmen shukuriyya haushi yake bata, although halayen nata sound childish ah times......

Tana gama zubawa ta janyo trolley d'in ta fito, tana zagayowa compound mashkur ya kar6i trolley d'in yasaka ah motanshi sannan ya shiga ya tayar suka fita, suna fita ummi ta fad'a mishi asibitin dan haka suka wuche kai tsaye.

isarsu suka tarar har an shigar da ita labour room, dashike ah asibitin take awo ba wani problems dasuka samu, kuma sunada duk wani records na rashin lafiyarta, so tuntuni suka fara tackling duk wani abu dasuke zatan ze iya zame musu matsala.....

Hankalinsu duka ba'a kwanche yake bah, daga ummi har Nene sun manta sukira abuu ko abiii su sanar dashi halin da ake chiki, addu'ah duka su hudum da suke asibitin sukeyi, kallo d'aya zaka musu kasan sunachikin damuwa, ita ummi abun mamaki yake bata sosai, ah lissafin da takeyi ma yau aqalla saura kwana 20 EDD d'inta

"how's dis possible?, to kodai juyi yaran yayi doctors d'in suka zata haihuwa che?, but that wouldn't be possible, sunsan aikinsu kuma sunsan komi akai, she's suprise and she can't still believe it, Allah yasa kar shukuriyya ta d'auko dogon naquda irin nawa, Allah yabata sauqin naquda irinta Nene, Allah ka sauqaqa mata"

Addu'ah da zanchen zuchin da ummi take tayi kenan, she know who she is, indai shukuriyya tayi gadan naqudarta to lallai zata sha matuqar wahala, dan saitayi kwana 15-20 tana naquda, kuma bata ta6a haihuwa kafin EDD d'inta ba, ko yaushe sai EDD d'inta yawuche sosai sannan take haihuwa, tabbas tana matuqar shan wahala wurin naquda, bata fatan shukuriyya tasamu wannan naqudar........

Tunani ummi takeyi same time din, tunanin kuwa be wuche anya ma shukuriyya tana shan rubutun da adduoin da ake bata kuwa, tunda abun be damunta musamman ma dataga chewan akwai sauran lokachi sosai, amma yanzu duk hankalinta ya tashi, addu'ah kawai takeyi tana sunbatu.....

Ah 6angaren haiydar yana chan yana addu'ah shima harda nafila, shidai tunda yake ba'a ta6a haihuwa kokuma wani abu makanchin haka akusa dashi bah, saboda haka shi besan ya wahala ko sauqin abun yakeba, amma tunda akache mishi haihuwa che yaji gabanshi yayi mummunar fad'uwa, saboda ya halarchi jana'iza da dama ah gida sanda yake KT, kuma jana'izar mata dayawa daya halarta akanche mishi wurin haihuwa nerh suka rasa ransu, hakan yasa duk hankalinshi yatashi, yayi sujjada ma besan sanda zuchiyarshi ta narke yafara zubarda hawaye bah, tuno rasuwar wata qaramar yarinya da yayi wadda ta mutu wajen haihuwa batareda ta haifi yaran bah, akaje aka chire yaran shima ya mutu, abunda yafad'o mishi kenan aranshi har yasashi kuka, baya tunanin ze iya ganin gawar shukuriyya, baze iya jana'izar mutuwarta bah, bayaso ta mutu, she owes him a lot

"innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah ka sauketa lafiya, Allah ka bata tsahon rai me amfani, ya Allah ka rayata da abunda zata haifa, ya Allah kaxama gatana, banida wani farinchiki daya wuche kasanchewa tareda wannan baiwar taka, ya Allah ka sauqaqa mata "

Sumbatu da adduoin dayakeyi kenan tunda sukazo, duk chikinsu babu wanda yakeda nutsuwar dazai gane halinda wani yake chiki ballantana ya rarrasheshi, daqyar ma ummi Allah yasa mata nutsuwar kiran abuu ah waya ta sanar dashi, wayarta ta zaro chikin jaka ahankali zatayi dialing numbanshi, saiga kiranshi nanma ya shigo phone d'inta

"Lafiya kuwa? Kuna ina nerh? Ina shukuriyya?"

Abuu ya tambaya daidai lokachin da yaji ummi tayi picking

Shigowarsu gidan kenan suka tarar babu kowa ah gidan se masu aiki, which is not common ah gidan, bcous hardly indai bawani dalili me qarfi ba kokuma bawai sunyi tafiya nerh dukansu bah gidan yazama empty, kuma ya tambayi gate man yafad'a mishi yanda mutanen gidan suka fiche d'aya bayan d'aya, hakan yasa jikinshi yabashi babu lafiya, shiyasa yayi saurin kiranta....

"Toh!! Shukuriyya che dai ba lafiya, munzo asibiti sunche haihuwa nerh, tundaxu ma suka ....."

"Wani asibiti?"
abuu ya tambaya eagerly saboda baze iya jira ta qarasa hirar ta ba

Tana fad'a mishi asibitin ya fad'awa abiii abunda sukache sannan suka juya suka bar gidan batareda sun sanar da goggo halin da ake chiki bah, dashike ta riga ta shige side inta ita.









MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now