23

1.6K 85 2
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘




2⃣3⃣


Suna shiga chikin gidan shukuriyya ta gudu daki abunta, dan tasan sababin masifar kaka, idan ta fara ko saurarawa batayi, aikuwa kaman ta sani, dan kaka nashiga tahauta da masifah, wai tana zaune lafiya abunta amma tazo ta tayar mata da hankali, itadai shukuriyya tanajinta amma saitayi shiru kaman ruwa ya chinyeta, dan tasan idan tayi magana yanzu kamar ta qarawa wutar fetur nerh, haka kaka tayita mita har saida taji kiran sallar maghribah sannan ta saurara.


🌳🌺😘

Shukuriyya che zaune da kaka bayan anyi sallahr isha'i, haquri tabawa kaka sannan tache inshaAllah baxata qaraba, dariya kaka tayi tache babu komi takwara, daxun mah dokin fushi nahau, amma nasan ked'in bamai qiriniya bache bah ai, abinchi shukuriyya ta zubo musu, sunachi suna d'an ta6a hirar duniya,
acikin hirar ne mah take tambayar kaka

"'yawwa kaka dama kinsan wannan mutumin daya kawoni gida d'azu naga har kin fad'i sunansa ma?'"

"ohho haiydar !"
kaka tafad'a tana d'an murmushi

'"nasanshi ai, tunda dadewa, tun yana qaramunshi kuwa, mutumin arziqi ne ae, kowa yana yabonshi ah unguwa, ba ruwanshi da shiga sabgar shirme, gashi akwai qoqarin neman nakansa, har nan yake zuwa ya gaishe ni, akwai hali mae kyau kam babu laifi, gyatumarsa ma qawata ce, mutuniyar arziqi da ita, takan aikoshi gurina lokaci xuwa lokaci."

Kaka taqarasa maganar tana murmusawa....

Tana fad'in haka shukriyya ta kwashe da dariya hadda riqe ciki, kawai kaka ta tsaya ta saki baki tana kallonta

'ke lapiya kuwa?'

Dariyar tasamu tad'an tsagaita mata da qyar

"wallahi kaka ya fad'amun da muna tahowa dazu, ashe da gaske ne, qawarki tabb."
Shukuriyya ta qarashe maganar da mamaki

Kawai kaka tsayawa tayi tana kallanta da mamaki, wannan ne abun dariya? kallonta tayi tace

"toh mene ne aciki ?"

'bakomae, tsohuwa che itama kenan ashe.'
Tafada tana cigaba da dariya.

Kaka ma dariyar tasa
'lallae kaji mun 'ya Allah shirya mun ke, dad'in abun yadda muka tsufan haka kowa zai tsufan.'
Duka suka sa dariya.........


🌳🌺😘

Ahaka rayuwa tachigaba da kasanchewa shukuriyya achiki garin katsina, babu laifi tanajin dad'in zaman garin sosai, musamman yanda kaka ke janta ajiki tana sauraron lamuranta, ah lokuta da dama takan kasanche chikin farin chiki da murna, saidai wani lokachin komai nata yakan tsaya chak idan ta tuna past dinta, yan'uwanta, da abokan arziqi, musamman mah margayin mijinta, duk saitaji tana missing dinsu, wani lokachin idan taji tunanin yan'uwanta ya mata yawa, saitaji kaman ta koma Kaduna, amma idan ta tuna chewa ko taje baxataga Kamal bah, kawai saitaga baxata iya komawa bah.

Family dinta suna yawan ziyartarta akai-akai, musamman mah mashkur, dan uwa rabin jiki, koda yaushe yana kan hanyar katsina dan ganin yar'uwarsa, wani lokachinma duk qarshen sati yake zuwa yaganta, ko gajiya bayayi, yana kaimata komai dayasan zata buqata, sannan ya xauna da ita suyi hira, yaji matsalolinta sannan su tattauna akai....

Shikam harga Allah bayasan zaman shukuriyya ah katsina, danshi betab'a mafarkin ache ta koma qauye tana *RAYUWA* bah, though qauyensu kaka bawai qauye bane sosai wanda za'ai gyashin zama ah chikinsa, amma ah fahimtar mashkur qauye-qauyene, saboda haka mah babu yanda beyi iya qoqarinshi bah wajen ganin yayi convincing shukuriyya akan takoma kaduna amma qememe taqi, duk sanda ya ziyarcheta sai yaayi mata maganar, amma ah qarshe mah kuka take sakamasa, shikam bayasan ganin bachin ranta, dan haka ya gyaleta yadaina damunta akan komawa kaduna, amma tabbas dayasan chewar zuwanta katsina bana wuchin gadi bane bah, da baxai barta ta tahobah tun farko.......
Wannan Keenan.........

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now