🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*
0⃣4⃣
Bayan mashkur yashiga daki abba yakalli umma yache
"Umman mashkur yadai?" ( haka yake kiranta yanzu )
tache "abban mashkur babu komai kawai dai naji wani abu araina gameda da abunda mashkur yache, yanzu ache har mashkur yayi wayan dazai fara maganan qanne? duk sai naji babu dadi da bashida su"
Tayi maganan in a low tuneabba yache
"haba umman mashkur, yanzu da bakinki kike fadar wannan maganar? wannan ai ba abun damuwa bane bah, Allah yana sane dake kuma shidaya baki mashkur ai shi zai baki waninsa, wani hanin ga Allah baiwa ne bakisan abunda yatana dar miki bah, kiyi hakuri idan kinada rabo zaki qara samun haihuwa, daga gareni babu matsala kuma banida damuwa, inasanki ah haka kuma mashkur ya isheni rayuwa, nagodewa Allah da yabani shi kema ki gode masa saiya qara miki wani, ni ban isheki ishara bah? nikadai na rayu agidan mu mahaifina yasameni bayan shekarunsa sunja sosai, mukuma Allah yabamu mashkur ah qananin shekaru..."kalamai masu dadi abba yadunga yiwa umma harta kwantar da hankalinta sannan suka wuche daki suka fara hada kayan tafiya katsina dan gobe yakeso su wuche....
Asubar fari suka kama hanya sai katsina, kaka kam tayi murnar zuwansu sai tsokanar mashkur takeyi
" karma kazo inda nake danni nasake kah saki uku bana auran, wannan wani irin miji ne yatafi yabar matarsa sai sati-sati zaidunga zuwa dubata? to kaje na barwa mutanen kaduna"
dariya sukayi gaba dayansu sannan akayi sabuwar gaisuwa ta musamman....
Satinsu biyu ah katsina suka dawo kaduna, Awannan lokachine kuma Allah ya azurtasu da diya mache wadda aka sakamata sunan kaka wato maryam ake kiranta da *shukuriyya* dan suna ganin ita kyautache daga Allah, sunsameta bayan shekara shida babu haihuwa, mashkur kam kusan yafi kowa murna dan yanaganin yasamu qanwa, ko ah Skul dinsu da anfara hira zaiche shima yanada qanwa shukuriyya kuma idan ta girma skull dinnan za'a kawota kuma duk wanda yadaketa sai na rama mata kullum maganar sa kenan,,,,
Rannan ah skull hamza yache indai shukuriyya ta girma saiya mata duka, zokaga tada jijiyoyin wuya gurin mashkur, aikuwa ji kake tas-tas yadauke hamza da mari, kankache me sun rikiche da fada da kyar antynsu ta raba su, ta tambayi dalilin fadan mashkur yache
" chewa yayi saiya zane shukuriyya "
anty tache "ina shukuriyyan?" mashkur yache
"tana gida ae, bata iya tafiya bah, umma che kullum take goyata abayanta idan tana kuka"
sai yanzu antyn mah tagane ashe fada ake akan yarinyar dako magana bata fara bah, dariya antyn tayi sosai dan mashkur ya burgeta sannan ta rabasu tabasu hakuri...
Ahaka rayuwa tachigaba da tafiya domin soyayyar kowa ah gidan ta koma kan shukuriyya, dan wataran da kyar ake banbare mashkur daga jikinta sannan yatafi skull, lokachin da aka saka shukuriyya ah skull kuwa kafarta kafar mashkur, yayita nan-nan da ita, gata da nutsuwa yarinyar batada harigido irinna yara, yarinya kyakkyawa San kowa qin Wanda yarasa, umma kuwa ta hade kan yaranta tanabasu kulawar da ta dache, musamman mah shukuriyya tunda ita macheche....
*6 YEARS LATER*
umma takara haifo santalelen danta mai kama da mashkur ( ni meerah nache umma sai shekara 6 -6 ake haihuwa) murna agidan nan ai ba'a magana, shukuriyya kam kamar ita aka haifawa, bayan kwana bakwai akayi taron suna yaro yachi suna hanif, ah wannan lokachi abba yagama gina sabon gidansa mai kyau achan qasansu kusada gidansu hamza, gidane flat mai kyau babban parlour guda daya sai dakin abba Wanda yake akwai parlour karami achiki da dakinshi da toilet , sai umma itama kofar dakinta yana main parlour shima me toilet achiki, saikuma dayan side din dakin mashkur ne da shukuriyya suma dukda toilet achiki, kuma masu matsaikaitan girmane dakin, sai kitchen ah parlour din shima maidan girma, akwai store achiki, sai compound din gidan yanada dan girma dan abba har motarsa yake ajjewa kuma asamu extra space...
bayan suna suka tare ah sabon gidansu wanchan gidan kuma abba yazuba haya achiki, tunda suka dawo kusada gidan su hamza dawa Allah ya hada? kullum mashkur yana gidan har saida umma ta taka masa burki dan taga yawan nashi yafara yawa, shukuriyya mah takan Shiga lokachi zuwa lokachi gurin qawarta humaira, saidai humairan tafi shigowa gurinta, umma da mamansu humaira kam sun saba dan daman tun kafin sudawo suke amunta da ita sanadin abotar hamza da mashkur
shukuriyya bata da yawo sosai saidai tanada san yara, gatada hankali da nutsuwa gasan tsafta dukda karanchin shekarunta, ko bah komai agurin umma tagani, dan umma gwanache gurin wadannan abubuwa, wannan dalili ne yasa shukuriyya kesan shiga gidansu humaira, dan akwai yara sosai agidan, dan kusan duk bayan shekara biyu mamansu humaira take haihuwa, shukuriyya kam kullum tana goyeda hanif ah bayanta, ko ina zataje dashi take zuwa saidai idan skull zataje, shukuriyya akwaita da shiga rai duk inda tazauna sai an sota, saboda tanada abubuwan da za'a sota, kowani mutum yanasan yaga wanda yakeda tsafta, san yara, uwa uba kokari, bare kuma ache yarinyache tahada wadannan abubuwan, wannan ne yasa take shiga ran kowa, 1st position shine take dauka koda yaushe ah skull...
ana wannan yanayi ne aka aiko wada su umma dan aike daga katsina , chewar kaka babu lafiya kuma jikinta yayi tsanani dan haka suzo, aikuwa babu shiri suka Kama hanya sai katsina.....MEERAH
IG @cuttieemaria
