10

1.8K 101 11
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


dedicated to ayshertee  (nisharpp)

Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘



1⃣0⃣

                  

Sai guraren qarfe daya na rana ta farka daga bacchin, yanayin data tsinchi kanta ne yasa ta tuna da abunda yafaru dazu, guntayen hawaye ne suka zubo mata ah idanunta, jikinta asanyaye ta tashi tashiga toilet tayi brush tayi wanka saboda yanayin da ake chiki na zafine sannan ta dauro alwala tazo tatayarda sallah,,,,. tana chikin yin raka'ar qarshe kamal yashigo dakin, amadadin tayi sallama sai tachigaba da sallar ta, ganin sallar tata ta qi qarewa yasa yatashi yabar dakin, motarshi yadauka yabar gidan...

               🌳🌺😘

gidansu shukuriyya yafara wuchewa yagaishe da iyayenta sannan yashiga gidan umman Kamal yadade agidan sunata hira tanata tsokanarsa amaryarsa, shikuwa sai dariya yakeyi, kafin daga baya yabar gidan ,yakama hanyar gidansa.

               
shukuriyya najin fitar Kamal ta sallame sallarta, tarasa meyasa takejin kunyarsa, batasan koda idone suhada dashi, ba'a haka taso tazomai gidansa bah, amma yazatayi da qaddara, hawayene suke zuba sirara ah idanunta
"Allah ya isa tsakanina dakai, Allah kayi mun sakayya tsakanina da wannan bawannaka"
tashi tayi ta ninke sallayar tachire hijab din jikinta ta fito parlour, to her surprised sai taga flask akan dining table, taje tabude su duka sai taga abinchi ne achiki, babu ko kunya ta diba ta fara chi, murmushi ne qarara afuskarta, aranta kuwa chewa takeyi "Allah sarki uncle kamal sannu da qoqari, kalli yarda ya iya girki kamar wata mache"
tanachi tana nishadi tana santi harda tsiyayar lemo, chan kuma ko me tatuna sai ga hawaye ah idanunta, abunchin tabata qarasa chi ba kenan tahaqura ta tashi ta barshi agurin, daki ta tafi abunta tana hawaye, tundaga ranar da wannan abun yafaru da ita har zuwa yau bata qara samun kwanchiyar hankali bah, takasa mantawa da wannnan ranar kullum yunqurinta bai wuche tamanta da abunda yafaru da ita bah amma takasa, duk sanda zata zauna ita kadai saita tuna, ashe haka ko wache mache takeji idan akayi mata fyade? lallai zuchiyoyin mata da yawa ta illata,
" Allah ka saka mana,, ameen"
tafada aranta,,, haka ta dunga surutai da tunane-tunane har zuwa sallar la'asar, ta tashi ta gabatarda sallarta, bayan ta idar taji motar uncle Kamal tashigo gidan, toilet tafada ta kulle kofar tafara wankan dole, koda yashigo dakin yajita tana wanka sai shima yawuche nasa toilet din yayi wanka, yafito ya kwashe kwanukan datachi abinchi ya kai kitchen ya wanke, sauran na chikin flask dinma haka ya hadasu gaba daya yabayar da abinchin da yake chiki sannan ya wanke kwanukan, yadawo falo yazauna, yananan zaune ah falo har magriba amma bata fito daga dakinta bah, yana mamakin chanjawar ta, yasan dai tana matuqar sansa tomenene haka takeyi? shin ita ba musulma bache, bazata yarda da qaddara bah, haqiqa tana chutarda rayuwarsa, yanasanta sosai, yana tausaya mata, amma shi aganinsa wannan abun ai yariga yawuche, be kamata yayi affecting rayuwar auren su bah, shi yanzu yafi tausayawa kansa akan yarda yake tausaya mata, at least ko fuskarta yakamata tadunga barinshi yana kalla, kokuma tadunga zama sunayin hira ko iya wadannan abubuwan sun isheshi, kuma zaiji dadi idan tayi masa hakan, amma Sam taqi, shi koda iya wadannan yasamu daga gareta sun isheshi komai, wannan tunanin yadunga yi har yaje masallachi yadawo, yana shigowa yadauki motarsa yafita, kaji yaje yasiyo musu masu yawa yasaka wasu ah fridge sannan yadaura wanda za'a chi yanzu akan dinning table, dakinta ya wuche ya tararda ita akan sofa ta daura kanta akan guiwarta, sallama yayi kafin yazauna ah gefen gadonta
" shukuriyya!!!!"
yakira sunanta ahankali, dago kanta tayi batareda ta bari sun hada ido bah ta amsa tache
     "na'am"
yache
"meyake damunki?"
tache " ba komai"
    "bakida lafiya ne?"
yaqara tambaya
tache "lafiyata lau"
uncle Kamal yaja dogon numfashi sannan yache
"shukuriyya Ashe akwai lokachin dazaizo dazaki dunga boye mun damuwarki? ina tunanin ko ah wanchan lokachin ban chan-chan chi haka daga gareki bah, ballantana yanzu danake matsayin mijinki, idan baki fadamun bah wazaki fadawa?"
kalamai masu dadi da kwantar da hankali yadunga fadawa shukuriyya, atunaninsa zata sauko kokuma tafada masa damuwar ta amma Sam taqi....
(ni meerah nache wannan shukuriyya dama haka kike da taurin kai gaskiya kin fara bani haushi )
hakanan yakyaleta Yakama hannunta suka fita falo, yazaunar da ita akan kujera yache
"mezakichi?"
tache "babu komai"
yache "baze yuwu kiche babu komai bah"
kitchen yatafi yadaura masu indomie yakawo musu taji attaruhu da albasa, ga kuma naman kazar daya taho dashi, hakanan yadunga tursasata yana lallabata harta chi sannan yachi nashi, koda tagama chi daki tatafi ta kwanta, Kamal kuwa yana gamachi zuwa yayi ya wanke kwanukan yadawo falo yachigaba da going through wannan case din dasuka farayi ajigawa ranarda wanchan fate din yasamu shukuriyya, zuwa shadaya na dare ya haqura ya rufe takardun, yaje dakinta yamata addu'ah sannan ya wuche dakinsa yakwanta,,,, yadauki alqawarin bazai tursasata abusa komai bah, zaita lallabata har zuwa sanda zata dawo irin rayuwar da tayi abaya, zaijira har zuwa wannan lokachin domin yasan zaizo, wannan alqawarine yadaukarwa kansa....

( ni meerah nache abari ya huche shiyake kawo raban wani dae)

             
(🙊Af ni meerah ai namanta mah ashe mijintane fah ba saurayinta bah ashe yariga yasameta mah ) lolx

                 🌳🌺😘

*BAYAN WATA BIYU*
wannan itache rayuwarda wadannan ma'auratan sukeyi awannan gidan harna tsahon wata biyu, kullum Kamal ne yakeyi musu abunchi na safe, rana, dakuma dare, be taba gajiya bah, kuma betaba tursasa ta tayi abunda bata sobah, haka sukeyin rayuwar su babu dadi kuma duk daga bangaren shukuriyya matsalar take, har zuwa wannan lokachin babu abunda yachanja daga wannan rayuwar....

MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now