40

1.1K 63 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*



4⃣0⃣





Kafin tafiyarsu sun qara danqa amanar companies dinsu dasuka gada awurin mahifinsu ahannun abokinshi, daman shike kula musu dashi tundaga yarinta, yanxunma ahannunshi suka bar komai suka tafi abunsu....

Bayan sun koma abuja abuu yafara zuwa wurin aikinshi NNPC dakenan abuja, anan aka saka su A~li, sadiiq farouq da usiii makaranta, ummi tana kulada rayuwarsu yarda yakamata, kullum itache ke shiryasu tsaf sannan tabasu breakfast sannan takaisu Skul, idan lokachin tashi yayi tajeta daukosu, haka islamiyya ma xata kaisu ta d'aukosu sannan idan andawo gida ayi homework idan dare yayi suyi kallo kad'an sannan ta shiryasu kowa yakwanta, kullum sai ummi tayimusu wannan hidimar, dukda chewar akwai masu aiki sannan akwai driver amma bata bari suyiwa yaransu aiki, da hannunta take kuladasu,,,,, wannan shine aikinta achikin gidan kullum, sai kuma kukan takaichin rashin yarinyarta wanda kullum saitayi yafi aqirga, tun ana binchiken har aka daina, saboda su Kansu yan sandan sungaji, dahaka labarin haiydar da Kibdiyya yashafe achikin zuri'arsu..

                     

6angaren nene kuwa suna chan turkey abunsu suna rayuwarsu hankali kwanche, ko lokachinda abuu suka samu wannan accident din na rashin yarinyarsu nene batayi musu jajeba ko ah waya, ballantana tayi stepping foot d'inta ah Nigeria, haka tayi zamanta achan, kullum idan abiii yakira waya abuja yana making video call dakowa agidan, wani lokachin ma abun saiya zama kamar wani show, suyita murna suna dariya idan suna tareda mahaifinsu, don ummi ta jajairche wurin nuna musu abiii shine mahaifinsu, aiki nerh yasa yabar qasar sannan ta nuna musu nene itache mahaifiyarsu, saidai yaran jin ummi kawai sukeyi, sudai sunyarda chewan abiii dan uwansu nerh sannan yanada mata wadda basu ta6a ganinta bah, amma su basu ta6a daukar chewar sunada wasu iyayen dasuka wuche ummi da abuu bah.....

Bayan two years da komawansu turkey nene tahaifi yarinyarta mache aka saka mata suna *fatima zarah* , achan Turkey tahaifeta, kuma kobayan haihuwar basuxo gida bah, saima abuu da ummi nerh dasukaje sukaga baby, sati d'aya sukayi sannan suka dawo Nigeria,,,,

Bayan two years nene taqara haifo yarinyarta mache akasa mata suna *Bilkisu* shima basuxo Nigeria bah, kawai dai anyimusu sending pictures din yarinyar nerh, tananan kyakkyawa da ita kamar baturiya, ummi taso zuwa ganin baby amma abuu yahanata saboda chikin dake jikinta, badan tasoba tahaqura taxauna, after lyk two months itama Allah ya sauketa lafiya ta haifi yarinyarta mache aka saka mata *Amina* , yarinya kyakkyawa fara mai jan kunne.

Bayan an yaye biily daga nono abuu yad'aukosu yadawo dasu abuja Nigeria wurin dan uwanshi, sosai goggo tafara masifa tache yanda yaxo dasu haka xai koma dasu, amma saiya xauna ya fahimtarda ita chewar saboda yanayin garin yadawodasu bawai saboda nene bah, sosai yanuna mata babu tarbiyya agarin sannan babu ilimin addini, goggo ta fahimcheshi don haka takar6i yaran aka qara miqawa ummi su, bayan wasu kwanaki yakoma Turkey abunshi, goggo tasan kawai yafadi hakanne don ya kare matarshi, amma tasan sarai nene chewa tayi baxata riqesu bah shiyasa ya kawosu, itakuwa ummi dad'i taji dasuka dawo, koba komai zasu taso kansu ahade in one family.....

Tunda yaran suka tashi suka fahimchi wanene su da yanda abubuwa suka faru arayuwarsu suke tausayin kansu da kuma ummi, suna qarajin tsanar nene aransu domin suna ganin ita tayi silar rashin yayansu haiydar sannan ta dalilin hakan tasa suka rasa qanwarsu kibdiya, abu mafi muni shine yarda ta jefar dasu tasa qafa tayi tafiyarta tabarsu batareda ta damu bah, hakan yasa basujinta kokad'an achikin zuchiyarsu, basu d'auketa ah matsayin uwa ba tunda tundaga yarintarsu har zuwa yanxu bata ta6a zuwa wurinsu bah, in fact tunda tabar Nigeria bata qara dawowa bah bare taxo ta gansu, wanda su baxasu iya qirga adadin xuwan ummi turkey bah tunda sukayi wayo, abun takaichin ko ah waya bata nemansu, saima idan ummi che ta tilasta musu suche ina nene shine abiii xai chemusu bacchi takeyi wanda tuntuni sunsan qaryane, babu yanda xa'ayi ache duk rayuwarta bacchi takeyi, hakan yasa qiyayyarta taqaru azuchiyoyinsu.....

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now