84

1K 86 23
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳

Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH

Ina barar addu'arku dan Allah, Allah yayiwa Nene na rasuwa, kusakata ah addu'ah plz, Allah ya jiqanta daduk wani musulmi amin!!

8⃣4⃣

                        🌳🌺😘

       Juyawa tayi ta kalli haiydar dake zaune agefe yana zubarda hawaye, kallanshi tayi sannan tache

     "Am very sorry haiydar, I felt to give you a child, it wasn't my option, hadt been nasan wannan problems d'inne yasa naketa samun abortions I could have talk to my doctor, although kayi iya qoqarin ka wurin ganin munje munga likita amma naqi, trust me ina tsoran rasa baby nane shiyasa banje bah, bayan wannan banida wani dalili, kayafemun, namaka asarar baby's har guda biyu, it was coincidence, amma kayarda dani, nafika san yaran, nafika qaunarsu, naqi zuwane saboda banasan na rasasu, ka tuna irin azabar danasha ah farkon chikin,, amma naqi zubarda chikin saboda banaso na rasasu, tunani na be wuche inyi sauri in haifesu ba kafin na mutu, dan jikina yana yawan bani chewar baxanyi tsahon raibah, shiyasa nake gaggawar inhaifa maka yara, ko babu komai zanbar masu yimun addu'ah, saidai bansan chewar ban isa nayiwa Allah wayo bah, gashi nagama gudun asibitin yau gani  achikin shi, kuma ah asibitin dai chikin ya zube"
Tafad'a tana kuka....

Kasa magana haiydar yayi saima kukanshi daya chigaba, gaba d'aya nadamar rayuwarshi yakeyi, gani yakeyi kaman shiya sakawa shukuriyya chutar dayake jikinta, tabbas yabayarda gudummawa sosai wurin chigaban larurarta, sai yanxu ma datake fad'a yake tuna wasu abubuwan dakuma yanda suka kasanche, tabbas yayi babban kuskure, be ta6a tambayarta matsalarta bah, kuma sunsamu matsala sosai awurin girki kafin daga baya komai yayi settling, indai wani abu yasamu shukuriyya baze ta6a yafewa kanshi bah...

Daqyar yaqaraso gabanta sannan yache

    "Laifinane shukuriyya, nina ja miki komai, inada tabbachin chewar nine najaza miki wannan larurar tun ah farko...."
Sauri shukuriyya tayi ta rufe mishi bakinshi

     "Lokachin da nafara larurata ko saninka banyi bah"
Tafad'a tana dariya

Qoqarin magana yakeyi amma taqara rufe mishi bakinshi sannan ta qifta mishi ido, da alama yagane abunda take nufi dan haka yayi Shiru yana kallanta, murmushi tayi sannan tache

     "How did you feel today? Yaudai gaka ga family d'inka, badaman ina fad'a maka karka fitar da rai ba? Kaga hukunchin abangiji koh?"

Shiru yayi kafin yache

   "Tabbas naji farinchiki mara misaltuwa dazuwansu, saidai sunzo alokachinda bana chikin yanayi na dad'i"

     "Kuma hakan ba yana nufin karka godewa Allah bah ba.."
Tafad'a tana dungure mishi kai chikin sigar wasa

Dariya duka sukayi ah wurin kafin haiydar yache

     "Ya kikaji ke dakika San chewar cousin d'ina che ke?"

     "Honestly I can't say, saboda har yanxu zuchiyata takasa yarda da abun, sai nake ganin kamar mafarkine, har ynxu nakasa yarda da chewar niba y'ar gidanmu bache"
Chikin sigar wasa tayi maganar

      "Ke y'ar gidanku che ai shukuriyya babu wanda ya isa yaja da hakan"
Ummi tafad'a tana dariyar dole

Shukuriyya che ta kalli mashkur sannan tache
    "Ya mashkur!! Nasan na baka chiwan kai sosai daka baya, musamman na qin kar6ar maganar chi gaba da karatuna, banayi hakan bane danna qona maka rai bah, nayi hakanne saboda nasan gajeran lokachi nake dashi, nasan chewar mutuwa zanyi, jin hakan yasa naga karatun bashida amfani agareni, tabbas naso nayi karatu saidai qaddara ta riga fata, chiwo yariga yachi qarfina, shiyasa kaga na dage naqi yarda nayi jamb d'annan, ka gafartamun  dan Allah, bantaba  burin sa6a maka bah"

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now