59

1K 78 5
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳




Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*






5⃣9⃣


Ranar tana idarda sallar issha tayi kwanchiyarta, dan daman tun kafin chiwon nata ma tana bacchi da wuri nerh, ko takan haiydar bata qara bi ba balle tasan halin dayake chiki, chikin dare wuraren qarfe d'aya kamar an tsunguleta ta farka daga bacchi, kalle-kalle tafara ad'akin sannan tamiqe zaune ta jingina da pillow d'inta, tunani tayi chewan duk yau bataga haiydar yachi abinchi bah, inzata iya tunawa ma saitache tun kafin suje asibiti, tausayinshi taji ya ratsa zuchiyarta, tana tsoron kar wata larurar taje ta kamashi ta dalilinta domin baxatayi farin chiki da hakan bah, miqewa tayi jiki asanyaye ta fita daga d'akin, to her surprise saita hangi haiydar yanata kaikoma ah parlourn nasu, ganinta dayayi ta fito yasa ya tsaya chak yadaina tafiya, saima qureta da yayi da wani irin kallo mai chikeda manufofi, itakam tsayawa tayi tarasa abunyi saima sunkuyarda kanta da tayi qasa, ganin hakan yasa ya nufo inda take dasaurinshi yana tambayarta
"Kina buqatar wani abunne?"

Ko ansashi batayi ba ta wuche kitchen abunta, evn though ba abunda zatayi ah kitchen d'in, tana shiga tad'an tsaya for like five minutes saikuma ta fito ta wuche d'aki, still yana wurin data barshi ah tsaye, tana shiga d'aki tayi ajiyan zuchiya sannan ta zauna agefen gadanta, baxata iya chemishi yaje yachi abinchi bah, amma hakanan hankalinta yakasa kwanchiya da qinchin abinchin nashi, ita ta lura ma har yafita ramewa, haka ta koma tayi bacchinta batareda ta mishi magana bah.....

Tun asuba data tashi bata komaba, bayan ta idar da sallah tayita addu'ointa kafin dataga gari yafara haske ta miqe, kitchen ta nufa taga still abinchin jiya yananan babu wanda ya ta6a, abinchi tayi niyyar d'aurawa amma se umma takirata ah waya tache ga babanta nan dasu haniff zasuzo su dubata, xasu zo mata da abinchi, hakan yasa tafasa d'aurawa taje ta kintsa gidan, dukda daman ko ina tsaf yake agidan,,,,,

Wurin 9 Abban nasu yaxo tareda haniff da hanifah, ba wani dad'e wa sukayi bah agidan, daman duba jikinnata yazo yayi, hakanan suka gaisa adafe sannan sukayi sallama, Abba daxe tafi yachire kud'i 10k yabawa haiydar, ga kuma kayan tea daya kawo musu ah manyan gwangwanaye, godiya sukayita mishi dagashi har shukuriyya din, albarka yayita samusu sannan yaqara musu nasiya da addu'ah, daga qarshe sukayi sallama suka tafi,,,,,

suna fita ta d'auke annurin dayake fuskanta, daman tasakashi nerh saboda albarkachin mahaifinta dayaxo, ganin hakan yasa shikanshi haiydar yasha jinin jikinshi, miqewa tayi taje ta bud'e flaskses d'in da suka kawo, kunun gyad'a nerh lafiyaye na d'anyar gyad'a, saikuma pepper chickens ah flask shima me yawa, d'aya flask d'in ta bud'e taga sphagetti nerh dan haka taje ta d'auko plate da cup ta d'iba tafara sha, tas tashanye kunun gyad'an sannan ta zuba taliyan dayawa ah plate, dan umma ta mata gargad'i chewan tachi abinchi sosai sannan kajin ma haka, tas tachinye duk abunda ta zuba, tana gamawa takai used dishes d'in kitchen sannan ta dawo ta zauna,,,,,

Tayi tunanin haiydar zechi abinchin amma Shiru bataga ya ta6a bah, al'amarin nashi seya fara bata tsoro matuqa, dafarko tayi tunanin ta qyaleshi amma saitayi tunanin abubuwa da dama achikin zuchiyarta, sai kawai ta tashi ta kwashe kayan tea d'inda mahaifinta yakawo takai lokan kitchen inda suke ajjewa ta ajje, daman tuntuni wanda suke dashi yaqare, shikuma ba wani qarfin siyowa nerh dashi bah, dawowa tayi ta kwashe flask d'in abinchin takai tsakiyan parlour ta ajje inda sukechin abinchi tare dashi, yana zaune yanata kallanta, fruits d'inda umma takawo jiya ta d'auko ta mishi juice dashi sannan ta kawo parlourn ta ajje, tana gamawa tanufi d'aki abunta, yana ganin ta shiga ya d'auko yafara chi, baxe iya masalta irin yunwan dayake ji bah, don chikinshi harwani zafi yake mishi, gashi ko kasuwa be qara fita bah tun ranar, so babu kud'in ah hannunshi, tas yaqare banda yau da Abba yabashi kud'i to ko sisi bashida shi, zama yayi yachi abinchin kamar ba gobe, saida yachika chikinshi sannan ya tashi ah wurin, harwani jiri yake gani daya tashi saboda yanda damuwa da yunwa ta mishi yawa, d'aki yatafi yayi wanka ya shirya sannan yafita waje, siyayya ya musu da kud'in da Abba yabashi sannan ya shigo dasu gidan tana kallan shigowarshi amma ta d'auke kanta daga wurinshi, saida ya ajje komai ah gurin daya dache sannan yaxo kusada ita ya tsuguna daga qasa
"Shukuriyya k......."
Bata barshi ya fad'i abunda ke ranshi ba ta miqe tabar wurin, ganin hakan yasa yayi zamashi awurin yanabin bayanta da kallo,,,,


Haka ranar ya wuni yana bin bango kamar shine mara lafiyar, da yammachin ranar inna ta iso Kaduna, dan daman yasanar da ita shukuriyya tayi 6ari, hakan yasa ta nache saitaxo ta dubata, dafarko yaqi amma ganin ta matsa yasa yache ta taho kawai zai sameta ah Tasha, suna qarasowa suka sameshi ah tasha dan yadad'e yana jiransu, ya d'aukota suka nufi gidanshi, baqaramun murna shukuriyya tayi da zuwan inna bah, hakan yasa taso ta manta da damuwa dakuma larurar datake chiki,,,,

Zuwan inna gidan yasa gidan yayi kamar komi lafiya nerh, saboda shukuriyya ta jajirche wurin nuna chewar lafiya qalau suke zaune kuma babu wata matsala ah tsakaninsu, baqaramun dad'i hakan yayiwa inna bah, dan tun farkon ta sani chewar haiydar beyi za6en tumun dare bah, kwana biyu inna tayi chikin Kaduna ta koma gida, amma kafinnan saida sukaje gidansu shukuriyya ta gaisa da iyayenta ta qara musu godiya ga alheren da ake ma yaranta, sunji dad'in zuwanta sosai, ranar dazata tafi kuwa Abba nerh yasa mashkur yakaita ah motarshi sannan yamata alheri sosai, umma ma haka, ita kanta shukuriyya saidata bata wasu turamen atamfofi, haka dai suka had'a mata shatara ta arziqi sannan mashkur yamaidata KT....


Tana tafiya komai yakoma kamar yaune abun yafaru, daman koda inna take gidan ita shukuriyya bawai tana shiga harkarshi bane, kawai tana qoqarin ganin babu wani abu daxe had'asu nerh, dukda chewar shi haiydar yayi amfanida wannan opportunity d'in dan ganin yasamu sunyi magana amma hakan ya gagara don sosai ta iya takunta.

🌳🌺😘

_*bayan sati biyu*_

Wurin sati biyu kenan shukuriyya da haiydar suna zaman doya da manja, bata kulashi ko kad'an, idan tana parlour nerh yaxo yaxauna toh zata tashi tabar wurin, idan kuma d'akinta yashigo haka zata juya mishi baya kokuma tamishi nuni da waje, gashi zata mishi abinchi ta ajje mishi kullum ah inda ya dache, amma bata qara bari sun zauna inuwa d'aya bah, bayasan ganin ranta yaqara 6achi dan haka sai yayi yarda takeso kawai, amma sosai matuqa yakejin abunda take mishi achikin zuchiyarshi, babu abunda yafi tafiyarmishi da tunaninshi gameda ita irin yarda takasa furta ko kalma d'aya akanshi har yau, wannan abun yafi tayar mishi da hankali, shi yanxu bashida wani buri dayawuche ache tayi mishi magana, shi koda zaginshine tayi, kokuma tafurta kalmar yafiya kokuma akasin hakan......

Kasan chewar yau lahadi da wuri yadawo daga kasuwa, yana shigowa yanufi d'akinta amma se yaji tana wanka, hakan yasa ya nufi nashi d'akin ya kintsa kanshi sannan yafito yaxauna yana jiran fitowarta, ayarda yakejin zuchiyarshi yau sedai komi zai faru ya faru amma shi sam yagaji da zaman kuramen dasukeyi achikin gidan, idandai hakan ta d'auka ah martsayin horo agareshi to baxe iya jurewa bah, dan yayi mishi tsauri, har gara ta chanja salo kokuma tafad'a mishi abunda yake chikin zuchiyarta kawai,,,,,,

Yakai wurin hour d'aya azaune kafin ta fito, dan harya fara gyangyad'in gajiya, dan duk kwanakin nan bawani bacchi yakeyi bah, jin motsinta ah parlourn yasa yayi firgigit yafarka sannan ya daidaita nutsuwarshi, kitchen ta shiga ta fito da girkin datayi ta jera ah inda take ajjewa kullum, sannan ta d'ibi nata ta koma kan kujera ta zauna tafara chi batareda ta kalli ko inda yakeba, sosai hakan datakeyi yake qona mishi rai amma ya daure ya danne zuchiyarshi, barinta yayi tachi abinchin tagama sannan ya tashi ahankali yaje kujerar datake kai yaxauna agefenta

"Shukuriyya dan Allah ki saurareni, ki tsaya muyi magana dan Allah"

Banza tayi dashi kaman batasan meyake fad'a bah, hakan yaso yad'an tunzurashi musamman yanda ta mishi mugun kallo, amma kasan chewar yasan bashida gaskiya yasa yaqara danne zuchiyarshi, magana yaqara mata ta mishi harara sannan ta miqe azuchiye zata bar wurin, shikuwa ganin ta tashi akan kujerar yasa yayi azamar miqewa ya kwallawa sunanta kira da qarfi "shukuriyya",,, at the same time kuma yasa hannushi yajuyo da ita tana fuskantar sa, hanjin chikinta ba qaramun kad'awa sukayi bah, lokachi d'aya jikinta yafara rawa dan tayi mummunar tsorata da yanayinshi, hawayene suka fara zubomata afuskarta na tsoro da firgita, dan daman tun ranar da haiydar yafad'a mata maganar take jin tsoranshi kawai dannewa takeyi take zaune dashi.

🌳🌺😘








MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now