06

2.3K 116 6
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘




0⃣6⃣



Kwanaki uku kenan da tafiyar su umma suka dawo, ah wannan kwanaki shukuriyya tasaba da uncle kamal matuqar sabo fiye da zaton mai karatu, tanazama suyi karatu sosai dan ita tanasan mutumin dazai koya mata karatu, sannan sukan zauna yayitah basu labarin barkwanchi wanda zaisa suyita dariya, wani lokachin mah saiya kwashesu gaba dayansu su tafi wajen wasan yara, da wannan nerh suka saba ah iya kwanaki uku, dan daman kamal mutum nerh me san yara shima,,,, bayan dah suka dawo sunyiwa umman hamza godiya sosai abisa ruqon amanar da ta yiwa yaranta, umman hamza tache menene abun godiya ai duk yarana ne,,, banda murna da zumudi babu abunda shukuriyya takeyi ganin iyayenta sun dawo gida, shikam uncle kamal ji yayi dama ache basu dawo yanxu bah, dan yasaba da shukuriyya sosai, shi d'an kwanakin da sukayi mah gaba daya yamanta ba'a gidan take bah, gani yakeyi kamar ta dawo gidan da zama gaba daya nerh, sai yanzu da iyayenta suka dawo tukunna...,, haka umman hamza ta tattara musu kayansu gaba daya suka wuche gidansu...
ah bangaren su shukuriyya kuwa surutun zumudi kawai suke zubawa iyayen nasu, suche wanchan suche wanchen ko gajiya basayi, kaka kam taji sauqi sosai dan suna zuwa katsina asibiti suka kaita, chikin ikon Allah ta war-ware abunta kamar ba ita tayi wannan jinyar da ake tunanin bazatayi rai bah,, Ikon Allah kenan.

🌳🌺😘

uncle kamal yana shiga gidansu shukuriyya sosai dan har iyayenta ya saba dasu, shiyake yimata homework da sauran abubuwa, infact komai nata Wanda mashkur keyi mata ah da yanxu uncle Kamal nerh yakeyi mata, tasamu brother ah sama wanda they are not related by blood but related by heart, yanzu bata da zanche saina uncle Kamal, kullum hirarta guda daya che "uncle kamal" "uncle kamal" idan tafara maganarsa wani lokachin ah gida harsai umma tache ya'isa haka tukunna zatayi Shiru (kunsan yaro).

*bayan shekara biyu*

umma ta qara haifo yarta mache wadda tachi suna hanifah, su shukuriyya sai murna akeyi anfara tara qanne, izuwa wannan lokachin shaquwa mai qarfi che atsakanin duka gidajen, uncle Kamal da shukuriyya kam shaquwa che me qarfi ah tsakaninsu, daga iyayenshi har nata sunsan manufarsa akanta, ita kadaiche bata sani bah, kuma yayi alqawarin sai randa ta isa tasani zai sanar da ita, dan haryanzu kallan yarinya yake yimata sosai, ah tunaninsa tayi qanqanta kalmar soyayya ta fara ratsa kunnuwanta, shikuwa abba tsoran yaran zamani yakeyi, yana tsoran ranarda zata mallaki hankalin kanta tache batasan uncle kamal, bazai taba yiwa yarinyarsa dole bah, saidai bazaiji dadin al'amarin bah .


*8 YEARS LATER*

🌳🌺😘

Bayan qwaqwarmaya da qananun qalubale na rayuwa wadanda baxa'a rasa bah su shukriyya an kammala secondary skull successfully, su mashkur da hamza kuwa an gama university, uncle kamal kuwa tuntuni yakama qasa, aiki sosai yakeyi, income ta ko ina, dan yanzu yazama chikakken lawyer me zaman kansa.

umma da kanta ta hadawa yaaranta walima nagani nafada Wanda akayi ah chikin gidansu, anyi shagali sosai dukkansu suka gayyato frnds dinsu, murna gurin shukriyya ba'a magana domun ita gani takeyi ko ya mashkur be kaita farin chikiba, don gani takeyi secondary dinnan data gama tafi wanda yagama university. Ansha gift kala-kala daga gurin yan'uwa da abokan arziqi, uncle kamal was too busy ranar, bexo walimarta bah amma ya aiko mata da gift dinta.

Atsayin wannan shekaru babu abunda ya chanja daga abunda uncle kamal yakeyi mata, saima abunda yaqaru dan kullum wani saban Santa ne yake shiga chikin zuchiyarsa, shukuriyya tadade da fahimtar uncle kamal santa yakeyi, kuma itama ta dade da yardar wa zuchiyarta irin san da takeyi masa, saidai zata jira randa zai furta mata da bakinsa, kuma tayi alqawarin zata soshi tsakaninta da Allah, wannan alqawari nerh tayi da zuchiyarta.
shukuriyya anzama budurwa kyanta yaqara fitowa sosai fiye da dah, be course she is at the age, gashi ta taso Yar gata agurin iyayenta, yayanta da kuma uncle dinta, gatan yayi mata yawa, shiyasa abubuwanta suke tafiya daidai , gashi kullum halayenta na gari qara bayyana sukeyi , shukuriyya baiwar Allah.

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now