99

960 89 10
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳

Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH

9⃣9⃣

Umma na riqe da twins ah hannunta sai juyawa takeyi tana tofa musu addu'ah aduk wani sassa na jikinsu, tana ganin yanda hanifah taketa kumbure kumbure akan bata bata ba amma tayi mata banza kamar bata jita bah, idan ba'a musu addu'ah ba meza ah musu? Tas ta tofesu tana qare musu kallo sannan ta miqawa hanif da hanifah su gani, sai sannan suka saki fuskarsu tun bayan shigowa gidan da sukayi, achewarsu sunzo da zumudin ganin baby's amma an hanasu kar6a, saika rantse an hana su nerh gaba d'aya...


Dashike tun dazu sukazo har Abba yazo ya gansu yamata sannu sannan yakar6i yara ya musu addu'ah, yanxu yana chan tareda su abuu sunata hira irin tasu ta manya chikeda raha.....

Shukuriyya hira taketa yiwa umma, saika rantse sun dad'e nerh basu hadu bah, she couldn't get enough of her no matter what, umma is her world, she can't denied that, she feel more comfort duk sanda take tare da ita, she speaks her mind to her other than any human being, daga ita se mashkur babu na ukun su, indai zata fadawa wa wani Abu me mahimmanchi other than dis two people to kowa ze iya ji, dukda chewar daga baya ma komi ya bayyana chewan basune iyayenta ba amma dukda haka babu abunda ya chanja daga gareta.......

Sunyi maganan komi da umma harda wanda ma batayi da kowa chikin gidan ba, da yake hanif da hanifah sun fita parlour da baby's d'in ahannunsu, sai ta qara samun damar ke6ewa da umma da kuma mashkur d'in, nanne ma take sanar dasu qudirinta gameda sunan da za'a sakawa yaran kamar dai yanda haiydar yabata za6i, takuma basu hujjojinta, umma che tache

"Gaskiya kin kyauta shukuriyya, kinyi halarchi, Allah ya miki albarka, Allh ya raya mana Ku gaba d'aya"

Murmushi tayi sannan tache

"Umma komi yana chanjawa nerh bisa tsarin abunda ubangiji ya tsara, inba dan hakaba ban ta6a tunanin zanyi aure mijina yabani za6in sakawa yarana suna ba sannan insaka sunan daba naki da Abba ba, Allah nerh shaidar zuchiyata"

In a serious tune tayi maganan, umma ta fahimcheta, hakan yasa tache

"Ai haihuwa yanxu aka fara shukuriyya, fatana Allah yabaku masu amfani ya raya muku su"

Murmushin gefen baki shukuriyya tayi wanda yafi kama da yaqe, is like maganan yasa tunaninta ya tafi wani wurinne wanda har yasa kwalla yad'an zubar mata kad'an, amma chikin dabara tayi amfanida gefen hannunta ta goge, kafin nan ma dukansu sun ganta, amma tun bayan wasu lokachi kafin yanxu umma bata chika san yimata tambayoyi anyhow ba, hakan yasa tayi kamar bata gani ba lurada chewar bataso agani nerh.....

Mashkur ma sambarka yayi da tunanin da shukuriyya tayi akan baby's d'inta, chikin hakane ma takewa umma maganar bikinshi, umma che tache

"Aikeda yayan naki kunfi kusa, tunda ya zabi hakan kawai ki barshi yayi, mu kanmu hankalinmu zefi kwanchiya"

Hakanan sukayita hira, ummi che ta shigo takewa umma qorafin shukuriyya taqi zagewa tabawa yaranta nono, achewarta wai basa kamawa, nan umma, ummi, Nene sukayi mata chaa aka suna mata fad'a, achewarsu yaran dayazo duniya ai babu abunda yasani, itache zatayi duk dabarar daxatayi ta basu sannan tasasu su sha dole, hakadai chikin hikima da dabara ta samusu harsuka fara sha, complain tafara wai zafi yake mata, ummi tache ai daman se ahankali ze kawo tunda yanxune akayi haihuwan, amma gara ta chire quiya tadunga basu dan shayar da yara biyu ba abune me sauqi bah,....

Wunin ranar baqine sukayita zuwa kamar kullum, hakadai ake d'aga yaran ana ajjewa, shukuriyya har tausaya musu take kar jikinsu yayi tsami, se wurin isha sannan gidan yayi tsit alamar babu wani baqo daya rage sai masu gidan, Abba da umma kam sun koma KD, akan chewar a day to the naming ceremony zasuzo tareda inna da kaka, saisu kwana idan akayi bikin suna saisu koma, shukuriyya bataso ba amma haka nan ta haqura bayan tasha lallashi awurin umma, dashike ma anbar mata hanif da hanifah tareda ita sai bata wani damu sosai bah, amma saboda irin hakane yasa taso ache taje ta haihu ah KD din, kobabu komai idan tayi numfashi zataga umma ah gefenta, dukda chewar nandinma babu abunda ta rasa....

Kayan barkan wanda umma da abba suka kawo mata ta juye akan gado tana qarewa kallo, duk chikin kayan da aka bata na kyauta babu wanda tayiwa kallo d'aya ya shiga ranta kamar wannan, d'aya bayan d'aya ta dunga d'agawa tana kalla kayane masu kyau kuma masu tsada, wani leder kuma wanda tun daxu aka kaishi kitchen yajin daddawa nerh me rai da lafiya bokiti guda biyu duka manya achiki aka zuba mata, she can't thank them enough, mayarwa tayi kowanne wurinshi sannan ta ajje ah gefe, biily che ta shigo hannunta da baby girl din ta miqa mata

"Tun daxu take kuka ummi tache ki bata tasha"

Ansarta tayi silently tana ajiyar zuchiya sannan tache

"Biily kwashe kayan nan ki tafi dashi please"

Kwasar kayan Biily tayi sannan ta fiche daga d'akin, kallan yarinyar shukuriyya ta tsaya yi, anche maza sunfi fitina amma wannan karan bataga alamar hakan bah, kafin yayi kuka d'aya tayi goma, haka jiya suka kwana tana mata kukan dabe kai zuchi ba, rashin bacchin nata da kuma hayaniyar yau datayi yawa shine ya haifar mata dawani matsananchin chiwan kai, harji takeyi kamar kanta ze rabe biyu saboda chiwo......

Tana gama sha madadin tayi bacchi saita qara tangarar da idanunta tanata shure shure, itadai bacchi takeji sosai, ta janyo wayarta zata kira wani chikinsu yazo ya d'auka sega haiydar nan yashigo da boy din ahannunshi, dan ajiyar zuchiya tayi, bataso shogowarshi yanxu ba, dantasan idan ya zauna ze iya raba dare agurin, itakuma kanta chiwo yake mata sosai, gaisawa sukayi ya mata sannu da jiki yanata wasa da babynshi ah hannu,....

Tunda akayi haihuwan se dare yake zuwa, saikuma da safe ida ya leqo su, shi ah lallai fushi yakeyi ba'a bashi matarshi ba, jiya har zuwa yayi ya samu ummi yache abashi ita su koma chan, ummi dai tache ba ruwanta yaje gurin Nene, chan ma wuta wuta tamai tache saidai yaje yayiwa goggo magana, hakanan kuwa yaje ya samu goggo ya mata magana, goggo kuwa tache Sam batasan zanche bah, tache lallai saidai yajira tayi arba'in tukun, haka ya tafi yanata qunquni an hanashi matarshi, kowa chikin gidan saida yaga qarfin hali da rashin kunya irin tashi, achewarsu mata nawane suke barin gari su tafi gida wankan jego, wanda mijin ma saiya dad'e be gansu bah, shikuwa kullum gashi ga ta, bacchi nerh kawai ke rabasu amma ache ze tashi hankalinshi, kowa wautarsa da rashin kunyarsa yake gani afili, shikuwa haiydar ah bangarensa ba haka bane ba, babu abunda yafiso irin yaga sun kwana tare sun tashi tare, yafiso yayinda yake bacchi yadunga jin d'umin su ajikinsa, ah kwanakin nan ma dabasa tare kwata kwata baya iya bacchi, se yakai wurin asuba yana juyi akan gado, shi sam baya maraba da wannan aladun, tunda chan ma ba qaunarsu yakeyi ba bare yanzu dayasan darajar iyali......

"Kin biye musu kinqi ki biyoni koh?"

Yanda yayi maganar ma dariya ya bata sosai wallahi, dariyar che taso ta qufular dashi, tsayawa yayi kawai yana kallanta, badan kar ache yafiya San zuchiya ba dasai yache shukuriyya sam bata damu dashi ba, to amma yasan idan ya fad'i hakan beyi adalchi ba, to amma yarasa dame ze fasalta abunda take mishi, idan yamata maganar daya kamata ache ta jimanta mishi saitayita mocking nashi tana mishi dariya, gashinan ma yanxu...

Ganin ya 6ata rai yasa tache
"Kayi haquri mana, kwana 40 d'in nawa yake game yawan rai?, yanxu zakaga yazo ya wuche, ummn?"

Kad'a kanshi yayi kamar qaramin yaro yana mayar mata da murmushin.

Vote, comment, share and share ur views





MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now