19

1.6K 74 10
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘




1⃣9⃣

   
                      

     "Shikenan"
   "Alhaji ya haula"
"innalillahi wa inna'ilaihir raji'un"

Maigadi yafada tareda yin zaman dirshan ah qasa kamar wanda aka tankwabar....

Shukuriyya che ta bishi da ido dan san fahimtar abunda yake fada,

    "Mekake nufi?"
tafada ah hankali chikin sanyin murya kamar ba itache takeyin kuka yanxu bah, ah lokachi daya kuma hawayen dake zubowa daka idanunta suka daina zuba,

    "Hajiya alhaji ya mutu"
mai gadi yafada yana sharche guminda yake zubo masa daga Kansa,,,

   "Nooo",
"this can never happen"
"Ya kamal baze mutu yanxu bah, saboda bamuyi maganar mutuwa dashi bah"

Wata iriyar nutsuwa che ta saukar mata ah lokachin, ah nutse ta chika kamal  daga ruqon hannunshi datakeyi, sannan ta dauke kansa dake kan chinyarta ta ajje ah qasa, dagudu ta tafi chikin gida,.

Wayarta ta dauko don yin kira saidai ta rasa wanda zata kira, gashidai ta bude contact dinta amma ta rasa wanda zata kira, sai tunani takeyi kamar wadda batada kowa, numban mashkur tayi dialing amma harta katse be daga bah, haka ta qara kiransa be daga bah, saida tayi mishi 10missed calls amma beyi picking bah, gajiya tayi da kiransa kawai ta kira hamza, shima saida tayi masa wajen 5missed calls amma be daga bah,

     " ya subhanallahi"
Ta fada ah ranta, yayinda wata zufah take keto mata ta ko'ina ah jikinta....

Asibitinsu ta kira ah waya, tayi sa'ar samunsu, tasanardasu abunda ya faru chikun nutsuwa sannan sukache gasunan zuwa,,,

fitowa tayi da gudu ta dawo inda kamal yake ah kwanche, tsugunawa tayi ah gabansa hade da ruqo hannayenshi, addu'ah kawai take tofah mishi, hoping that dogon suma yayi ba mutuwa bah.....

                       
             *30 minutes later*

Motan asibiti nerh yayi parking ah qofar gidan kamal chikin jiniya irin tasa, Wanda yake dauke da ma'aikatan lafiya achiki, motar tana tsayawa da Sauri ma'aikatan lafiyar dake chiki suka fito suka shigo gidan Kamal dan daukarsa, suna shiga suka ganshi kwanche chikin jini, haka suka daukeshi suka daura shi kan gadon marasa lafiya sannan suka sakashi ah motan, suka kama hanyar asibiti chikin gaggawa.
shukuriyya kam har ah chikin motar ta kasa sakin hannun kamal, sannan har yanxu addu'ah kawai take tofa masa, ma'aikatan lafiyar dake chikin ambulance din sunkasa fahimtar wani irin taimako zasuyiwa kamal kafin suqarasa asibitin, dan basuga alamar yana buqatar hakan bah, hakanan suka kyaleshi suka zuba masa ido suna kallanshi, suna jira suje asibitin, idan yaso koma menene ah tantanche achan.....

         
                        🌳🌺😘

Mashkur da hamza nerh ke tafiya ah hanya suna hirar ball dinda suka kalla yanzu, sai dariya sukeyi, da alama wadanda sukeso suchi nerh sukachi, suna zuwa qofar gida sukayi sallama da juna kowa yashiga gidansu.......
                     

Mashkur yana shiga ya tararda mamansu ah parlour ya durqusa ya gaisheta, ta amsa masa gaisuwar tana mitar wannan Daren da yake kaiwa wajen kallan ball, haquri yabata kamar kullum, dan ba yau aka fara bah sannan ya tashi ya tafi dakinshi, toilet ya Shiga yayi alwala yana istigifarin rashin yin sallar ishha da wuri sannan ya fito ya tayarda sallah......

Yana idarda sallah ya jawo wayarshi dake kan gado, wadda ya ajjeta saboda kallan ball daxasu tafi, daukowa yayi da nufin bude data, amma saiyaga missed calls din shukuriyya har guda goma,
     "lafiya?"
yafada ah fili yana tambayar kansa, parlournsu yafito dauke da wayar tashi ah hannu, yanemi waje ya zauna.

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now