🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*
0⃣5⃣
Awannan lokachin kuma su mashkur suna xuwa skul ba'ayi musu Hutu bah, duk da haka umma taso tafiya dasu amma umman hamza tache sam batasan zanche bah ai anriga anzama daya dan haka tayi tafiyarta ta barsu dan baza ah katse musu skull bah, musamman mah tunda ba dadewa zasuyi ah katsina bah, aikuwa hakan akayi, dan itada abba kawai suka tafi sai hanif dan daman goyanshi akeyi lokachin, akabar mashkur da shukuriyya agidansu hamza, ranar dasuka tafi shukuriyya tachi kuka dan daman ita akwai kawazuchi, komai takeyi tana manne da umma da abban ta, ganin mashkur atareda itane mah yasaka ta dan kwantar da hankalin ta amma da babu shi mah sam bazata zauna bah, dakyar umma ta lallaba ta sannan ta zauna, aikuwa suna tafiya taqara fashewa da wani saban kukan batayi Shiru bah har saida barchin wahala yadauketa ah wajen, ah pourlourn tayi barchi tana ajiyar zuciya saboda kukan da tayi, su mashkur kam ana chan ana wasa ah bayan gida .....
*2hrs later*
wani saurayi nagani ah tsaye ah kofar gidansu hamza kyakkyawa ne irin chocolate dinnan,shekarunsa zasukai kama ishirin haka, rataye da jaka ah kafadarsa da kuma trolley dinshi yana ta kwankwasa kofar gidan, daga chikin gidan kuma umman hamza che keta kwalawa hamza kira
" hamza!!! Hamza,!!!"
kaje ka bude qofah ana bugawa, sai bude murya take tana kiransa sai chan ya amsa mata yataho, tanata masa fadan idan suna wasa kwata-kwata basa jin gari, dasurinsa ya qarasa gate din gidan ko tsayawa tambayar waye beyi bah yabude kofar saboda yanda yaga maman nashi tanata fada, wazai gani? Ihuu ya kwallah tareda da kiran sunan shi
"uncle Kamal "
yafada tareda hugging dinshi at thesame tym, ummanshi dake chiki itama tafito da saurin ta tana dariya tache
" lallai Kamal,, sai yau? tun jiya nake zuba ido fah"
Dariyar ya mayar mata sannan yache
"wlh umman hamza comitment ne sukayi yawa sai jiya nagama clearing komai, amma yanzu ai gashinan na qaraso"
yafada yana dariya yayinda suka koma chikin gidan gaba dayansu dasuri hamza yazagaya bayan gidan yakira qannenshi tareda mashkur kan suzo uncle kamal yazo, ae kuwa dasaurinsu suka bar wasan suka tafi chikin gidan sai sannu dazuwa sukeyi masa, duk sun kanan-nadeshi kowa da hirar da yakeyi masa, chikinsu harda mashkur kaman daman yasanshi tuntuni ( kunsan yara da saurin sabo) yadauko tsarabar daya tahomusu da ita yaraba musu, wasa ne akansu dan haka suka tashi suka bar falon suka kai tsarabar daki suka koma Inda suka fito dan chigaba ah inda suka tsaya...
umman hamza ta gabatar masa da abinchi yafara chi yache
" kamar kinsan da yunwa ta naqaraso"Saida ya chika chikinsa sannan ya lura da wata kyakkyawar yarinya agefansa tana bacchi
" mashaAllah "
yafada ahankali yana admiring kyan yarinyar
" she is damn beautiful "
shine kurum abunda yafada, umman hamza che tashigo parlourn tache
" ah kamal harka gama?"
yache
"eh wlh"
Sai yanzu suka kara gaisawa atsanake, yabata saqon gaishe gaishen yan uwa da abokan arziki sannan yafiddo mata da tsarabar da aka bashi yataho mata da ita ya miqa mata tanata godiya kuwa, sai ah lokachin yache
"umman hamza wache yarinyache wannan?"
ya fada yana Nuna shukuriyya dake kwanche kan carpet tanata bacchi abunta, tache
"yaran moqochiyata ne wlh, mutanen katsina ne dazu ne aka aiko babu lafiya shine suka tafi babu shiri, ga yaran suna zuwa makaranta sai nache abarsu ah nan kawai sujesu dawo, itada yayanta ne ai wannan daka ganshi tare da hamza... yache
" gued!! amma yarinyar tanada kyau"
tache
"ina ruwan shukuriyya"
kamal yache
"unanta kenan?"
tache " eh!! maryam ne asalin sunanta amma haka ake kiranta"
Yache "Allah sarki!! zaku bani ita umman hamza?"
Dariya tayi sannan tache
"idan tanaso sai ah baka ae"
sukayi dariya gaba dayansu tache
" kukan tafiyarsu mah takeyi shine barchi ya kwasheta anan, ina fargabar ta tashi ta chigaba daga inda ta ....... Bata karasa fada bah shukuriyya dake kwanche tafara juye-juye, saikuwa ta hau murza idanun ta, bude idonta keda wuya ta daura su akan kamal, su sun zata mah kukan zata chigaba dayi ganin yanda take yamutsa fuska saisuka ji tache
" ina wuni "
tana duban kamal, da mamaki ah fuskarsa ya amsa mata, tajuya tache
" umman hamza ina ya mashkur?"
tache
"Yana waje suna wasa"
sai kawai tatashi salin alin ta tafi toilet , tayi brush ta wanke fuskarta tafito tawuche gurinsu mashkur
" WAW "
kawai kamal yafada, yarinyar ta burgeshi, ache yarinya kamar wannan tasan tayi duk wadannan abubuwan batareda anche tayibah
" she is amazing "
yafada yanabin hanyar da tabi da kallo, kan kache me harta saki jikinta tanata wasa kamar ba ita take wannan kukan ba dazu, sai wasan ta takeyi tana guje-guje da yara atsakar Gida, ga humaira chan tana wasa dasu mashkur amma ita bataje gurinsu bah, tafi jin dadin wasa chikin qananan yara, tagoya wanna ta sauke tayi wa wannan doki tasaukeshi tayi gudu da wanchan, haka tadunga yi wa yaran sai dariya sukeyi alamar suna jin dadin wasan, duk abunnnan da takeyi Kamal na jikin window yana kallanta, saiyaji yarinyar taqara burgeshi, yaji yanasan yarinyar, yanasan kasanchewa tareda ita.
" she is just 6, but zan raineta, zan kula da ita"
Yafada aransa yana nodding din kansa bai san ma ta tahobah saboda tunanin da yakeyi saijin sallamarta kawai yayi, toilet tanufa tayi alwala ta tayarda sallah, mamaki yakeyi sosai, shikansa baliqi mai hankali yanajin kiran sallar amma betashi ya gabatar bah saboda gajiyar tafiya, gasu hamza chan ma ko niyyar motsawa basuyi bah bare uwa-uba humaira, dukkansu sun girmemata amma ita hartasan taje tayi, tana idar da sallah tanufi gurinsu taje ta zauna kusa da yayanta, tache
"ya mshkur har na idar da sallar la'asar"
yache
" toh sannu "
yachigaba da wasansa, ganin baida niyyar motsawa tache
"kaima kayi taka tun dazu koh?"
yache "ah-ah banyi bah"
Aikuwa ta tashi tache
"yeahh nidai tawa har taje, idan bakayi taka da wuri bah baza tajebah, kaga nayimaka wayo nafika lada, ai dagudu yatashi ya nufi fanfo yafara alwala yana chewa "Allah baki isaba saina fiki samun ladan"
Jin abunda tafada na chewar tafisu lada dukkansu suka tashi aka fara rige-rigen alwala, itadai ta dauki baby boy din umman hamza da take goyo wanda yake kukan antafi anbarshi ta goyashi ah bayanta tana jijigashi, kan kache me yayi barchi, takaishi daki ta kwantar sannan ta dawo falo ta zauna, tana dawowa taga har sun idar da sallah, humaira takalleta tache
"Kinga muma mun idar da tamu ladan mu yazama daya kenan koh?"
shukuriyya tache
" nawa yafi naku saboda nina tuna muku kukaje kukayi"
Aikuwa humaira ta qufula tajuya tache
" wai haka uncle kamal?"
uncle kamal yache
"eh mana, tanada ladan tunatarwa"
Hamza yana gefe yache
"in Allah ya yarda kullum nizan dunga tunawa kowa nagidan nan"
mashkur yache
"ai mantawa zaka dunga yi nixan dunga tunawa kowa"
harsun fara musu uncle kamal yadakatardasu yache suyi hakuri xa'aga Wanda zai dunga tunawa wani, sukache toh suka tashi dukkansu suka tafi daki sukabar shukuriyya, sai gasu sunfito kowa dauke da biscuit da alawan da uncle kamal yabasu dazu da yazo gidan, lokachin shukuriyya tana bachi , bema san tana gurin bah alokachin , danhaka be bata bah kowa yazauna yafara chi banda shukuriyya ita ko kallansu batayi bah TV mah take kallo abunta, mashkur yazaro biyu anashi rabin biscuit din kenan yamiqa mata yache
"shukuriyya ungo"
ta kalleshi ta kalli biscuit din ba tareda ta karba bah tache
"ya mashkur ni banachin biscuit me madara"
yache "sai wanne?"
tache masa
"Mara madara mana kachinye abunka kawai" yache "kee shukuriyya kojiya fah naga kinchi biscuit me madara ah skull kuma da kudinki kika siya" hamza yache "nima naganta harta bani guda daya" shukriyyah tache ai jiya nachi na final bazan kara chiba" sukache "shikenan toh"
humaira dake gefe tamiqo mata alawan hannunta shukuriyya tache "nadaina shan sweet ay chiwon chiki yake sawa"
kamal duk yana jinsu yarinyar made him totally speechless, tashi yayi yafita dan yasiyo mata mara madara ah kanti ah ransa kuwa chewa yakeyi wato abun wani be dameta bah kenan, tunda gashi har blood brother dinta yabata taqi karba, kuma dasuna chi ko kallo basu isheta bah gsky tanada hankali sosai, yasiyo yakawo mata, yayi tunanin bazata karba bah to his supprise sai yaga takarba tafara chi tana chikin chi saiga umman hamza tashigo falon shukuriyya tache
"umman hamza babu abunda za'a yi miki ?"
tache "babu komai shukuriyya girkin darene kuma sai anjima zan daura" tache "ai nima na iya bare maggi indaka shi da gishiri kuma ina goge kitchen idan umma ta barar da miya, inzaki dafa kema zan tayaki"
tafada tanachin biscuit hankalinta ah kwanche, umman hamza tayi dariya tache to kibari saina daura tukun zan kiraki .
humaira nagama chin tsaraba ta miqe tache "kuzo muje muchigaba da wasan damukeyi dazu yayi dadi sosai" suka tashi gaba dayansu zasu tafi banda shukuriyya wadda ko motsawa bata yibah, mashkur ya kalleta yache "ke baza kibah?" tache
"tabdi Jan haka kurum intaka yaran aljanu su hau kaina , indunga yin hauka irin na unty Bilkisu (malamar Skul dinsu mai aljanu) kuma anche sai yamma tayi aljanu suke fitowa yin wasa, inkaima kanayin wasa su hau kanka, tache babu ruwana bazanyi bah"
ai babu shiri kowa yakoma yazauna, uncle Kamal kuwa dariya kawai yakeyi dan izuwa yanzu yarinyar tadaina bashi mamaki dariya kawai take bashi, yarinya y'ar karama da ita sai wayon bala'i "she is extremely incomparable "
uncle Kamal yakalli umman hamza yache "yarinyar nan tachika wayo fah , ina qara Santa"
umman hamza tache
"ai tafi haka mah shiyasa nake son abotarta da humaira"haka suka zauna ah falo har zuwa magriba lokachin magriba yanayi ladan ya fara kiran sallah, korufe baki beyi bah suka miqe suka tafi yin sallah, ita kanta umman hamza abun dariya yabata ganin yanda suka miqe da hanzari, ita kanta sai taji shukuriyya ta qara burgeta .....
da lokachin barchi yayi kowa yatafi ya kwanta, uncle Kamal shima yawuche dakin baqi ya kwanta da tunanin shukuriyya fal aransa...
(uncle Kamal qanin umman hamza ne uwa daya uba daya, yanada shekaru ashirin yanzu ah duniya, ya kammala secndry skull dinshi shekarar data wuche yanzu haka Skul zai fara ah nan Kaduna shine dalilin zuwansa kaduna kuma dalilin dayasa yadawo gidan umman hamza da zama).
MEERAH
