107: "realisations"

975 73 20
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳


Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH


1⃣0⃣6⃣


Tunda yashiga side d'in goggo ya jingina kanshi akan kujerar daya zauna, tunani yakeyi kala-kala achikin zuchiyarshi, rintse idanshi yayi yana tuna abunda kulu ta fad'a mishi d'axu

"Kullum haka kake chewa, you said it each and everyday, kullum maganar ka kenan I was never like my mother , but you never tell me not for once that I was like you""

"Bahaka nake ba kulu, I was never like you, bani kika gada ba, amma idan har kulu zatayi wannan furuchin lallai taji wata maganar awani gurin, towaya gaya mata?"

Saqe saqen da babannata yake tayi achikin ranshi kenan kafin goggo ta fito ta same shi, tsohuwa sosai, tsohuwa me ran qarfe, duk jikinta furfura, tsufa sosai ah bayyane atareda ita

"Haiydar! Saukar yaushe? Tafad'a chikin dasasshiyar muryarta irinta tsofaffi"

"Yanxu na shigo, dawowa ta kenan"

"Me kache?"

Goggo taqara tambaya, Sam bataji yanxu sosai, dukda chewar ansaka mata abun qarin sautin magana ah kunnenta, amma dukda haka saika d'aga muryarka sosai sannan zatajika, wani binma saidai kayi maganar kamar ihu sannan zataji abinda ka fad'a.....

"Yanxu na shigo, dawowa ta kenan"

"Aihoo! Sannu da zuwa, kaje ga abinchi achan ka zuba kachi"

Murmushin qarfin hali yayi sannan yamiqe yaje wurin dinning table ya zauna, abinchin ya zuba ah plate ya zuba masa ido ya kasa chi, lamarin kulu na bashi matuqar tsoro, da sam tana shakkar sa, amma yanzu ta daina, ko tsoronshi bataji, tsaf take kallan kwayar idanshi ta fad'a masa magana san ranta, shikuma ta inda Allah ya jarabcheshi kenan.....

Matse wani guntun hawaye yayi sannan ya d'auka spoon yafara chin abinchin dake wurin.....

Yau shekara goma sha shida kenan da kwanan abinchin shi yadawo wurin da zama, tun bayan rasuwar matarshi shukuriyya goggo tachigaba da d'aukar d'awainiyar abinchin shi, na safe na rana dakuma na dare, wani lokachin ma itache take dafa masa da kanta, yanxu nerh da shekaru suka qara ja ta haqura da shiga kitchen da kanta, amma dukda haka anan takesa masu aiki su dafa su kawo mishi yachi, har gobe kula take dashi kamar qaramin yaro, babu abunda zechewa goggo sai fatan Allah yabiyata da gidan Aljanna sakamakon alkairanta agareshi.......

Yana gama chin abinchin ya wuche side d'insa ya shiga dakinsa ya rufe, wanka yayi sannan yasaka kaya marasa nauyi, komawa yayi kan gado abubuwa dayawa suna dawo mishi ah kwanyar kansa

"Allah nerh kadai yasan dalilin dayasa shukuriyya ta mutu bayan ta haifeki, wataqila ubangiji bayaso ta shaqi baqin chiki daga gareki kulu"

"Wataqila kuma Nina qaza wurin tarbiyantar dake, shiyasa kika zama abunda kika zama"

Duk haiydar nerh yake wannan tunanin achikin zuchiyarshi, wasu maganganun ma ah fili yake yinsu tsabar yanda damuwa ta mishi yawa

"Ikon Allah! Yanxu kulu menene ban miki ba ah RAYUWA? Na miki wanka da hannuna, na shiryaki da hannuna, na miki tsarki da hannuna, nakaiki makaranta da kaina, banta6a barinki tareda wasuba, saboda kar in auri wadda zata wahalar mun daku yasa naqi qara aure tun bayan rasuwar mahaifiyarku , na kulada Ku dakaina, i did more than best to you, i gave you more than enough, amma ache babu sakayyar daxaki mun se wannan, duk soyayyar dana nuna miki anan zata qare, you end up raising your voice on me, nizaki dunga nunawa da yatsa, nine ban isa in fad'a miki kiji ba, kodai soyyayar dana nuna miki che tayi yawa hartasa kika sangarche haka? Tome nayi ma? Meyasa taju be kasanche haka ba, kayya! Ya Allah ga kulu nan, ya Allah ka shiryeta shirin addinin musulunchi, ya Allah karka azabtar da ita bisa abunda takeyi, ya Allah na yafe mata, ya Allah ka yafe mata, ya Allah karkayi fushi da ita, ya Allah kasata ah hanya madaidaichiya.......

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now