41

1.3K 67 1
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳




Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*




4⃣1⃣



                      

Achan bangaren shukuriyya kuwa tun bayan tafiyar haiydar daga qofar gidansu tachigaba da kukanta awurin, saida tayi me isarta sannan tanufi chikin gida abunta, tana shiga batareda ta kalli wurin da kaka take zaune ba tayi chikin d'akinta, ita kuwa kaka ganin yarda ta shigo tana zun6urar baki gaba yasa ta d'auke idonta akanta, tana mamakin miskilanchi irinna yarinyar......

Tana shiga daki wani kukan me qarfi yaqwache mata, tunani takeyi yarda akayi haiydar yasan batun fyad'en da akayi mata, saida kukan ya tsaya mata sannan ta janyo wayarta dake gefen gado, tunanin abunda zatayi da wayar kawai takeyi, wani bangaren zuchiyanta yana chemata ta kira umma taji yarda akayi amma saitaga hakan rashin kunya nerh, gashi kuma mashkur har yanxu fushi yakeyi da ita ballantana ta kirashi, sai kawai wayar taxame mata kamar wani madubi yanayin yanda ta tsaya tana kallan wayar, addu'oi takeyi achikin zuchiyarta har tafara jin sanyi sannan ta bud'e gallery d'inta tafara kallan pictures d'in Kamal, wanda bata ta6a gajiya da kallansu

"kaga abubuwan danaketa going through koh?, meyasa kabarni ya Kamal ?, meyasa ?"
Abundant tadunga furtawa kenan tana kallan hotan kamar da mutum take magana, tana kallansu har bacchi yatafi da ita awurin......


                  
             Shikuwa haiydar ikon Allah nerh kawai yakaishi gida, har wani jiri nerh yake d'ibarshi ahanya, saika rantse shaye-shaye yayi saboda yanda yake tangal-tangal ah titi, yana shiga gidansu kaitsaye dakinshi yanufa, tura karyayyiyar qofarshi yayi sannan yakutsa kanshi chikin dakin, yana shiga ya d'agata yamayar ya rufe, kai tsaye kan matacchiyar katifarshi mara isasshen soso yaje ya fad'a, har yanzu zuchiyarshi ta kasa lamunche mishi chewar shukuriyya itache yarinyar dayayi raping few years back
      hawayene masu zafi suka fara zubo mishi kan qunchinshi, ashe da gaske nerh kome ka aikata aduniya bibiyarka yakeyi?, wala alkhairi wala sharri,,,, shikam yaga chikakken misali akanshi, yarinyar dayafi santa fiyeda kowani mahaluqi aduniya ashe shine yafara lalata mata RAYUWA?, tunani yafarayi abunda ya rud'e shi har yayi raping dinta, tabbas ba komi bane fache sharrin zuchiya dakuma na shaid'an, sosai zuchiyarshi take mishi zugi abusa abunda ya aikata, yana danasanin tsautsayin dayajashi haryayi fashi ranar dakuma QADDARAR data afkomashi nayiwa yarinyar mutane fyade, baxe iya tuna wannan shine karo na nawa dayayi danasanin abunda ya aikata bah, abu d'aya zai iya tunawa shine tun ranar daya aikata abun yake danasani, kuma tun ranar beqara samun farinchiki ba ah rayuwarshi, komai yaxo mishi chikin rayuwarshi abaibai yake xuwa, kuma hakan yanada alaqa da chutarda yarinyar dayayi....

Tunani yakeyi sosai akan yarda xe 6ullowa al'amarin amma yakasa samarwa kanshi mafita, qwaqwalwar kanshi harwani zafi take mishi da rad'adi saboda yanda ya takura mata aqanqanin lokachi, jikinshi kuwa har rawa yake mishi saboda yarda fargaba tamishi yawa, lokachi d'aya wani irin zazza6i me zafi ya rufe shi, gawani chiwon kai me tsananin zafi, chikin qanqanin lokachi yafara fita ahaiyachinshi tayarda shikanshi besan awani irin hali yake chikiba, kafin zuwa wani d'an lokachi harya gala6aita......

Innarshi kuwa taji lokachin dayashigo chikin gidan amma kafin ta fito harya shige chikin d'akinshi, ganin hakan yasa ta koma tachigaba da harkar gabanta, har bayan sallar la'asar haiydar befito daga dakinshi bah, itakuma inna bata damu ta duboshi bah, domin inda sabo tasaba da halinshi na zaman d'aki, don wani lokachin saiya wuni adaki tun safe be fito bah, sai wuraren maghriba zaka ganshi ya fito, hakan yasa inna batayi tunanin komai bah ganin be fito bah.....

Sai da inna taga har anyi sallar maghriba haiydar be fito ba sannan jikinta yabata babu dad'i, tana idar da sallah tafito daga dakinta danufin shiga dakinshi tagani ko bacchi yakeyi, tanafitowa daga dakinta malam iro nashigowa gidan, dawowarshi daga masallachi kenan...

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now