page 32

1.1K 71 6
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Allah ka jikan mahaifiya ta ka gafarta mata ka yafe mata kurakuren ta

Ya Allah ka bawa mahaifina lafiya


Allah ka yafe mana laifukan mu kasa mu gama da duniya da lahira lafiya

Sakon gaisuwata ga daukacin fans na soyayya ko sha'awa

Mai dambu Allah ya Kara daukaka da basira

Mallakar Jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
*****************

P32

Not edited



Ko da maigadi ya bude kofar Bai ma tsaya ya ga ko waye ba kawai ya kau ce,ya bashi hanya.ashfaq ko da yayi ready ganin aleena Sai ganin wani almajiri yayi ya shigo,take ya saki wani uban tsaki mtssss ya harari maigadi da kallon shi Kuma wannan yaron fa?

Wallahi bansan shi ba ranka ya dade na zaci ma shi kake ta jira tun dazun ai,kaji mutum me zan tsaya na jira anan me zai yi mini,ni bansan shi ba.inji ashfaq.kai dan malam zo kafi ta kaji nan ba wajen zuwan ku bane kuyi wasa kaji ko,'saboda mu ba na Allah ba ne ba ko' ashfaq yace,sannan yace kalli almajirin yace zo nan,yaron ya zo  daga Ina kake ,na fito bara me Ina so na Sami abincin da zan karya da shi yunwa nake ji sosai ya fada Yana shafa cikin sa da tun jiya bai ci komai ba, subhanalillahi Kai wannan duniya yanzu Dan wannan yaron da bai wuce shekara shidda ko bakwai ba shi ne aka kawo shi bara cikin wani gari,yadda duniyar nan ta lalace  da ko dai a safe yaron ko ya hadu da mutanen banza su lalata masa rayuwa ya tashi a tutar babu,tunda ba karatun ba Kuma tarbiyar,yana gama maganar zucin sannan a fili yace menene sunan ka Dan asabe  ya ba shi amsa a Kai tsaya,ashfaq yayi murmushi to dan asabe ka rin ka zuwa kullum kana karbar abinci a nan kaji ,duk ka zo ka Sami maigadi zai baka abinci ka ci ka koshi Amman karinka zama a iya makarantar allon ku kawai ka dai na yawon nan,tab lallai kana so malam ya yi kasa kasa da ni ke nan,Sai jikin sa yayi sanyi ya zuba wa yaron ido wato shi kanshi malam din me take tura su yin bara Kai Allah ya kyauta,su malaman nan sun San ba zasu iya kula da yaran muta ne ba to meye na karbar su,su Kuma karbi kudi wajen iyayen su ko da yake dukka laifin na iyayen ne ai.

Ashfaq  ya cire dubu daya daga aljihun sa ya ba wa maigadi yace yaje ya siyowa dan asabe abinci kafin a gama na gidan,to ranka ya dade wa zai zauna a nan kafin na dawo Kuma ,ya Harare shi tare da cewa just go and do what I told you now kafiye surutu,a million maigadi ya fice ya bar gidan tare da jin dadin yadda ashfaq yake taimakawa mutane shi Allah yayi yo shi mutum ne shi Mai tausayi kamar iayayen sa,ohhh Allah ka bashi abokiyar zama saliha Mai irin halin sa kada ka hada shi da wacce zata ta zo ta canza shi daga wadannan kyawawan halayen na sa ya koma kankamau.
*******

Yau kam su madam Aleena an Sha barci don tunda ta tashi da kafin asubah za tayi alwala tadan yi nafilfil kafin lokacin sallah yayi Sai taga period din ta yazo ta koma ta cigaba da barcin ta kawai dama Kuma ba wani cikakken barcin ta Sami ba cikin dare saboda tunanin miskilin mutumin ta

Ummi tana zaune a saki suna Dan taba hira da Abba game da yadda yake samun saukin jikin sa,ta ga shuru aleena ba ta fito ba balle har ta Dan yi wasu abubuwan sannan ta wuce gidan hajiya Khadija Amma ba ta gan ta ta fito.abban su Ina zuwa don Allah zanje na dubu yarinyar nan yau Bata fito ba balle ta shirya  ta wuce can gidan,to Allah yasa dai lafiya,in Sha Allah.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now