page 26

1.2K 78 11
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Zauren jarumai writers association

Happy maulud! Happy maulud!

Allah ka karawa annabi daraja da daukaka.

Ya Allah ka jikan mahaifiyata da dan uwana garba kasa aljanna ce makomar su ka yafe musu kurakuran su.

Ya Allah ka bawa mahaifina lafiya  da yara na da duk wani wanda ba lafiya.

Sakon gaisuwa ta gareku fans din soyayya ko sha'awa wandan da na sani da wadan da bansan su ba, ina farin ciki da soyayyar ku gareni.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

Not edited

P26

Yana zaune yana ta tunanin nan abinda ke faruwa da shi, sai ga amir ya shigo dakin saboda mom tace "yaje ya duba ko lafiya bai kawo musu maganin ba suna ta jira ko shima jikin ne" ya ya dai doctor ko duk cikin soyayyar ce haka ka fada cikin tunani, wai ma tsaya malam ka gayamin garin yaya har dukkan ku ka gangaro  daga kan bene? Kuna gudun soyayya ne bakusan kun zo farkon step din ba sai kawai kuka fara gangarowa saboda bakwa cikin hankalin ku? Sai kawai ya kama dariya yau ina ganin ikon Allah, yau ashfaq kai ne ka fada cikin soyayya haka dumu dumu hahhhhhhh

Shi dai ko uffan bai ce masa ba don shi abinda ya keji ma ya ishe shi da wannan surutun.kai matsalar ka ke nan sai ana magana ta hankali sai ka kama ka kawo wacce ba ta hankali ba, cewa aka yi ma soyayya muke yi? Ko nace maka son ta nake yi ne? kawai dai the only thing i understand is"akwai wani abu da ke faruwa a tsakanin mu ko in ce a tare da ni da bansan menene ba" na kasa fahimtar abin, kuma akan ta ne nake jin wannan abun, ya ja tsaki mtssssss yarinya kawai ta zo za ta dagulamin lissafi na da hankali na akwance.

Man ka yarda dani ka amince wallahi ka fada cikin son aleena, son ma kuma zazzafa trust me.sai kayi ai ni dai ban ce ina son ta ba, ba kuma zance ba har yanzu banga macen da nake so ba tukun, har yaushe muka hadu da ita da zaka rinka cewa ai na fada cikin son ta? 

To na ji yanzu bani maganin na je na kai musu don a bawa matar ta mu ko fever din ya sake ta da wuri , kuma da alama dai yau ba zamu kwashi garar girki cikjn farin ciki ba don aleena ba dai iya girki ba.to meye na yabon ta haka  ya dalla masa harara, amir ya fashe da dariya to meye na harara ta ni dai ka ganni nan anyi mini mata so ba ma wacce zan gani tayi mini sai mai irin suna na 🙄

Ashfaq ya tashi yana dan layi ya dauko masa maganin don Allah ka je ka kai musu ni ka ishe ni da surutu haba, ya cilla mishi maganin shi kuma ya cafe, ya zo zai fita daga room din sai ya kira sunan sa ashfaq ina ga kawai zan canza sheka ne, me kake nufi ashfaq ya tambaye sa da yanayi rashin fahimta, to kaga dai aleena she is very beatiful and young kuma ga ta da shape mai kyau da ba kowacce macece take da irin sa ba sannan wannan ma tun yanzu ke nan ina da in ta kara girma kuma musamman dazu da aka cire mata hijab ashfaq ya gwalo ido zuciyar sa ta fara tafasa, to ina ganin kawai zan ko ma wajen ta in ce ina son ta kawai ya karasa yana murmushin tsokana, ai da gudu ashfaq ya dauki takalmin sa ya jefa masa amir ya sunkuya takalmin ya wuce ta saman kansa, abin bai masa ba ya runtumo a guje wajen amir, da guda amir yayi waje yana dariya yana kiran mom ki zo ki cece ni xai ashfaq zai illa ta ni.

Suka sauko kasan a haka, ashfaq na binsa, shi kuma yana kiran sunan mom, mom tace "meye haka ku kuma, ku ba kwa girma na, me ya hada ku haka" mom wai kawai don nace zan koma wajen aleena shike nan ranshi ya bace ya biyo wai ban isa ba, ya juya yadda mom ba zata gani ba yayiwa ashfaq gwalo😛 don so yake ya dan fara ankarar da mom akan alakar aleena da ashfaq din.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now