page 25

1.3K 81 3
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANUR RAHIM

Zauren jarumai writers association

Allah ka bawa mahaifina lafiya ka jikan mahaifiya ta kasa aljanna makomar ta ka haskaka kabarinta amin.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
***********************

Page 25

Not edited

Ina jiran amsar ki fa ta kara yin shuru , sai ji tayi ya wani kyal kyale da dariya, ke kar fa ki dauki magana ta serious da wasa nake yi miki fa, ina so kawai naga yadda zaki yi ne, hmmm kawai ta iya cewa amman jikin ta yayi sanyi don wani iri kawai take ji a jikin ta.

To ga lemon naka nan ni zan tafi kasa, no ki dan dakata don Allah akwai abinda nake so na tambaye ki in ba damuwa, kallon da tayi masa shi ya nuna masa cewa zata saurare shi don Allah wacce makarantar kike zuwa kuma ajin ki nawa yanzu?

"Ai ina ganin wannan bai shafe ka ba akan abinda ya shafe ni" to ai abinda ya shafe ki ni ma ya shafe ni madam, to ta ina ya shafe ka? Yayi shuru (yarinyar nan ta na da wayo ya fada a ransa) saboda ke sister din kawata ce kuma kanwata afnan kin ga kuwa abinda ya shafi afnan ai ya shafe ni, to ni bansani ba! Sai kaje ka bincika ai ta harare shi, to kika sani ko na bincika din amman bakomai zanje na kara bincikawa din madam.

To ka ban hanya zan wuce ko "ga abinda kace a kawo maka zaka sha baka sha ba ka tsaya kana ta surutu" eh ai ke kika koya min surutun don ni ba ma'abocin magana ba sai a kanki, wai yau me yake damun ka ne? "Ni ma bansani ba fa don Allah ki taya ni binciken abinda ke damuna pls! Ki hakuri kuma da abinda amatullah tayi miki, ta kara hararar sa yace eh bakomai tun da ni na janyo miki ko? To nan gaba ya za a yi ke nan, kamar ya nan gaba ta tambaye shi, no bakomai kawai ina fatan dai kawai komai ya zo mana cikin sauki.

Salamu alaikum amira ta bude kofar tare da yin sallamar ni fa ya ashfaq ban.... Bata kara sa ba maganar ta makale mata ganin yadda suke, ita kuwa aleena wata irin kunya ce ta kama ta ta yadda amira ta riske su, amira ta kalli
A

shfaq tace " ya ashfaq ya dai" nothing ya mayar ma ta don shi ko a jikin sa, tasa dariya kawai tana hasko wani abu a zuciyar ta.

Ni fa na duba na duba ko ina axikin motar banga takardun da ka ce ba, is ok ma lil sis kije kawai na duba anjima yanzu ina son nayi wanka ne, ok ta juya zata fita aleena tai saurin ce ma ta ki tsayani ma na mu ta fi tare, dama tare kuka zo ne da ita da zaki ce ta tsaya? Amira ko na jin haka tai sauri tayi gaba tana murmushi.

Wai don Allah meye haka ne meke damunka? Ka kyale ni na wuce mana ni ban ma ji dadin yadda amira ta zo ta same mu ba saboda bana son zargi a rayuwa ta kar ta dauke ni mai wani hali daban! Ko? Yace mata, wallahi zan ture ka na wuce idan ka fadi kaji ciwo ba ruwa na," you are welcom dear "ya ce mata har da wani bude hannu, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, to ko dai dama dan iska ne iskanci yake son yayi da ni, eh fa haka ne gaskiya in ba haka ba meye na wani tattareni haka tana ta tunani, nan zuciyar ta ta kara amince mata ai ga abinda ya ke son yayi da ita.

Sai kawai ta fashe da kuka " don Allah ya ashfaq kar ka aikatamin haka karka raba ni da kima ta wallahi in ma don ina yi ma rashin kunya ne na dai na ba zan sake ba don Allah" me ashfaq zai yi in ba dariya ba sosai ya rinka kyal kyalewa da dariya har da rike ciki lallai yarinyar nan yarinya ce ga kuma tsoro she is innocent, i like her.da ya gai ta cigaba da kukan ne yace ke tsaya me kike tunanin zan yi miki ne?ni dai na roke ka da Allah ka bar ni naje gidan miji na lafiya, hahhhh to waye mijin na ki?

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now