page 47

1.2K 69 29
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA

ALLAH YA KARA MANA LAFIYA DA ZAMA LAFIYA

AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION I LOVE YOU ALL.

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
*******************

P47

...... A yadda take kallon cikin kwayar idanun sa tana hango tsakanin bacin rai da kishi karara a kan fuskar sa,

Ta kawar da kanta kasa tare da cewa "me ya kawo ka Ina ce ka gama aikin da za kayi ko?ko akwai abinda baka isar ba shiyasa ka kasa hakuri Sai ka zo ka ga yadda zamu kare da wannan Annur din? To ka kwantar da hankalin ba  damuwa zan rike shi da hannu bibbiyu Kuma zan so shi tsakani da Allah kamar yadda zuciya ta ta riga ta Kani da son wani,zan yi kokari na cire wancan daga zuciya ta da ruhina na maybe gurbin sa da Annur tunda shine yake Sona tsakanin sa da Allah"

Za ta juya ta koma Saurin dakatar da ita saboda yadda zuciyar sa take 'kuna da Kuma kasan fahimtar ma abinda take cewa
Ki tsaya pls ni ban ma fahimci abinda kike nufi ba da wadannan maganganun naki Angel,ni ya kamata raina ya baci saboda yadda na zo na ganki tare da wani,alhalin na gaya miki cewa zan zo.
Ta zare ido "ni yausheka ce min zaka zo,bakayi  wannan maganar da ni ba ya Ashfaq in dai Kuma ba so kake ka raina min hankali ba,ni kike gayawa haka 😳 lallai wuyan ki ya isa yanka kafin ma na cigaba,wannan can wanene  kike hira da shi har kina wani wage masa baki yana ganin murmushin ki da ni ka dai ya kamata ace ni kike yiwa shi,ta Dan harare shi,a matsayin ka na WA ke nan da Kai kadai zaka ga murmushi na Kar ka manta fa har yanzu a market nake fa, ba igiyar kowa akaina malam,a matsayi na na mijinki Mana tunda lokaci kadan ya rage a daura Mana aure ko?
Aleena tasa wata irin dariya ta raining hankali tace"au Allah miji ko Kuma mijin bogi da zaka sa naji kunya na kuntatar IYAYENA to gwara tun lokacin na tsaya na fidda gwanina ranar da za a rataya ma igiyoyi nima a rataya min.
Ashfaq yayi shuru tare da dafe kansa yana fad'in innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

Shi kuwa Annur momy tana daukar wayar Bai ko tsaya gaishe ta ba ya fara tambayar ta "momy a Ina ma wannan kawar taki take aminiyarki wacce ki kayi naje na gaishe ta naki?"

Momy tace to me ya faru Kuma Annur ko zumunci zakayi ne yau?eh momy Ina so yau na fatan ya Miki Rai ne in yu Miki abinda kike so,ah ah to masha Allah ai kuwa da na ji dadi sosai ma kuwa,nan tayi masa kwatancen gidan su Aleena da ke nan unguwar tudun yola,to ya sunan kawar taki ?
Sunan ta zai Sai yaran ta biyu mata,babbar ita ce Aleena Sai karamar Kuma Afnan.
Momy ko ita ce wacce kike cewa naje na ganta ko zatayi min ki hada mu aure?
Momy ta Dan yi murmushin manya ita ce Mana Annur,amman yanzu...Annur ya katse ta ya isa momy bari zan je gidan na su yanzu zan gaishe su,Sai ki fa'dawa aminiyar taki,me suke ce mata?umma suke Kiran ta da shi.ok momy tanks I love you ya katse wayar sannan ya koma jikin motar sa.
Momy ko abin ya bata mamaki mutukawai Annur ne yake cewa zai je yayi zumunci hmmm to Allah ya Kara shiryar min da Kai,sannan ta kirawo umma take gaya mata yau dai Dan ta Annur zai zo ya gaishe ta yanzu ma,umma ta ji da'di sosai ta ce to Allah ya kawo shi lfy,ya Kara shirya Mana shi,Amin sannan sukayi sallama kowa na kaunar 'yaruwarta,umma a zuciyar ta tace bazan taba mantawa da irin taimakon da kukeyi mini ba kawata,ba abinda zaki nema a wajena na kasa yi Miki shi mutukar Ina da iko a kan abin.

Su kuwa sunan can suma ta rigima gaba daya ta cazawa Ashfaq Kai da maganganun ta,shi yana kokarin ya fahimtar da ita cewa shi Bai turo  kowa,shi yake so ya turo kansa da kansa amman gaba daya taki yarda,saboda yadda zuciyar ta ke yi mata zafi da Kuma Sai take ganin abin a matsayin raining hankali ma yake yi mata.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now