page 51

896 60 16
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKUREN SU KA SA SUN CIKIM DAUSAYIN ALJANNA

MALLAKAR JAMILA(Maman Amir)

WATTPAD@jami1020
********************
B

an manta da ku ba wadanda suke kirana a waya da masu yimin text akan suna jirana fa nayi sabon posting dukkan ku na gode da wannan kauna agareni ni ma Ina kaunar ku sosai😘

Ina mai mutukar ba da hakuri da rashin jina da ku kayi na kwana Goma don bana ce kwana biyu ba,abubuwan sunyi yimin yawa don da Ina tunanin ma na ajiye labarin tunda Yana da yawa Kuma bani da lokaci.to ganin yadda mutane suke ta kirana da yimin text na ce to bari nayi kokari dai na Kara sa labarin Amman zan Yankee shi ne kawai(ko kuwa ya kuka ganiina jiran Ra'ayoyin ku)saboda akwai wani labari da na fara Shima Ina so na gama shi Amman shi ban ma farayin posting ba har sai na gama sannan zan sake,Amman shi in Sha Allah zai kasance paid book ne(ga masu cewa na mayar da soyayya ko sha'awa paid book, to ku saurara paid book dina Yana nan tafe In Sha Allah 300 ne kacal sai anuna min kauna😘)

P51

Yan mata ne da yawa kowacce ta ci kwalliya sun sa ankon sky blue lace da Kuma purple net a kansu kowacce ta na nuna ita ce ta fi haduwa ga motoci a jere acikin layin nan saboda yawansu ma bazan iya ƙirga su ba,

Yan mata sai shiga cikin motocin suke yi ana tafiya da su wajen party da wannan motar ta tashi sai wannan ma ta tashi har da aka ga ma kwashe ƴan matan amare abinda ya rage kawai amare za a ɗauka,nan na hango anty da wasu sun sha purple shadda rantatstsiya sai ɗaukar ido take yi na karasa wajen da sauri na hmmm suwa zan gani...ASHFAQ ne da Amir sun sha huluna da wasu irin agoguna na gwal fuskar su tana shinning na nuna cewa su angwaye ne sunyi kyau sosai ga su farare amman Ashfaq ya doke Amir nesa ba kusa ba don shi sai ayi tunanin irin balaraben nan ne yayi shigar kayan hausawa faɗin yadda sukayi kyau ma dai ɓata lokaci ne (maman sultan dai sa baku labari don nasa suna wajen party tuntuni dasu besty).

"Kai wai me yake damun ka ne Ashfaq duk ka wani canza haka wata jarabar ne ke da mun ka ne?Amir ko dai kun je kun Sha wani maganin ne da har ya ke sa ku wannan jarabar,nace kuyi hakuri motar ku daban motar Amar'e daban idan kun isa wajen party sai ku fito tare Amman ka wani kafe haka kace Sam baka San zancen ba Kai da amaryar ka zaka tafi,yau Kai ma Amir har da Kai ayi min musu saboda ya Koya ma tantiranci."
Ahsfaq ya juya bayan shi yadda ba zai Kalli fuskar ta ba sannan yace"wallahi kin ji na rantse sis idan har ba da Aleena ba to wallahi ba zan je wajen party ba"
"to nima dai kusan haka ne aunty Hassan dina yace kaza dole na bi shi"shi ma amir ya mayar mata

Yau na shiga uku da yaran nan ni wallahi tsoron na hada ku da yaran mutane nake yi acikin mota ku kadai.ta fada da yar damuwa a fuskar ta.Ashfaq yace acikin zuciyar shi "da yake cinye su za muyi ba"mtsss
"Wai me ya ke faruwa ne?ya ku har yanzu ba ku tafi ba,ni fa bana son ayi Daren nan don Hakan ba shi da fa'ida"yawa dad gwara da ka fito in ji Amir kawai ya je ya rungume shi da shagwaba,dad ya Kalli Ashfaq ya ga fuskar shi a murtuke alamun ran shi a bace yake ita ma Aunty akwai alamun dumuwa a fuskar ta,sai ya dawo da idon sa kan Aunty Yana tambayarta meyake faruwa da fuskar shi.
Dad wai su lallai sai an basu Amar'e sun tafi tare da su nace su bari ni zan taho da Amaren sun ki yards shine duk suke ta wani fushi har rantsuwar akayi min in ba da su ba ba za su je ba,shi Kuma ji yadda wannan ya zo ya kanainaye ka don a ce nayi musu laifi ta karashe tana Dan zumburo baki na shagwaba.
Dad yayi dariya yace iKon Allah to ke an taba yin haka yara da matan su kice ba zasu tafi tare da su ba haka kawai,to dad ai naga ba a daura auren ba sai gobe Kuma wallahi dad kan su rawa yake yi.to na ji yanzu sai ayi musu alfarma a basu su tafi tare ku Kuma ku kiyaye don naga kan ku Yana rawa ya Kara she maganar cikin dariya,sannan ya Kalli Amir yace to yanzu dai a sake ni haka nan nasha iska tun da dai yayar ta ku ta yarda,ya Kalli Ashfaq ma yace to wani dai sai a saki fuska haka nan lokacin biki so ake a ga ango cikin murmushi a ko da yaushe,hhh. Ashfaq ya zo ya rungeme dad yace tank you dad,you are wlcm sons Amman a kiyaye Allah yayi muku albarka suka amsa da Amin.sannan ya wuce Aunty ta juta ta Harare su sannan ta wuce cikin gidan domin fito da Amaren,eh mun ji dai koma me zakiyi kiyi. Ashfaq ya fada a hankali don Kar ta ji,shagen kaya wato Kai ka ma fini matsuwa ke nan to wallahi kayi a hankali ba a dai daura ba tukun Kar ka je ka turmushe yarinya acikin mota wata irin harara Ashafaq ya banka wa Amir tare da cewa saboda nine bunsuru kamar ka ko?,Amir ya kyalkyale da dariya eh na ji din ai gwara ni Ina nunawa a Fili Kai kuwa fa sai karin ka nunawa abin Bai dameka ba Kai na Allah ne bayan Kuma ba haka ba ne ba,Amir dai Yana ta zuba ya ga ashe shi ba ma kallon sa ya ke ba hankali sa Yana ga wani waje "Masha Allah"Amir ya ji Ashfaq ya fada ai nan da nan ya juya wajen da ya ga Ashfaq na kallon nan ya hango su Aleena da Amira an fito kowaccen su ta Sha purple shadda gown Amman kasan rigar ansa lace sai hannun shi ma an sa purple lace sannan daga bayan dinkin an dauko purple lace din da ya ji stones ga flowers din kanana an hade musu da rigar sai ya tashi kamar alkyabba ce a jikin sai gwargwaron su golden sun ci wasu dan Kara dan karar sarkoki na zinare da awarwaro da Dan kunne,takalman su ma golden ne da yar jakar su golden Kai fadin ma kyan da suka yi sai muga ma shafin nan ma bamu gama ba,sunyi kyau har sun gaji ga su farare ga Kuma gyara da suka Sha more especially ma Aleena ta karayin wani jajir da ita kamar kana latsa fatar jini zai fito,suna ta kowa a hankali a hankali sai kace sun hau kan stage.

Shima Amir shagala yayi da kallon su Yana Yana ya ba kyawun su a zuciyar shi,sun GAF da za su Kara so ne sai ya kama yiwa Amira signal yasa hannayen shi dukka guda biyu akan kirjun sa dai dai zuciyar sa sai Amira ta Dan Harare shi sai duk suka Kara sa dariya,anti kawai girgiza Kai tayi saboda abin nasu ta wuce abun magana

Doctor kuwa ya kasa cewa komai kawai kallon ta yakeyi Yana godewa Allah abisa wannan ni'ima da ya bashi duk da dai ta wani bangaren na zuciyarsa Yana Dan jin haushin ta akan yadda ta biyewa anti taki yarda su hadu wajen kwana hudu Bai sa ta a idon sa ba yayi bin har ya gaji yace Kuma Sai ya rama wannan wulakancin da tayi masa,ga hudu bar da anti ta ke musu wai Kar su saki jiki da mu mtssss,sai yayi sauri ya kauda Kansa daga kallon da yake mata Yana fatan Allah yasa ma ba ta ga kallon da yake mata ba(Kai kuji fa zuciya na so ta kalla Amman ana hanata ba cin Kansa take yiwa.hahhhh)

Suna Kara so wa wajen su kafin anti tayi magana Amir ya rigaya da cewa ohhh janiman kinyi kyau wallahi sosai fa kamar irin indiyawan nan,wacce tayi muki kwalliyae nan gaskiya ta cancanci kyauta ke ma Kuma da ta Taki kyauta yayi mata kiss ta hura iska,ita kuwa Amir tayi sauri ta cafe tasa a kirjin ta tana ta murmushi,Anti tayi sakato tana kallon su Imani yayi mata yawa ta ma rasa abin cewa Sai ta juyar da idon ta wajen miskilallun nan Sai ta ga shi Yana kallon wani gefe ita Kuma ta Kalli kasa,hmmm to ga sunan na kawo muku su kowa ya shiga motar sa ku Kuma na ja muku kunne Kar ku manta abinda na ce muku especially ke Amira na ga kan ki sai rawa ya ke Yi idan kika Yi wasa to wallahi zai fara hayaki ni Kuma ba na nan balle
N

a zuba Miki ruwa ya dai na Sai mun hadu a can zan jira ku don nasa har na isa ma kafin ku je.

Sai ga ya Ammar ya fito rike da yaran sa "wai ke Ina kika shiga Ina ta Neman ki?"

So sorry sweet heart mu tafi kawai lokaci na kurewa,nan ta tafi ta bar su a wajen,Ango Amir yayi sauri ya budewa amaryar shi kofa ya ce "Bismillah"tayi mishi fari da ido sannan ta shiga cikin motar ya rufe ya koma daya bangaren ya shiga ya zauna,Yana jira motar su Ashfaq ta farayin gaba sannan ta su din dama haka aka tsara Sai ya ji shuru,Amira ta tabo shi ta ce Kalli mutanan mu.kyale su sayi sa gama ki juyo kalle ni yau ba za ki Kalli kowa ba sai ni yay rana ta ce duk sai sukayi murmushi.

Ashfaq Bai ce mata komai ya juya ya bude motar sa ta wajen inda zai zauna ya shiga ciki ya kawar da kan shi can dai ya ji shuru bai ga Aleena ta shigo ba.lekowar da zai kawai sai gani yayi ta juya zata koma,ya zaro ido a million yayi wuf ya bude kofar motar ya je ya Tari gaban ta ya tsaya ita Kuma kawai ta kau da kan ta zan ta can za hanya,sai ganin shi tayi ya tsugunna ya daga hannayen sa biyu alamar roko Yana bata hakuri da idanuwan sa zuwa 30 seconds Sai ta juya ta koma wajen motar ta tsaya ta na jiran sa da sauri ya ta so ya bude mata motar tare da cewa plsss da sansanyar muryar sa da take nuni da roko,ta girgiza Kai ta shiga cikin motar ya rufe motar har da ajiyar zuciya" thank God" yace sannnan ya za gaya ya shiga cikin motar yacewa driver su tafi.

Amir ya kwashe da dariya gain drama da ta faru a tsakanin su yace ato ka gayawa mace Jan aji wa ma yake jawa amarya aji in ban da abin Ashfaq.hahhhh

"Yauwa ga sunan sun ta so yanzun nan sai ayi abin yadda aka tsara bana son wani mistake in ba haka ba to a kudin ku.
*****

Wallahi na gaji da rubu ma hadu a next page,idan naga yadda ruwan comments da vote

Sabon littafi na Yana nan tafe in Sha Allah Amman paid book ne sai a fito anuna min kauna.(KE CE RAYUWATA )sunan book din ke nan akan 300🌹💖

Comment

Comment

Share, vote and follow me on my Wattpad tanks

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now