p55

1.2K 45 10
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU KA HASKAKA KABARIN SU KA YALWATA KABARIN SU TARE DA YAN UWA NA MUSULMAI

MALLAKAR JAMILA (MAMAN AMIR)

WATTPAD @jami1020
*********************

Ina godiya gareku masoyana da bakwa gajiya da ni,a ko da yaushe kuna jiran Kuga sabon posting dina especially Yan Wattpad 😘😘😘Ina yin ku irin sosai din nan fa.

Sannan da sabon book dina KE CE. RAYUWATA Yana nan tafe kamar yadda na gaya muku Amman paid book ne 300 kacal ta wannan acct din za a tura Jamila ibrahim zenith bank 2008237969.sai atura da shaidar biya ta wannan number 07038185042.pls ku Taya ni sharing.tanks.

Last page
******

A can police station ba irin dukan da ba ayi wannan mutumin ba Amman ya ki ya yi magana ballanta na ya fadi dalili da yasa har ya aikata wa Amatullah haka don asamu irin masu mugun taurine Kannan
Sunyi da waje wa cewa idan aka kama su ita Amatullah ita za ta zo ta Ciro su daga cell ko Kuma su tona mata asiri nan da sati daya bayan kama su.
****

Shalelan Alhaji ne kawai a kwance a kan gadon asibiti an sa masa oxygen ga mommy tana tsaye ta wajen window saboda ba dama su shiga ciki sunyi zugum zugumhawaye kawai ke zuba a idanun ta sai addua kawai da takeyi acikin zuciyar ta akan Allah ya bawa Dan ta lafiya ya Kuma shirya shi,Alhaji ya matso kusa da ita zai taba domin ya rarrashe ta tayi sauri daga masa hannu tare da banks masa wata irin harara"ka sani idan har na rasa yaro na to wallahi Sai Allah yayi Mana hisabi da Kai saboda duk a dalilin ka ne Annur ya ke cikin matsalar nan"sannan tayi shuru zai Kara magana ta daga mishi hannun manuni tare da cewa "I warned you don't say anything to me"ganin yadda idanun ta sukayi da Kuma yadda take masa tsawa shi ya sa yayi sauri ya kame bakin sa gum saboda tunda suke ba ta taba yi masa musu ba ballantana tsawa.

Sai ya ja baya ya zauna ya fara karatun ta nutsu ya Kuma yarda cewa duk shi ne ya bata yaron sa baya taba nuna masa cewa wannan shi ne abu mai kyau wannan ba shi da kyau sai dai ya kyale shi yayi yadda yake idan Kuma maman ta rsawatar masa ko ta nuna masa abinda yayi Bai kama ta ba sai kawai ya hau kan ta da fada,Yana cikin tunanin nan sai ga hawaye sharrrr ya zubo masa Yana fada a zuciyar sa "gaskiya na cuci Kai na da yaro na da Kuma mata ta,mata ta saliha ce ga tsoron Allah ga bin duk abinda nace mata Amman duk na man ta da wannan na butul cewa ubangijina na manta da wannan ni'ima da yayi mini,nabi son zuciya na manta da bakowa ne Allah ya ke azurta shi da mace ta gari ba"ya Allah ka yafe mini ka tashi kafadun yaro na,Allah na tuba,Yana ta goge hawayen sa Yana ta Kara yin istigfari.a washe garin ne Kuma a ka daura auren su Aleena da Ashfaq.
Sai wajen yamma Mommy tana tsaye sai ta ga Dan yatsan shalele Yana motsi da sauri ta ce "Alhamdulillah " sai duk a ka taso kanta ganin abinda ta gani da gudu Alhaji ya tafi kirawo doctor Yana share hawayen sa da yake zuba na farin cikin farfadowar yaron sa.

A can bangaren kuwa ana nan ana ta Shan shagalin biki don ma rashin lafiyar Amatullah ta Dan katse wasu abubuwan,ga abinci nan da abin Sha kala kala sai Wanda ka zaba Kuma yadda abin ya Kuma kayatarwa shine mom tace su hade bikin waje daya kawai to Sai akasa samu wani Kato kango nan kusa da su to kowa ya dwbo tawagar sa can zai je ya jibge har da su kan su Amaren,Ina Kara kutsa Kai na ta wajen kawayen Amar'e na hango Yan group din SOYAYYA KO SHA'AWA suna brush da cinyoyin kaza ga juice a gaban su da robar faro sun dauki sanyi sosai can na hango besty na ita cinyar kaza ma biyu ta hada tana brush maman sultan na Miata magana ta kicsauraron ta wai a kyale ta yau ranar farin ciki ce bikin Aleena da Ashfaq don ta Dade tana jiran bikin nan Amman ba ayi ba sai yanzu

Nan a Yan group din Wattpad suma sukayi caa akan ta wai suma har da su a jiran bikin😜 sai gashi sun tashi da sauri samhat Banat har da Ture ni wai za suje daukar hoto da Aleena Kuma ba za Subaru wajen har sai an Kai ta dakin Ashfaq nace to ai sai ku cigaba ni na tafi daukar rahoto😀😂

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now