page 49

1.1K 75 25
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KA SA ALJANNAH CE MAKOMAR
SU TARE DA 'YAN'UWA MUSULMA.

Ba zan manta da ke ba mai dambu Ian Kara godiya ba iya ka

P49
  Not edited

.......yadda gaban ta yake ta faduwan nan tasan shine a kusa da ita Amman taki ta juya don tana jin haushin sa sosai.
Da hannu yayi wa Amira alamar da wuce ta basu wuri,ta tashi tana murmushi tace to sis Allah ya huci zuciyar ki ya yayyafa mata ruwan sanyi ga dalilin fushin nan ya zo.
Galla mata harara kawai tayi ba tare da tace komai ba,Amman can cikin zuciyar ta tana Dan jin sanyi a cikin ta.

Ya zo gaban ta ya tsaya ta juyar da kan ta,ya Kara komawa d'aya side d'in Sai ya Kara komawa wani side d'in,shuru shuru bata ji ya Kara biyo ta ba juyowar da za tayi kawai sai ta ganshi yana rike da kunnuwan sa Yana up and down alamar ba da hakuri tare da langwabar da kan shi irin a tausaya masa din nan.

"Sai kayi sau biyar sannan zan hakura da alk'awarin siyo min ice cream 🍦 babbar roba"

Da Bai ce komai ba Amman tunda ya ji tace ice cream babbar roba ai Sai ya wani zare ido Ina laifin karamar roba.

" Oh to shike nan tunda ba zaka siyo ba,bazan hakura ba"ta cuno baki waje ta juyar da kan ta

Sai tayi masifar yi masa kyau tare da jin wani yarrrr a jikin sa nan da nan yayi nodding kan sa,har yanzu Yana rike da ears d'in sa
K

o da zata jiyo Sai ta ga Yana rike da kunnuwan sa Yana up and down alamar ba da hakuri Yana Kara langwabar da kan shi,Yana tura mata sakon tayi hakuri fa yayi laifi ba zai Kara ba.

Sai kawai abin ya bawa Aleena dariya Sai ta hau yin dariya tare da cewa to shike nan Amman Sai kayi Sau biyar sannan zan hakura.

Ya zare ido waje yace "are you serious?"

Da ido ta amsa masa da cewa yes

"To ya zan yi ni mijin kan tace tunda dai ina so my Angel ta huce,Amman fa idan na gama zan baki wani labari da Sai kin ji kunyar wannan punishment d'in da kika sani,Kuma idan kafa ta tayi ciwo ke ce zaki yi min tausa har Sai ta dai na ciwo"

Ta Kara d'aga kafad'a irin ba ruwan ta d'in nan,sannan. Ta fara counting da hannun ta,alamin dai dole fa Sai yayi don gashi har ta fara k'irgawa😊

Da ya ga dai ba sarki Sai Allah Sai ya tashi din ya fara,ya na yi tana k'irgawa har dai ya Kai biyar sannan tai wani mugun k'yalk'yale wa da dariya saboda yadda ya ha'da gumi a fuskar sa,ya zo kusa da ita ya zauna

Yana yace "ash Allah na ba ki ji baya na ba da gwiwowina ba ciwo"ya d'an b'ata fuska

Kai dai wallahi rago ne daga d'an wannan abun shine har ka gaji Tabb

Oh ni ki ke cewa rago?ya yi kyau yarinya lokaci k'alilan ne Yana zuwa da zaki ga ne ni ba rago ba ne jarumi ne.yana karshe maganar ya saki wani lallausan murmushi da yake da ma'anoni da yawa,don ba abinda yake tunanowa Sai zuwan wannan lokaci, jiya yake kamar ya janyo shi.

"Me ka ke tunani?"ta fa'da in a low voice da ta Kara kashe masa jiki

Ya saki wani wahalallan numfashi ba komai Angel

Are you sure?takara tambayar sa tare da d'aga masa gira
Shi dai ya kasa cewa komai Sai nodding kansa yayi.

Can dai da ya samu ya dai-dai ta kan sa,sannan ya iya cewa "Ina ta ya ki farin cikin gama makaranta da kika yi Allah ya sa albarka yasa zaki amfana da shi da yaran mu ma su amfana da shi my Angel"

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now