page 44

1K 71 10
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA.

SAKON GAISUWA TA GA DUKKA FANS DINA NIMA INA YIN KU BA IYAKA,MASU KIRA DA MASU TEXT😘

DAGA KUNGIYAR AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA KARA DAUKAKA.INA YIN KU SABODA HADIN KAN KU

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
*******************

ALLAH YA KARBI IBADUN MU YA KUMA YAFE MANA KUSKURE DA MUKAYI ,YA BIYA MANA BUKATUN MU NA ALHERI YASA MUNA DAGA CIKIN 'YAN TATTUN BAYI .

BARKAN MU DA SALLAH🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉💐💐💐💐🍬🍬🍬🍬🍭🍭🍭🍭🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🍏🍏🍏🍏🍦🍦🍦💖💝💝😃😃😃😃😃💖💖💖💖💖💖

P44

Annur dai yana zaune cikin mota duk haushi da bakin ciki ya cika mishi shi ciki,don gani ya ke kamar da gayya Ashfaq ya ke yiwa Aleena haka,shi Kuma gashi Yana fa man jiran su don ya matsu ya San gidan su yarinyar da Kuma samin wacece ita.shi abin ma mamaki ya ke ba shi Wai akan mace yake ta Shan wahala haka har da Mari😂

Shi kuwa Ashfaq da kyar ya bar wajen motar fuskar sa Sai annuri take fitarwa don Yana cikin farin ciki mutuka,ya Kuma tabbatar wa kan sa cewa ita ma Aleena tana son sa,so ba zai wani Sha wahala da ya gaya mata za ta ce yes.

A haka ya Kara sa ciki ya karbo musu icream din roba biyu ya fito waje, kafin ya karasa wajen mota Sai ya ga wani yana wa wani dan tsoho fa'da Wai ya dame shi da bara,tsohon ko ya kafe ya ki tafiya Yana ta faman rokon mutumin.

Ashfaq ya fasa zuwa wajen motar su ya nufi wajen su,"salamu alaikum,Wai me yake faruwa baba?"Ashfaq ya tambayi tsohon.kafin ya bashi amsa Sai wannan Alhajin ya ce"bari Kai da Dan samari wannan mutumin ne ya ishe ni da bara Wai Sai na taimaka masa da wani abu zai siyawa iyalina shi abinci Sai kace ni na haifa masa,nace ya tafi ya bani waje yaki bansani ba ko Sai yake idan na tayar da motar ya shiga gaban motar yace na bige shi don na bashi wani abu mtsss"

Ashfaq ya girgiza Kai kawai ya ce "to Allah ya baka hakuri ka ja motar ka kayi wucewarka Alhaji"

Bayan tafiyar Alhajin ne ya kalli tsohon ya ga ba ma wani tsufa yayi sosai ba da zai tsaya yayi ta faman yin bara ana wulakanta shi,ya kamata ace Yana neman na kanshi duk da dai yanzu kasar nan ta lalacewa in ma ka nemi aikin da kyar zaka samu,ya furzar da iska daga bakin sa

Ya sa hannu a aljihu ya deb knowo kudi Bai ma San ko nawa ba ne ya mikawa tsohon,jikin sa na rawa yasa hannu ya karba har da rissinawa da Sauri Ashfaq ya tare shi tare da nunin a'a,

"Yaro Allah ya sakama da alkhairi ya biyaka da jannatul firdausi ya raya maka yaranka da zuri'ar ka baki daya hakika da akwai irin ku da yawa a duniya da mu talakawa bamu Sha wahala ba a rayuwar nan,na Sami abinda zanje na ciyar da iyali na

Kwana biyu,na nemi aikin da zan yi na rasa,shi yasa nazo nake yin bara ko Allah yasa na Sami Wanda zai ji Kai na,Kai wannan duniya Allah ya iya mana Sai kuma ya fashe da Kuka"

Baba idan ba damuwa zan tambaye ka,Ina jinka yaro,yauwa dama idan har zaka amince zan sama maka aikin gadi a cikin asibitin mu in ya so Sai ku rinka shifting tsakanin ka da daya maigadin.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now