page 3

2.3K 100 7
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir rahmanur rahim

Allah ka gafartawa mahaifiyata kasa aljanna makomarta tare da wadanda suka rigamu gidan gaskiya.

Jinjina gareku adda ramla da Khadija Khalid Allah ya saka da alkhairi.

Mallakar Jamila(Maman amir)

Wattpad @jami1020
******************
P3

Kuuuu ka ke ji ashfaq ya taka birki yayin da ita kuma aleena tayi sauri ta tsugunnah don kuwa tayi mugun tsorata kuma ta kasa tashi tsaye shi kuma ashfaq yana cikin mota yana jiran ta tashi ya wuce ita kuma taki tashi ranshi a mugun bace ya fito cikin zafin nama yana cewa ke ba kya gani ne bakya jin horn ne kika kama kika shiga gaban mota ta so kike na bigeki don kiyi mini sharri aleena tana kasa a tsugunne tana jin irin yadda yake zazzaga mata masifa ranta ya baci ta Ga shine da laifi shi ya kama ta ma ya zo ya bata hakuri Amman ya tsaya yana yi mata fada ta ce yo ita kuwa ba za ta tashi ba sai ji tayi yana cewa Idan baki tashi ba zan daga ki na wurgar dake nan ma shuru ba ta koyi motsi ba tana kissima irin rashin kunyar da zata yi masa duk da dai ba halinta ba ne kawai ba tayi an kara ba sai ji tayi tana yawo a cikin iska ya Dan gwarar da ita gefe yana karkade hannun sa yana cewa dirty girl tasa na taba jikin ta da hannuna mtssss har ya juya zai koma mota sai ji yayi ta finciko shi da duk karfin da Allah ya bata Tass ta bashi gud slap a tsadaddiyar fuskar sa ya dago ya kalleta ta kara masa wani ta na cewa how dare you touch me who do you think u are da zaka sa kazamin hannunka ka taba jikina.
Shi ko ashfaq yana dafe da kuncin sa imani yayi mishi yawa yau shi yarinya karama ta mara ya dago da niyyar ramawa nan idanun su suka gauraya dana juna ya tsaya yana kallon cikin idanta ita ma tana kallon cikin idon sa wajen minti daya ba Wanda ya sauke idanun sa daga na juna sai can tayi tsaki ta kauce taje ta dauki sabulun da ummi ta aike ta ta siyo ta wuce ta bar shi a wajen zuciyarta tana kuna wai yau wani namiji ne da ba muharra min taba ya tabata har da kwallar ta.

Ashfaq yana tsaye wajen ya ma rasa ma abinda zaiyi kwata kwata wai yau shi wata yarinya ta Mara kaii tab kuma wai ya tsaya bai rama ba yayi mata dukan tsiya ya kama ta tasa a rufe ta a police station nan da nan yayi saurin juyawa amman ya nemeta kasa da sama to ina ta shiga cikin gidajen nan ko daya daga cikin yan aiki ce nan yayi kwafa ya shiga motarsa ya wuce zuwa wajen daurin auren ranshi a mutukar bace idanun sa sunyi ja yana kissima irin abinda zai mata duk ranar da suka hadu
********************

Ita kuwa aleena tana isa gida tana yin sallama ta shiga ciki ummi ga sabulun yanayin da tayi magana zaka fahimci ranta a bace yake sai ummi tace ke kuma ke da wa kawai sai ta fashe da kuka tana cewa ba wani ne a cikin mota ya kusa bugeni ba kuma ya zo yana ta faman yimin masifa ta fada cikin sigar shagwaba tace subhanalillahi ummi fa wai don na ki tashi shine ya dauke ni ya ajiye ni gefe ni ni kuma na mare shi Abban su da yake kwance sai da ya tashi saboda firgita ummi kuwa hannu tasa aka tana cewa aleena zaki janyo mana musifa muna zaman zaman mu lafiya ina ke ina marin maikudi kisa ya zo ya rufe mu to ummi wa ya ce ya dauke ni ni da ba muharramar ba ummi tace to Allah ya kiyaye ke meyasa kika ki tashi da ya bi ta kan ki ai kinga shike nan kin mutu yayi mana asara kuma bamu iya ja da su tunda suna da kudi mukuwa abincin da zamuci ma wani lokacin gagarar mu yakeyi Abban su yayi murmushi kawai yace Allah ya kyauta.

Salamu alaikum mom tayi sallama cikin gidan su aleena ummi ta amsa wa alaikumus salam maraba ummi tace aleena dauko wata taburma ta ce to ummi ta dauko ta burma ta shinfida ta durkusa ta gaisheta mom ta amsa cikin fara a tana yaba nutsuwar aleena sai ga afnan ma ta zo ta ce ina kwana mom ta amsa sai ji sukayi afnan ta ce ina mai kyau dazu na ganshi har ya bani alawa ni kuma na ki karba sai mom tace toh waye kuma mai kyau ummi tana murmushi tace tun ranar da wasu suka tare a wancan gidan ta ganshi ta shigo tana cewa ta ga mai kyau mom ta karasa dariya tace ashfaq ne ko ai mune wadanda muka tare a gidan shine na shigo wajen ki mu gaisa ummi abin ya bata mamaki dama akwai masu kudin da suke rabar talaka tana cikin tunanin nan taji tana cewa suna na Khadija Yara na uku babbar tayi aure tana zaune a Abuja sunan ta Amra sai Ashfaq sai auta ta Amira Umma tace ummi ta ce masha Allah Allah ya raya mana su amin.
Nan suka shiga hira kamar sun sa ba sai mom tace don Allah ko zakiyi min hanyar wacce zata rinka taimakamin da aiki ina biyanta duk karshen wata ko sati sai ummi tayi shuru tana tunani.

To wa ummi zata samo?
Ina labarin doctor ashfaq wani mataki zai dauka akan aleena?
*********************
07038185042

Comment
Comment

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now