page 20

1.3K 80 8
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Daga jarumai writers association

Allah ka bawa mahaifina lafiya kasaka masa da alkhairi kaji kan mahaifiyata ka gafarta mata kasa aljanna makomarta tare da sauran 'yanuwa musulmai muma in tamu ta zo kasa mu cika da imani🙏

Godiya gareku masoyana sakon gaisuwar ku yana zuwa wajena

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpadd jami1020
**************************

P2⃣0⃣

Da sassafe ummi ta tashi bayan ta hada musu kumallo ta hadawa abba ruwan wanka ta kai masa bayan ya fito ta taya shi shiryawa cikin dan kayan sa mai kyau cikin wadanda suka rage masa sai ga abba ya fito yayi kyau sosai kamar ba shi ba sannan ta kawo masa abincin da tayi koko da kosai sai ta dan soya dankalin hausa don kuwa acikin kudin da su ashfaq suka  basu ta dan yi musu siyayyar kayan abinci dai dai na talaka

Bayan ta gama zuba masa abincin ta tashi zata fita yin aikin gidan tunda yanzu aleena bata nan abba ya tsayar da ita yace mata Allah ya saka miki da alkhairi ya ba ki aljanna ina jin dadin yadda kike kula da ni da yara na ba are da gajiyawar ki ba nagode sosai

Ita kuwa ummi duk yayi mata addu'an nan tana jin dadi sosai tana kuma samun kwarin gwiwa don me yafi haka dadi mijinka ya rinka sanya maka albarka yana maka addu'a kuma kullum amin abban su bakomai duk yiwa kai me in ban yi muku ba waye zai yi muku kuma meye amfani na ke nan suwa nake da su masu muhimmanci fiye da ku Allah dai ya baka lafiya abban su yanzu shi ashfaq din kawai zamu jira ya zo sai ku tafi kace kada a gayawa ahmadu kaga da ya zo sai ku tafi tare dukka umm kyale shi kawai kada na katse masa neman sa yana ma kokari wallahi ummin su ina jin dadin yadda yake kulawa da mu bai yar da zumunci ba gaskiya kam ahmadu sai dai muce Allah ya saka masa da alkhairi ya bamu ikon mayar masa da alkhairi amin

Bari naje na karasa aikace aikace na kafin ya zo ku tafin ko eh to ba laifi ai da mutuniyar tana nan da tuni ta gama yi miki gaskiya mu godewa Allah da ya bamu yarinya nutsatstsiya mai hankali da sanin ya kamata duk da karanci shekarunta haka ne kam Allah ya sa musu albarka amin sannan ta fita ta dau tsintsiya ta share gidan har da soro ta wanke ban'daki don ummi kam akwai tsafta sosai tana gamawa ta shiga tayi wanka ta dawo ta shirya tace to habibi gani na dawo na gama don naga yau hira ce a bakin nan naka ko soyayyar ce ta tashi sai duk suka sa dariya
*********

Aleena tana shiga gidan direct kitchen ta wuce duk da ta tarar da an share anyi mopping amman sai da ta kara sharewa  ta dauki dankalin turawa ta fara ferayewa tana cikinyi amira ta shigo kitchen din a guje taje ta rungumi aleena sis aleena ina cikin farin ciki fa tun jiya wallahi abinda nake ta jira ne ya faru dani   wallahi tayi murmushi ta ce to 'kya tsaya ai ko gaisawa muyi ko hahhh tasa dariya ai farin cikin da nake ciki ne na kasa gayawa kowa ko yaya amatullah da amina ban gaya musu ba kuma ma ba ma zan gaya musu ba ni duk haushi fa suke bani wallahi wai duk ajin su duk kyansu su nacewa namiji daya kamar ba 'yanuwa ba mtsss taja tsaki wai su fa nan duk ya ashfaq suke so fa shi kuma ko ta kansu ba ya yi amman sun nace har gwara amina ma naga ta dan hakura tana ja da baya amman ban ya amatullah kamar ma kara zuga ta akeyi mtsss gaban aleena dai sai faduwa yake yin jin wai duk 'yan matan nan son ashfaq sukeyi to k ina ruwanki da har xaki damu ai kuwa dai kam duk a zuci take zancen nan

A fili kuwa sai cewa tayi ke kam in kika fara surutu bakya tsayawa ne duk sai suka kyalkyale da dariya har da aleena ita da ba mai yawan dariya ba sai dai murmushi ni muje ki rakani na gai da mom sai mu dawo mu cigaba da aikin mu to muje sis

Suka hau sama zuwa dakin mom kowacce da sallama a bakin ta mom ko tana zaune kan sallaya tana ta lazimi don in dai ba wani abun ba to bata tashi har sai karfe bakwai kuma bata damuwa da batun breakfast don ta koyawa amira shiga kitchen karge shidda tun amira tana jin haushi har ta zo ta saba mom takan ce mata gwanda ki saba don kuwa gidan wani zaki je karkije kiyi ta sangarta

Mom tana ganin su ta fa'da'da murmushin ta aleena ta tsugunnah ina kwana mom amira kuwa jikin ta taje ta fada ta rungumeta lafiya aleena kema kizo ki rungumeni yadda 'yaruwar ki tayi ta taso cikin jin kunya da kaunar matar a zuciyar ta ta rungumeta yauwa 'yan matan mom sai duk suka sa dariya ya gida aleena ya ummin ku da jikin abban ku alhamdulillah to yayi kyau Allah ya shi muku albarka amin duk suka amsa a tare amira ta mike sis muje muyi mu hada breakfast kar mu makara mom me za muyi duk abinda ya zo muku shi za kuyi ok mom sis ta shi don ita ta matsu su ke'be gulma na cinta

Suna dawowa kitchen aleena ta cigaba da aikin ta ita kuma tace to bari nati sauri na hada stew ko da za aci dankalin to bayan dankalin kuma me zamu hada kuma sis tatsaya tana kallon aleena to sai muyi pancake ko eh to haka ma yayi amman ina ga fa sai kin yiwa ya ashfaq toasted bread din nan don naga ya ji dadin sa naga kima ya ci sosai har da guzirin sa na zuwa office da shi sai tayi banza da ita kamar ba ta ji me ta ce ba

Nan da nan suka gama hada komai suka jera akan dining sis bari naje nayi wanka ko in zo mu sha labari ko kizo muje saman tare no kije kawai bari na gama gyara kitchen din tukun na ko ok to shi ke nan ta yi sauri ta fita nan amatullah ta sauko kasa ta sha kwalliya kamar zata je gidan biki nan ko duk ashfaq akayiwa tunda tasan zasu hadu a akan dining ta leko kitchen din aleena ta gaisheta ganin zata girme ma ta ta amsa a dakile tana hararar alena saboda kwata kwata yarinyar bata yi mata ba ta fiye kyau da yawa mtsss

Alena kuwa ta juyo ta cigaba da aikin ta tana cewa a zuciyarta toni me nayiwa wannan matar ne na lura tun zuwa na gidan nan kamar haushi na take ji sai kace an ce mata ni budurwar wannan mutumin ce toh woo aleena me ya kawo zancen budurwa kuma hhhhhhh😜

Doctor ashfaq kuwa bai farka ba sai wajen karfe bakwai ya tashi da addua a bakin sa yana ya kalli in da ya kwanta a kasa yace to jiya dai ke nan kwanan kasa nayi gado na yayi missing di na ke nan ga duk jikina ciwo da sauri ya je ya fada wanka Allah ya so shi ya sami sallar asuba don duk rintsi sallar asuba bata wuce shi tun yana dan yaro ya saba da hak hatta zaman su a america bai sa ya canza ba gurgeje ya yayi wanka ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kayan farare sunyi mutukar karba sa ba fesa turare ya kai kala nawa ajiki sa ya dauko laptop dinsa ya dan fara aiki a kanta yan tunanin to ko yanzu yarinyar nan ta zo kuwa to dai da alamun ta zo tunda yana jiyo kamshin abinci i want to see this girl kai ashfaq ka kama kan ka fa yace acikjn zuciyar sa hmmm bayan ya gama abinda yakeyi a laptop din sannan ya dubi time ya ga takwas saura minti biyar ai da sauri ya ajiye ya dauki bakin glass yasa a fuskar sa saboda yana so ya karewa yarinyar nan kallo to kuma baya so kowa ya fuskan ci hakan

Ya ga minti biyar din taki tayi ya jja tsaki ya fito ya sauko kasa zuwa dining daidai lokacin kuma aleena ta fito ta gama aikin da takeyi zata koma falo ta jira sai kuwa suka hada ido da shi duk da dai shi da glass a fuskar sa kuma baki ne ba ka iya ganin kwayar idanun sa ta ji a jikin ta cewa sun hada ido ta sunkuyar da kanta kasa turaren sa yayi mata dadi ba kadan ba

Ya wuce kai tsaye zuwa dining table sai abin ya bawa amatullah mamaki don tasa baya saukowa har sai kowa ya fito wani lokacin ma har sai sun fara cin abinci tayi sauri itama ta tashi ta koma kan dining tana wani iyayi tana gaishe shi to itama aleena sai taga bata kyauta ba da bata gaishe shi ba ko ba komai ai ya girmeta kuma yana shirin taimakawa abbanta sai ta dan kalle shi ta ce ina kwana sai yayi kamar be ji me tace ba kamar ma wani wajen ya ke kallo bata san ita yake kallo ba ta kara dagowa tace ina kwana ita kuma amatullah don ta samu shiga wajen sa sai tace ya ashafaq me aikin nan fa tana gaisheka fa sai sannan ya dago ransa a bace ya cire glass yana kallon amatullah yace wacece mai aikin ta yi shuru ganin yanatin fuskar sa ya daka mata tsawa yana kara tambayarta wacece yar aikin
*************

07038185042

Comment
Comment

Don Allah a taya ni sharing pls

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now