page 43

1.1K 74 6
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA

YA ALLAH KA RAYA MANA YARAN MU AKAN TAFARKIN MA'AIKI

DAGA KUNGIYAR AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA KARA DAUKAKA YA HADE KAN MU

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
*******************

P43

Not edited

.........Alhaji ya Kara so cikin falon yana Kara cewa "wacece yarinyar nan?yar g gidan waye?wani yaro ne wannan da ya marar min yaro da ni da nake mahaifina sa ban taba sa hannu na mare shi  ba sai shi?wallahi Sai na dauki mataki akan su"

"Haba Alhaji irin wadannan tambayi haka?ya kamata ka tsaya ayi bincike akai kafin a yanke hukunci,don idan an bibiya mata yuwu Annur ke da laifi acikin wannan abun shi ya janyo fadan ma"momy ta kare maganar ta tare da watsawa Annur kallo,kallon da yake sauke da ka kiyayai kanka Kar ka janyo wata fitina

Annur ko ganin kallon da momy tayi masa,Sai kawai ya fashe da Kuka

Ganin kukan da Annur ya sa ne ya Kara hassala Alhaji,ni bansan wacce irin uwa ce ke ba da bakya hoton bayan danki akan komai,da a asibiti kika haihu cewa zanyi an canza miki yaro shi yasa bakya nuna masa so da kauna haba

Momy kuwa tace"to yanzu Alhaji kawai Sai na rinka bin bayan sa tana aikata 'barna ko abinda bai dace  ba sai na bi bayan sa?  Hakan da nake masa shi ne so da kaunar da nake masa,duk wata uwa ta gari tana so taga ta bawa 'ya'yanta tarbiyya mai kyau da kowa zaiyi alfahari da ita,kasani fa malaman ta farko a duniya ita ce uwa,domin it's ce zata fara ko ya wa yaro yin abu tun tana karami har ya fara girma ya shiga makaranta daganan malamai su karbe ta a makaranta,in ya dawo gida Kuma ta cigaba daga in da ta tsaya idan ya fita waje mutanan unguwa suma suyi na su.in ban da ma lalacewar zumuncin yanzu ai da wani yana iya yiwa yaranka hukunci a waje da tarbiyya tamkar shi ya haifa,amman ban da yanzu da duniya ta lalace.yanzu ka gaya min laifina don Allah?"

Ku dai bi duniya a sannu kasa ka cutar kai in an cuce ka kayi hakuri da sannu Allah zai sama maka.

"Allahu akbar ya ustaziyya momyn Annur"

Momy ba hatta Annur Sai da ya saki murmushi jin abinda Alhaji yace.

Kai Annur my boy,my sweet boy kana son yarinyar nan ko kuwa kawai da ka tsaya da ita ne kawai ka rage zafi?Daddy Ina son ta da gaske kuma da aure nake son ta.

Alhamdulillah ai ke abin farin ciki ya zo,ga abinda kike ta so yaron ki yayi nan ya kiyi Sai yanzu abin ya zo amman kina nan Sai faman huci kike yi,da har kina wani ya je yaga 'yar gidan kawarki,ya dan hararar ta

Ni kam yanzu ku ai Sai dai in samu ku ido kawai,yarinyar da nake fada ma yaje ya ganta tuni ma an bada ita Kuma kwanan nan za mu Sha biki da yardar Allah,Sai dai Kuma ba wai baki nayi maka ba baka ta ba samun yarinya irin Aleena ta,takan zo gidan nan lokaci lokaci Allah ne dai bai ta'ba hada ku ba,da ka ganta da Sai ka so ta.

To min ji ya isa haka kasan yanzun nan in aka cigaba za ta fa'da wa'azi kuma

"Yanzu Ina ne gidan su yarinyar? Ya sunan ta?"

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now