page 21

1.3K 77 6
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka gafartawa mahaifiyata da yan'uwana kasa aljanna makomarsu

Allah ka bawa mahaifina lafiya ka kara mana lafiya da duk wani musulmin da ba shi/ta da lafiya

Gaisuwa gareki hajiya mamn shureim ta munzali Allah ya kara soyayya da zama lafiya

Ina godiya gareku masoyana wadanda na sani da wandanda ban sani ba

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P21

Ashfaq ya kara daka mata tsawa ina tambayarki wacece yar'aikin daidai lokacin ne mom ta sauko kunnan ta suka jiye mata abinda ashfaq yake cewa ta kara so wajen tana cewa son menene ya faru kai da wa kake fada haka aleena tayi mata sannu da zuwa sannan ta sunkuyar da kanta kasa mom ta amsa amman hankalinta na ga ashfaq saboda da yadda ta kalli fuskarsa ta san cewa ran shi a bace yake

Son meya faru ne mom a kullum kina yawan yi mana na siha cewa wulakanta mutum ba shi da kyau ba shi da dadi kwata-kwata ko da kuwa mutum a karkashin ka yake ko ba haka haka ne son ta amsa masa to kiyiwa yarki magana ki ja kunnenta da kyau akan yadda ta wulakanta yarinyar nan ya nuna aleena next time idan ta karayin haka to zan dauki hukunci wallahi sai kawai ya mai da gilashin sa kan fuskar sa ya fara danna waya zuciyar shi a tafashe wai aleena ake cewa yar aiki mtssss ya ja tsakida har sai da ya fito waje

To wai takamaimai me ya faru ne haka da safen nan ke amatullah me ya faru ta komar da kallonta kan amatullah ita kuwa ta na zaune ta daskare a wajen kwakwalwar ta ta shiga aiki to menene don ta cewa wannan yarinyar yar'aiki to ma menene a tsakanin shi da yarinyar nan don ta ce haka shine ya wani harzuka haka to ko son ta yakeyi ne tab tashin hankali ke nan ai haka ma ba za ta taba faruwa ba gani ina ta zaune zaman jiransa sannan wata yarinya ta zo daga sama ta kwacemin shi hmmm lalle za ayi ta shin hankali ke nan

To ko kema bazaki gayamin laifin da kikayi masa bane ai sai na tambayi aleena tun da ita tana wajen ko nan hankalinta ya dawo jikin ta sai ta kalli mom tayi raurau da idon ta ce mom ba komai bane bafa wai don kawai nace wa wannan yarinyar ta nuna aleena da hannu 'yar aiki shike nan ya ashfaq ran ahi ya baci ya fara fada to mom don Allah nayi laifi ne ai naga 'yar aikin ce dai ko ta karshe maganar da tambayar mom

Mom tace gaskiya ba ki kyauta min ba abinda kikayi ba daidai ba ne tun far kon zuwan aleena sai da na ja muku kunne na nuna muku cewa aleena fa tamkar 'ya take a wajena ni ba 'yar aiki na dauke ta ba ta zo ne kawai don ta rinka taimakawa amira wajen girki don dukkan ku a matsayi daya na dauke ku wallahi har ga Allah ina son aleena har cikin zuciya ta saboda daga yau kada ki sake kiranta da wannan sunan tunda ai kinsan sunanta ko eh mom to bazan sake ba ta fada zuciyar ta na mata 'daci da tsanar aleena a ranta

Ita kuwa mom mamaki take to kawai don an gayawa aleena haka shine abinda har ya fusata tashi yake ta wani 'bata rai to ko dai akawai wata akasa ne
Hmmm

Bayan amira ta sauko ta zauna za a gara cin abinci ne mom ta kalli aleena ta ce to ke 'diyata ba zaki zauna ba ne sai ta danyi murmushi ta nuna mata kujerar da take kallon ta ashfaq tace ta zo ta zauna ta zagayo ta zauna duk tana jin ta wata iri tana mamakin kuma me ya fusata wannan mutumin dan an ce mata 'yar aiki to mecece ita in ba 'yar aikin ba ita ba ko ji haushi ba kawai abinda ba ta so shine wulakanci to ashe dai yana da dan kirki da sanin 'kimar mutum sai ta dan saki murmushi duk abinda takeyi idanun sa na kanta yana ganin tayi murmushi sai shima murmushin ya su'buce masa ya ji dadi har cikin ransa da ya ga ta saki ranta ba ta bata ranta ba

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now