page 11

1.3K 77 6
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka bawa mahaifi na lafiya da duk marasa lafiya mu kuma da muke da lafiya Allah ya kara mana ita

Allah ka raya mana yaran mu ka tsare mana su ka kuma shirya mana su

Mai dambu Allah ya kara daukaka ya ba da lafiya

Mallakar Jamila(Maman amir)

Wattpad jami1020
*****************
  P11

Ashfaq dai barci ya gagare shi don da ya rufe idon zai tilastawa kansa barci sai ya ga lokacin da ta mare tas sai ya bude ido yayi shuru sai ya ke hango fararen idanuwan ta masu kyau da haske cikin nasa idanun sannan da yadda ya karanci idanun na ta she is not a weak person duk da ya ganta karamar yarinya ce sai wata zuciyar ta ce mishi karama a ina hmmm har ta san ta dake ka a wajen nan mtssww ya kara Jan tsaki sai ya kara tuno da wani kamshi da take fitarwa mai sanyi kasa kasa ga kuma dadi sai ya lumshe ido can dai yace to ina ruwa na ma a haka dai yana ta tunanin nan har yayi barcin da yake ta so tun dazu ya dauke shi

Mom ma dai ana ta bagaran Tana tunanin me ya faru da ashfaq dinta ne in har ba mistake tayi ba taga lokacin da suka shigo yana tafiya a dan duke kuma yana dan kare gabansa to me ya faru Allah ka shirya mini yarana ka kare su daga aikata zina nan ta kira dad din su ashfaq tana cewa dad ya kamata ka dawo haka nan fa muna missing dinka sosai yace nima haka but don't worry am coming back soon nan tsofaffin suka cigaba da hirar su ta soyayya nace bari dai na kyale wadannan na koma wajen su aleena ita ma Na dau rahoto
**********

Aleena ma a bangaren ta da ta zo kwanciya kafin tayi barci haka tai ta tunani kala kala har ta fado abinda ya gudana tsakanin su da Wannan saurayin dan iska kawai sau biyu ke nan yana ta bata Wannan karon ma har da kusan rungumeta haushi ya kara cika ta ita tunda take ba wani namijin da ya taba kai hannu jikin ta sai dan iskan nan kai ita fa abinda tayi masa ma bai ishe ta bata fa to ke aleena kika  sani ko ya mutu saboda abinda kikayi masa wata zuciyar ta rada ma ta nan gaban ta ya fadi in ma bai mutu ba to yanzu haka kinyi masa lahani na shiga uku ai sai ta mike zaune in kuwa haka ne to ya zatayi ke nan can kuma tace ai shi ya janyo kawai tayi kwanciyarta bayan tayi addua sai barci

Can cikin barcin ta tayi mafarki ga Wannan saurayi ya zo wajen ta yana kuka yana cewa ta taimaka masa ita ce kawai  zata iya tai maka masa a duk fadin duniyar nan akan abinda yake ji tace to me ka ke so na taimaka ma da shi zai yi magana ke nan sai taji ana cewa aleena aleena ki tashi haka nan mana har an kira assalatu yau baki tashin ba nan ta mike a firgice tace ummi na tashi tayi adduar tashi daga barci sannan taje ta dauro alwala da ta dawo ta tashi afnan ma taje tayi alwala sannan ta tada sallah bayan ta idar ta zauna Tana karatu that is her habit idan tayi sallah asuba ba ta komawa barci za tayi ta karatun kur'ani har gari ya waye tana duba agogo taga karfe  shidda na safe ta mayar da kur'ani ta tashi taje ta gaida iyayenta to yanzu zaki shiga gidan ko eh ummi to ki kiyaye kinji Allah ya ba da sa a ya kuma tsare amin muje na raka ki kofar gida tace to bari  na dauko hijabi na ummi ta dauko hijabin suka fito ta rakata har ta shiga cikin gidan su ashfaq sannan ta koma guda

Aleena ta na shiga direct taje ta danna bell mom tayi Sauri ta bude don dama ita take ta zaman jira ta zo oyoyo diyata mom ta rungume ta ta dan yi murmushi ta zame kasa ina kwana mom lafiya lau kina lafiya aleena lafiya lau ya jikin Abban da sauki mom to Allah ya kara sauki amin

Yanzu mom dame zan fara muje kitchen din na nuna miki komai kafin amira ta sauko kuyi tare ko to mom ba laifi suka shiga cikin kitchen din komai tas tas saboda tun asuba mai aikin take zuwa ta wanke komai ta gyara tayi shara da mopping mom ta nun nuna mata komai har in da kayan abincin yake sannan tace yau abinda za kuyi kawai pepper soup na kayan ciki sai a soya Irish da kwai shi sai ki dan gasa wa ashfaq bread don yana son shi sosai bari naje na taso amira to mom nagode tayi murmushi kawai ta fita zuwa dakin amira

Ita kuma kawai aleena taga da ta tsaya jiran amira duk bata lokacin kawai sai ta fara dora pepper soup din ta wanke kayan cikin sosai da ruwan zafi sannan ta dora akan wuta yana fara zafi ta sauke ta kara dora wa a wuta sannan ta zuba kayan miya da kayan kamshi ta sa tafarnuwa sosai da ginger danya bayan tayi greating dinta saboda karni nan da nan gida ya kama kamshi ta dauko Irish zata fara feraye shi ke nan sai ga amira da sallama ta ta rugo aguje ta kamkame ta oyoyo my sister am sorry na barki ke kadai kina ta faman aleena tayi murmushi tace ba komai da kinyi zaman ki ma duk zan karasa hmmmm taja numfashi sister aleena me kika dora ne duk gidan kamshi ya keyi pepper soup ne na kayan ciki lallai yau zamu ci dadi kawo na cigaba da feraye Irish din sai ki soya eggs din OK mutum nawa ne zasu ci take tambayar amira bayan ta dauko kiret din kwana mutum 7 OK ta fasa rabin kiret din tasa maggi da albasa sai tafarnuwa kadan ta dora fraying pan ta dinka soyawa Tana saw a afaranti sai da tayi sau bakwai sannan ta kashe gas din nan suka fara soya dankalin turawan sunayi amira Tana tayi mata jira Tana bata labarin yayanta Dan kaida muskili ba Wanda take tsayawa yayi jira mai tsawo da shi zai abokinsa amir zai mom it a ma wani lokacin kuma Kinsan me sister in kinga yadda take yiwa mom shagwaba zai kace ba shi na matsu yayi aure Amman har yau tace ai bai ga wacce tayi masa kiji fa don Allah to ai amira aure lokaci ne idan lokaci yayi zai yi ai tace hmmm da alama kema ba ki son yin magana fa sister tun dazu ina tayi miki hira sai dai kiyi murmushi kawai ta fada cikin shagwaba to naji me kike so na narinka cewa kema kirinka magana to naji har suka gama soya dankalin aleena tana cikin rafin dankalin a faranti amira tace bari na leka ko ya aahfaq din ya sakko sai gata ta dawo aguje dan milkin fa ya sakko yanzu nan da 8 am zai hau kan dining ai mungama ko eh mom tace a gasa masa bread OK

Wai mom me ake dafawa ne yau gidan duk kamshi wallahi kamshin na yau ya banbanta dana kullum tayi murmushi tace son ai ni har na matsu na ci abincin nan aleena ce takeyin girkin oh har ta zo ne yayar afnan ko tace yes hope dai tana a tsafta mom sai ma kaganta tukun na Wannan zaka tantance hmmm kawai tace

Can kuma bayan ta gama gasa bread din tasa a plate ta rufe sannan ta kalli amira done well done sis bari na gayawa mom an kammala

Mom the food is ready to he ki kirawo wadannan masu son jikin su sauko suyi break son let's go ya tashi kawai ya hau dining ya zauna yana ta danna waya aleena fara kawo abincin to mom fara kawo cooler na farfesun ta ajiye ta koma ta dauko sauran da Saudi ya dago da kansa ina yasan kamshin turaren nan domin da zata wuce har sai da hijabin ta ya taba kujerar da yake kai don kusa da shi ta ajiye cooler ina na San kamshin nan mtsss
*****************

07038185042

Comment
Comment



SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now