page 27

1.2K 78 8
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Zauren jarumai writers association

Muna farin cikin da zuwan wannan wata naka mai alfarma, Allah ya kara daukaka darajar ka ya rasulillah(s.a.w)

Allah ka jikan mahaifiya ta kayi mata gafara kasa tana cikin ni'imar ka ya Allah.

Ina godiya gareku masoya na masu bibiya ta nagode Allah ya kara kauna.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P27

Not edited

Ni ima ganin ya amir mu kyale su tukun sai sun gama wahalar da kansu tukun na, kuma da alama shi ya ashfaq din ya fi kamuwa da son ta.don abinda na lura ita har yanzu ba ta gane menene so ba, kuma shi ya kamata ya fito yace yana son ta kamar yadda kai ma ka gaji da nukunukun ka ka fito ka furta mini ta karashe maganar da yi masa gwalo.

Au ni kike yiwa gwalo ko to akwai ranar kin dillanci ranar da ko kallo na ma bazaki iya yi ba balle har kiyi mini gwalo, ya kashe mata ido.ita bata fahimci me yake nufi ba sai tace"au yanzu kana addu'ar ranar da za ta zo har na kasa kallon ka ya amir"(idon ta ya ciko da kwallah) ke lil sis ki fahimci abinda nake nufi idan kinje zaki kwanta barci ki ta maimaita hirar nan da mukayi da ke may be ki fahimci abinda nake nufi, ina sonki lil sis wallahi bansan irin son da nake miki ba tun kima yarinya, kullum cikin fargaba nake ka da wani yazu ya rigani furtawa, ke kuma ayi rashin sa'a kice kina son sa hmmm ai da na shiga uku da sai da na tuttulawa kai na fetur na kyarta ashana wa kai na, amira ta kwashe da dariya ganin yadda yayi maganar.

To naji ya amir ni ma ai kasan ina... ina....ina.... ta kasa karasawa ta rufe fuskar ta kawai hmmm sai fa kin karasa yanzu ko kuma naki cin abincin kuma wallahi yunwa nake ji idan ban ci abinci ba alhakin yana kanki ya kwabe fuska.don Allah ka ci, ai na gaya miki bazan ci ba sai kin fadamin don nima naji irin abinda masoya ke ji idan dayan yace wa dayan i love you ya wani lumshe ido, kaiii to naji close your eye, i can't because ina so ki kalle ni cikin ido ki fada mini.

Ya amir ina so ka ci abincin amman ina ga an zo gabar da dolle na kyale ka haka, Allah ba zan iya kallon kwayar idon ka ba na fada ka dan bani lokaci don Allah, ya yi wani killer murmushi to naji nayi miki uzuri saboda ke farin shiga ce amman next time in na tambaya zaki gayamin ba tare da gardama ba ko?tayi knocking kan a alamar eh!

Good girl now zo ki zauna mu ci abincin mu gama hirar mu ko "ok" ta ce.nan suka cigaba da hirar su har lokacin sallah yayi suka tashi zasu je suyi sallah.

Na su dade da tashi ba aleena ta farka daga barcin, ta rinka bude idom ta a hankali tana ya mutse fuska saboda yadda kanta yayi mata nauyi, ta rinka kallon falo ko ina ta ga ba kowa, ta mike zaune dauke da salati a bakin ta, bayan ta zauna daidai ne fa sannan abubuwan da suka faro sukayi ta zuwan mata akwakwalwa, ta dafe kanta ta runtse idon ta wai me wannan bawan Allah yake nufi da ni me kalaman sa suke nufi agareni ne?ta dafe kan ta.

Ashfaq yayi sauri ya mike tsaye ya dafe kirjinsa, amir ya kalle shi ya ya dai me ya faru ne man ka tashi a firgice haka? Ta tashi ya sake maimaitawa da cewa ta tashi fa kawai yayi hanyar waje.

Amir ya bishi da kallon mamaki abin har ya kai ga haka tab wannan wacce irin soyayyace ne haka farat daya? tashin da tayi wai shine har ya ji ajikin sa ya wani tafi da sauri to sai na bika na ga abinda zakuyi ko kuma na fara labewa yadda ba za ku ganni ba amman sai na kirawo sahiba ta tukun na mugani a tare ya kyal..kyale.. da dariya ya nufi dakin amira ya kwankwasa ta bude kofar, tohh wooo ya amir kai ne da kanka a bakin kofa ta me yasa ba za kirani a waya ba? yanzu da a wani yanayi nake kuma fa ta cuno baki kinga ni yanzu gulma na kawo miki ki fito muje kasa lovers zasu hadu lets go and see ya janyo hannun ta ta kwace hannun ta galla masa harara, ya kalle ta yace bakomai duk a cikin so ne lil sis, sai kuma suka fashe da dariya dukkan su sukayi hanyar falon.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now