page42

1.3K 72 12
                                    

SHA'AWA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA.

SAKON GAISUWA TA GA DUKKA FANS DINA NIMA INA YIN KU BA IYAKA,MASU KIRA DA MASU TEXT😘

DAGA KUNGIYAR AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA KARA DAUKAKA.

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020

******************

Ban manta da ku ba Rashida bello,Maman Aslam(IYAMI),my besty, Aishatummulkhairi,Hafsat,Maman tee,maman sayyid ,Mom,comments dinku na girgizani❤️😘keep it up

P42


..........kuuuuuu kake ji karar burki,wadanda ke kusa da kan titin Sai da suka tsorata,balle Aleena da ke cikin motar,Sai da gaba daya ta kidime hankalin ta yayi masifar tashi  ganin yadda Ashfaq ke kokarin hallaka su.

Ta rinka cewa innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,tare da runtse idanun ta don ganin take kamar kashe su zai yi da motar kawai saboda bakin kishi.

Ashfaq ko da har lokacin zuciyar sa na masa zafi ganin da yayi wa Aleena da wani har tana ikirarin matar sa ce,da ya tuno Sai kawai ya bugi sitiyarin motar.

Da ya bugi sitiyarin motar Sai Aleena ta Kara tsorata amman bata bar fad'in innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba,sunyi wajen minti uku a haka har Shima ya fara bin abinda take cewa a 
H

ar dai zuciyar sa ta Dan yi sanyi(don fa'dar Allah ce,cewa idan awani abu ya dameka na masifa kace innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.to idan ka lazimci fa'dar haka Sai zuciyar ka tayi sanyi nutsuwa ta zo maka Allah zai SAUKAKA maka).

Jin shuru shuru Ashfaq bai tada motar ba sun tafi kuma bai ce mata komai ba sai kawai ta fashe da Kuka,da Sauri ya tsaya tana kallon ta tana ta faman Kuka,ya bata wajen minti uku yaga bata dai na kukan ba,iya kuma da gayya take kukan da yadda ta lurar da shi a Yan zaman da suka yi tare ba ya son ya ga mace tana Kuka,to shi yasa it's kuma ta cigaba da kukan.

Malama kiyi min shuru taki tayi shuru Sai ma kara murya da tayi,Sai ya daka mata tsawa yana cewa ba zakiyi min shurun ba,maimakon tayi shurun inaaaa ai Sai ta Kara murya da tafi waccen har da wayyo Allah Mom ki zo ki taimaka ni ya Ashfaq zai halakar dani tun kafin ki Kai ni dakin mijina 😭😭

Shi Ashfaq Sai abin ma ya fara bashi dariya,Sai ya dan kama murmushi yana cigaba da kallon ta har da gyara zaman sa ya fuskan ce ta,to kiyi min shurun ya isa haka muryar sa a hankali yake fa'dar hakan,hmmm ka fara saukowa ke nan ai wallahi baka isa bari ka gani

Mom mom,umma ba kuna Ina ku zo ku a ga zanin ni baba son na mutu yanzu Sai na ga yarana da jikokina da tattaba kunne har da uhum uhum,yanayi tana daga hannayen ta

Ashfaq bai son lokacin da dariya ta kufce mishi ba sai 'kyal'kyal'kyal ya keyi,har da Dan sunkuyawa .Sai tayi murmushi a zuciyar ta ganin ya sakko daga fushin da yayi har Yana dariya.sai da ya gama yi mai isar sa sannan ya ce lallai ma yarinyar nan wai har da wani cewa Sai Kinga yaranki da jikokina ki har dawani tattaba kunne da mea kika ce? Uhum uhum ta bashi amsa.

Hmmm yaran yanzu baku da kunya ko, a gaba na kike fa'dar haka,"to ya Ashfaq in ban fa'da a gaban ka ba a gaban wa zan fa'da?kai kadai nake iya yin sirri  ko nagaya mika maganar da ta dame ni ka kuma bani Shawara,ka ga ke nan ba kunya a tsakanin mu,ko na Sami Wanda zan aura Sai ka amince kafin ayi auren"

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now