page 14

1.2K 105 6
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka gafartawa mahaifiyata da yanuwana da sauran musulmi baki daya,Allah kabawa mahaifina lafiya da nisan kwana

Ina godiya sosai gareku masoyana a duk in da kuke

Mallakar Jamila(Maman amir)

Wattpad jami1020
****************

P14

Suna tafiya ashfaq na ta zumudin ya zo gida don ya ci girki mai dadi ya ga kuma abinda take kwadayin gani wato fuskar aleena yana ta murmushi yana kuma mamakin kansa me yake faruwa da shi ne ohoo koma dai menene yana jin dadin yanayin nan da yake ciki wai kai baka da hankali ne kai kadai Kayi ta faman doka murmushi you are mad gaskiya ehh naji din ka fadi duk abinda zaka ce hmmm kai kana ta zumudin nan idan kuma itace Wannan yarinyar fa ya zakayi ke nan kuuuuuu ya taka birki bakin ka ya sari dayan kashi ana maganar masu hankali kana shigo mana da ta marsa hankali

Wai kasan yadda na tsani yarinyar nan kuwa da Allah zai hada mu da ita ko hmmm ban ma San kalar wulakancin da zanyi mata na wallahi hmmm kai dai kasani ba girin girin ba..kai kasan irin wadannan maganganin naku ashfaq ya tare shi son kada ma ya karasa fada kyalkayal kyal kyallll..... Amir ya rinka dariya yana cewa to meye na katseni kabari na karasa abinda zance mana

Mtsss akan me zan bari ka karasa wai kuwa kasan aleena kuwa da ganin ta wallahi yarinya ce nutsatstsiya ga hankali da sanin ya kamata amir ya saki baki yana kallon sa to kai har yaushe kasanta da har ka ke sharhi akanta mtsss bata baki na ma nakeyi da nake baka labarin nan idan mun isa ina so ka rakani cikin gidan su zan gaishe da mahaifinta a zabure amir ya tashi kai ashfaq tun yanzu gaskiya Kayi saurin zuwa ka bari Ku gama fahimtar juna mana tukun nan kai amman lallai kuwa amir din nan to mom ce tace naje na duba mahaifin su aleena saboda na shi da lafiya bansamu na shiga shine nace yanzu muje tare amman har ka fassarani Allah ya shirye ka ehh na ji din kai me ba Kayi wa mutane bayani yadda zasu fahimci maganar ka kayi ta Abu kamar munafuki ashfaq dai yayi masa shurun son in bai yi shurun nan ba to fa amir ba zai yi shuru ba

Ganin haka sai ya zame yayi baya ya Dan kwanta ya lumshe idon sa wallahi ina sonki sosai kema Allah yasa kina sona in ma bakya so na to zan koya miki yadda zaki so ni amira na matsu na ganki ohhh Allah ashfaq dai yace in tayi wari ma ji.

Ummi suna zaune da abba a falon su shi kuma Abba yana kishingide to ni dai Allah yasa ka da aleena tayi musu shirme fa wallahi haba ummin su ke Kinsan halin yarinyar ki to meye abun damuwa in girki ne ta ita iri iri kina kuma koya mata to fargabar me zaki yi yari yarki bata da raahin kunya to kinga ai sai ki godewa Allah in sha Allahu babu abinda Zai faru sai alkhairi to Allah yasa nan kuma suka ji ana ta sallama daga waje wato kofar gida to suwaye kuma Allah yasa bakin alheri ne

Nan ta dauki hijabin ta ta leka kofar gida sai taci karo da su ashfaq suna ganin ta suka sunkuya duk kan su suna gaishe ta tace ahh daga nan Ku shigo ciki mana to ummin mu inji ashfaq ji munafuki har wani ummuin mu yake cewa wai har yaushe ya fara soyayya bansani ba Kayi kwafa

Dukkan su sun zaune a gaban Abba Kansu a sunkuye kamar wasu surukai sun zo gaisuwa  Abban ina wuni lafiya lau mai kyau sai suka sa dariya ya aikin na ka da sauki Allah ya kara sauki yayi afuwa kuma amin mai kyau dama zuwa mukayi mu gaisheka ahh yayi kyau masha Allah to shi abokin maka menene sunan sa amir ne suna na Abba Allah ya kara afuwa amin nan ashfaq ya ajiye musu yan Dari bibbiyu na dubu goma ahaka ma amir sannan suka gashi kai kai kai kuzo Ku dauki kudin Ku gaisuwar ma ta Isar wallahi haba Abba baka dauke mu yaranka ba ke nan ba haka ba ne ba amman to shi ke nan Allah ya yi albarka ya kara budi amin to mu samu tafi sai na shigo anjima da daddare zan shigo kuyi hira da kawata tunda barci take yi yanzu da yake yaga afnan akwance Tana barci to Allah ya nuna mana sannan suka fita suka shiga  gidan kowa yana zumudin ya ga fuskar tashi shi amir saboda soyayya shi kuma ashfaq dai na kasa gane me yasa yake so ya ga fuskar aleena masu karatu ko kunsan me yasa???

Suna shiga suka tarar da mom da yan matanta akan dining har sun gama cin abinci aleena kuwa kanta akasa amman tana jin muryarsu sai da gaban ta ya fadi tana jin haka ta shiga karantawa hasbunallahu wa ni'imal wakil a hankali sai ta ji muryar mom tana cewa mu dai munkasa hakurin jiran Ku mun ci namu don haba daya kamshin girkin aleena ya hana mu sakat dole sai da muka cika cikin mu duk suka sa dariya ban da aleena da ashfaq sai murmushi sukeyi aleena zo ki duba musu kinji yar albarka ni dai zan wuce sama na dan huta kunji ko suka ce to tace to Allah yayi muku albarka(yana da kyau iyaye surinka shiwa yaranau albarka bawau sai sunyi mana wani abun ba sannan ace Allah yayi albarka ba pls mu kiyaye)  sannanmom ta haura sama aleena kuma ta koma kitchen debo muau abincin da ya ke cikin cooler ko da ta dawo amir da amira suna ta hira ashfaq ya kalli su Amina yace su tashi su basu  waje zasu ci abinci shi da abokin sa duk suka tashi har sauran har sun haye sai amira a baya amir yayi Saudi ya kwala mata kira akan ta zo Zai tambaye ta wani abu ta dawo ta zauna aleena tana zuba musu abinci ashfaq yana ta danna waya amman fa na dole don kuwa ya matsu ya daga ido ya kalleta amman girman kai ya hana aleena tana zuba abincin tana cewa azuciyarta to shi Wannan ba Zai dago da kan sa ba da ganin sa dai yana da girman kai yaya aleena ina wuni inji amir kunya ta isheta au Dama bata gaishe su bane lah don Allah kuyi hakuri na sha afane wallahi ina wunin Ku ta fada cikin sanyin muryarta lafiya lay ya gajiyan girki don takanas aka ce  Na zo Na ci girkin ki don kin ita girki sosai sai ta danyi murmushi tace nagode

Shi kuwa ashfaq yana ta kokawa da zuciyar sa sallah ka daga kai ka kalle ta to menene in ka kalle ta ga amir nan sai kallonta yakeyi kuma suna ta zuba hira Dan iska kawai ya ja tsaki a fili ya ja plate din gaban shi ya kama cin abinci sa don dama a matse yake ya ci abinci duk da bai San ko menene ba kamshin duk ya ci ka cikin sa sai ci yakeyi cikin yanga sai ta ji muryar ta tana cewa bari naje nayi wanke wanke zan ta fi gida lokacin islmiyya ya kusa ta wuce kitchen

Wai za ta tafi wallahi ba ki Isa ki tafi aa sai naga fuskar ki kawai ya  tashi ya bi bayan ta

Tana Isa zata fara wanke wanke ke nan ta zi muryarsa cikin zanyi ya ce aleenaaa sai gaban ta ya ba da dam dam dam shi ma kuma gaban na shi dama yana ta dukan uku uku ta juyo a hankali ba tare da ta amsa ba nan idan su ya sarke da na juna
******************
07038185042
Comment
Comment

Pls vote and follow me on my wattpad

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now