page 29

1.1K 69 17
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

Zauren jarumai writers association


Allah ka bawa mahaifina lafiya kasa kaffara ne, ka jikan mahaifiyata da 'yanuwana da suka rasu, ka haskaka kabarin su ka gafarta musu.amin

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P29

Not edited

Ko da suka ta so aguje suna rige rigen wanda zai fara rungumar mutumin nan mai cikar kamala fuskar sa dauke da murmushi ya bude hannayen sa as usual  don yadda yake musu ke nan idan yayi tafiya ya dawo, sai ya bude hannayensa ya rungume kowa, ko in ce wanda ya riga karasowa.

Ashfaq da amir a tare suka zo suka rungeme shi suna cewa " dad barka da zuwa,  sannu da zuwa, dad ba wani labarin zuwanka" yace "to 'yan samari a barni na ji dumin 'ya ta ko duk kun zo kun tare mata waje fa kun gani sai turo baki take tana hararar ku fa"

Dariya suka sa ashfaq yace to wa ya hana ta ta zo ita ma.dad ya re su yace zo nan kin ji 'yar gidan dad rabu da su wadannan katti da har yanzu basu san sun girma ba ke ma zo naji dumin ki ko.  ta fada jikin sa tana cewa dad you are highly well come, but nayi fushi baka gaya mana zaka ta so yau ba ai gashi ba awani shirya maka komai ba fa na ci, ba bu komai zan ci duk abinda kuke da shi, kuma yanzun ma am ok.

Ina mom din ku take? Tana sama, to ku matsa ku gani naje na ga masoyiya ta don na kwana biyu bangan ta duk ina jina kamar wanda ya shekara bai ganta ba, kyalkyalkyal su ka sa dariya gaskiya abba sai ka tsaya munyi hira tukun na ka bamu labri sannan ka je wajen mom.

Tab kuji min yara ku don baku san yadda so yake ba ko? shiyasa nake so kuyi aure amman kun ki har yanzu ba wani labari sai kara girma kuke yi ina ga duk sadaka zanyi da ku mu huta kawai.

To ka kwantar da hankalin ka dad amir dai ya sami matar aure, dad cikin farin ciki yace da gaske kai zo zo matso kusa dani, oya tell me, is this true? sai ya dan sunkuyar da kan sa kasa alamun kunya, la la la la lallai yaro na ya fara girma yau ni ake jin kunya gaskiya ko wacce zan mata kyauta gagaruma.. "Wata ce fa a can layin 'yar fulani gidan su yana bakin titi" inji ashfaq

Wallahi dad karya yake yi sharri zai yi mini, kama ma fa san ko wacece fa, don ya san yanzu ashfaq yana iya hada masa gadar zare idan ya fada kuwa mai tsamo shi sai Allah, kuma shima fa dad ya ga wacce yake so fa anan take, kai kai ni zaka yiwa sharri? Eh nima ai sharrin kayi mini da kace wai wata ce 'yar fulani bayan ka santa ya harare shi

Dad dai sai fara'a yake yi, yana son yaran sa sosai, baya nuna banbanci tsakanin su da amir, duk daya ya dauke su, yana kuma sakar musu fuska sosai, shi ya sa ko magana zasuyi ko shawara kafin su sami mom sai sun sami dad tukun na.

Mom dai ta leko ta bakin window don ganin su waye a tsakar gidan suke ta hira haka, ai ko wa zata hango in ba habibin ta ba, tayi wani sassanyar a jiyar zuciya hadi da murmushi ta saki labulan tare da saukowa kasa.

A can ko sun sa shi a gaba wannan ya ce kaza wannan yace kaza, shi ashfaq ya dahe wata yar fulani ce amir yake so idan ba haka ba kuma to ya fadi sunan yarinyar, shi kuma bawan Allah amir ya kasa fada, wata irin sabuwar kunyar dad ya ji da tunda yake bai taba jin irin ta ba shi isa ya kasa fadar sunan amira.

Ita kuma a bangaren amira da ta ga ashfaq ya dage da gaske akwai wata 'yar fillo da amir yake so, kawai sai ta dauka ko gaske ne, ta kalle shi ta balla mishi harara, tace  "oh dama akwai wata 'yar fillo da kake so ke nan ko" ta kalli dad,  dad ta ho mu shiga daga ciki ka huta.

Wallahi wallahi karya yakeyi,  ni bansan wata 'yar fillo ba ashfaq ka gaya mata gaskiya,  duk ya wani rude.ashfaq yayi masa gwalo,  dad kuwa dariya yayi don ya fahimci kwanan zancen.zai yi magana ke nan mom ta kara so in da suke tana cewa "kai ku kyale min miji yaje ya huta daga zuwan shi kun cika shi da surutu ba abinci ba ruwan sha ba bashi abin zama ya hutu haba!

Thank God da kika zo zaki kwace ni wajen yaran nan, daga dawowa ta sai complain hahhhh yasa dariya,.mom ta kalle shi ta harare shi tace kai ma zakayi bayani ne da kwakwkwarar hujja.toh na shiga 'daka, ku kyale ni nima tawa ta same ni, ku bari na gama ba da hakuri anjima zamu zauna hira, yaja hannun matar sa, zo mu tafi mom ki kyale su ni kishirwa ma nake ji,sukayi cikin gida.

Amir ya kalli amira,  suna hada ido ta galla masa hararah sannan ta wuce cikin gida." Soyayya dadi tafi zuma zaki"ashfaq ya cigaba da yin wakar sa.hmmm ni dai kayi wa haka ko?amir yana fada yana nuna kirjin sa, shi dai ya cigaba da wakar sa yana kashewa masa ido. to yayi kyau dani kake zancen, indai ni ne sai na rama kai ka sani ai, sai naje na hada maka bom wajen aleena,  cak ashfaq ya tsaya da wakar da yakeyi, yes sai na hada maka bom wajen aleena, sai na kawo mata saurayi zankadede sun fara soyayya tare, ya gwalo ido me kake cewa amir? "ka bari don Allah bana son irin wannan wasan, don wannan ba wasa bane ba kwata kwata, me ya kawo aleena cikin maganar nan har da wani zancen zaka hada ta da saurayi saboda Allah"

Au haba ni ka manta wutar da ka kunna min ne wajen amira? to naji kayi hakuri zanje na kashe ta da kai na, amman don Allah ka fitar da aleena acikin maganar mu da wani saurayi da kace zaka kawo mata don nasan zaka iya aikatawa don Allah.to muje ciki ka ce mata kai da gangan kake wasa kawai kake yiwa dad.naji mu tafi suka wuce ciki yana addu'ar Allah yasa amira tayi saurin saukowa don ya santa in ta hau bata saukowa da wuri, shi kuwa yana tsoron tuggun amir.

Mom suna shiga cikin daki ta fusge hannun ta tace ni nayi fushi tun da baka sanar dani yau zaka ta so ba sai ganin ka kawai mukayi,  ya zo ta baya ya rungume ta am sorry wallahi na gaji da zaman can ne kuma duk hankali na ya kasa kwanciya ku kawai na ke son na gani especially my habibaty ya nuna ta da 'dan ya tsansa, sai suka sa dariya suka rungume juna, nan nace hmmm bari na fita na bar musu dakin su ina ta mamaki ashe tsofaffi ma suna soyayya haka ikon Allah.
***************

Acikin wani tangame falo ne da ya sha kayan alatu kala kala masu tsananin tsada na ga wani hadaddan saurayi a zaune yayi crossing legs din shi, da kaga fatar sa kasan wannan guy din dan hutu ne don fatarsa har wani sheki takeyi kamar wata mace nasan kuma baya rasa nasaba da irin mayukan da yake shafawa masu tsada order kasar waje.

Sai ga wata yarinya da ganin irin yanayin kayan jikin ta kasan 'yar aikin gidan ce, tana tahowa da saurin ta dauke da plate na lemo da ruwa sai wani abu a kanannade cikin tissue dana dan leka sai naga ashe meat pie ne a cikin tissue din,  duk a razana take kar tayi laifi ya ci mata mutunci , to garin saurin ne kuma tsautsayi ya sa ruwwn gorar ya fadi akan kafar sa, yan sa ihu kadan saboda ya dan ji zafi, tashin da zai yi kuwa ya wanke ta da mari tass ni kai na sai da na tsorata.

Daga baya ne naji muryar wata mata tana cewa yanzu kai annur ba zaka dai na wannan zafin zuciyar ta ka ba, me yasa kake haka ne babu kyau wulakanta mutum a rayuwa do min ba ka san me gaba zata haifar ba.haba momy bakya ganin yadda yarinyar nan ta zo ta kwalamin goran nan a kafa ta wallahi da zafi fa momy ya fada a shagwaban ce, momy zata kara magana ke nan, no gaskiya maman nur ki kyale shi ai abinda yayi shine daidai, ita bata da hankali ne da zata kwalawa yaro na ruwa a kafa hakan da yayi mata yayi daidai.Alhaji ka dai na daura wa annur gindifa ya rinka abinda ya ga dama mai kyau da mara kyau wallahi babu kyau kada wata rana ayi danasani fa, la'ilaha illallahu yanzu yaron naki guda daya tal da Allah ya bamu shi kike yiwa baki saboda Allah , ni fa ba baki nayi masa ba gaskiya nake gaya masa wallahi.

Annur tashi kayi ficewar ka kaje wani wajen ka huta kaji kar ka damu da abinda momy ka take maka ina tare da kai kaji ko, ok dady i love you so much wallahi, love you son, akwai kudi hannun ka ko na kara maka no dady ina da isashhen kudi a wajena kar ka damu bari naje gidan cin abinci kawai bye ya zari key ya fita daga gidan.momy tace Allah ya kyauta ya shirya mana kai ya hada ka da mace ta gari da zata shiryar min da kai.
**********

To fa hmmmm
*********

07038185042

Comment

Comment

Pls share vote and follow me on my wattpad.

Love you fans

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now