page 24

1.2K 79 5
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Daga jarumai writers association

Allah ka jikan mahaifiyata da dan'uwana ka yafe musu kurakuran su kasa aljanna ce makomar su

Ya Allah ka bawa mahaifina lafiya ka saukaka masa da duk wadanda ba su da lafiya

Ina miko sakon gaisuwa gareku masoya soyayya ko sha'awa a duk in da kuke musamman my besty khaery, Amina muhammad jarma, hafsaty, zee, maman sayyid, maman tee, hauwa, mamilosh, Aishaummulkhairi, meenartbz da dai sauran wadanda ban lissafo su ba ba kuma wai na manta da ku ba ne love you all.

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

Not edited

P24

Ashfaq yana barin gidan su aleena ummi da guda tai sauri ta rungeme abban su ta  saki wani irin kukan jin dadi 'yau ga abban su an samu wanda ya tsaya masa ya kai shi asibiti cikin mutunci da tausayawa ya kuma siyamasa  magunguna abinda auke ta mafarkin faruwar sa ga shi yau ya faru'to ai ba kuka zakiyi ba ummin su  addu'a zaki da ubangiji ya saukaka mana wannan abu sai dai Allah ya kawo lafiya kuma, ai na kasa boye farin cikin ne shiyasa wani lokacin idan farin ciki yayiwa mutum yawa to kawai sai dai ya fashe da kukan jin dadi

Fatan mu dai Allah ya baka lafiya abban su amin amin zainab to yanzu sai goben za a karbo daya sakamakon eh haka yace to masha Allah ni wallahi har Allah Allah nake ma aleena ta dawo don in ga irin farin cikin da za tayi shima abba yasa dariya ni dai yanzu da nayi sallah zan dan kwanta barci don na gaji sosai gaskiya kam ya kamata abban su ta fita ta zuba masa ruwa a buta don yin alwala.

Su aleena suna cikin kitchen suna hada lunch amatullah ta shigo cikin kitchen tana wani ya tsina ta bude frige ta dauko lemo da cup maimakin ta fita sai ta tsaya ta kalli su aleena ta ja mugun tsaki tace Allah ya sauwake haka fa yaran talakawa suke da sun je ko in ce da suga dan saurayi mai kyau da kudi shike nan sai a fara neman shigar da kai don a aure su to ni da na fada da babbar murya"ya ashfaq dai ya fi karfin wata ta dai na ma wahalar da kanta wajen shishshige masa wallahi ya ashfaq sai amatullah" sannan ta kara hararar aleena tayi ficewar ta daga kichen din tana karkada jiki.

Amira ta kalli aleena ta ga ta sunkuyar da kanta ta kira sunan ta sis aleena sai ta dan dago da kanta idanun ta cike da kwallah don Allah kiyi hakuri da abinda ya amatullah tayi miki ita dai a rayuwar ta ba ta so ta ga wata mace ta ra'bi ya ashfaq saboda mugun son da take yi masaba na wasa bane to ganin ya ashfaq ba ya kulata idan yana kula wata sai tayi zargin ko akwai wani abu a tsakanin su ne mom tayi masa fadan har ta gaji har cewa tayi za ta yi musu aure daga nan ya fara son amatullah din to shine fa shi kuma ya ashfaq yayi rantsuwar idan har tayi musu aure to ana daurawa yana yi mata saki uku kinji abinda ya dakatar da mom ke nan ta kira ya amatullah tayi mata fada da nasiha cewa ta hakura da ya ashfaq ita kuma taki yarda shine kawai ta zuba musu ido ba ta cewa komai.

Hmm lallai kuwa ti me ya sa ne ni kam mai kudi babu abinda yake so a rayuwa irin ya wulakanta talaka ya kaskantar dashi domin kawai shi ba shi da kudi suna mantawa da maikudi da talaka duk matsayin su daya a wajen Allah amman su masu kudi ba sa ganewa yau in kai ne dashi gobe wani ke da shi 'gashi ni don ba ni da shi na zo ina aiki shi yasa ta samu damar wulakanta ni sai hawaye ran ta yana yi mata zafi wallahi sis amira na tsani wulakanci bana son wulakanci wallahi wai har ni take cewa ina tusa kai na wajen ya ashfaq mutumin da ko maganar arziki ba ta hada mu da shi da tasan ma yadda akayi muka fara haduwa da ta zuba ruwa a kasa ta sha
'

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now