page 19

1.3K 89 5
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka haskaka musulunci ka kara daukaka shi

Allah ka jikan mahaifiyata ka haskaka kabarin ta kasa aljanna ce makomarta ka gafarta mata kurakuren ta tare da yan uwa musulmai da suka rasa rayukan su🙏

Allah ka biya mana bukatun mu na alkhairi kasa mu fikarfin zuciyar mu🙏

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

Ina mai bada hakuri na jina kwana biyu bana posting sakamakon rashin lafiyar da nayi amman yanzu alhamdulillah za arinka jina kamar ko da yaushe in sha Allah.
Ina godiya da wadannan da suka rinka kirana da ma su yimin text kai har da wadanda ma su kai min addua ba tare da sani na ba, ina godiya gareku my fans

P1⃣9⃣

  Haba ya amir da na gama makaranta fa ka ce ina laifin sai na shiga university na kai ko da 3 level ne sannan sai ayi auren a fada cikin shagwaba tana kara kasa da kanta tana wasa da 'yan yatsunta hmmm kafin lokacin nan na mutu ke nan ta zaro ido tana masa kallon saboda me yace eh mana in ba so kike ki kasheni ba ya za ayi ki ce sai na kara jiran wasu shekarun wai har shekara biyar nan gaba ban da shekarun da na dauka ina jiranki

Am sorry ni ba haka nake nufi ba sai ya mai da fuskar sa ya hade rai alamun ba wasa a maganar da zata fito daga bakin sa amira kalle ni nan kinsan dai na kai munzalin da za'a ce na ajiye mace a gidana ko Allah ya sani wallahi ina son yin aure anan kusa ko don saboda kaucewa fa'dawa halaka kuma sonki yasa na kasa yin auren nan don ina ta jira ki kai munzalin da zan furta miki soyayyar da nake yi miki kullum da fargaba nake kwana nake tashi saboda kada a wayi gari lokacin da zan furta miki wani ya rigani ko kuma ki ce ke bakya so na na sha nuna miki alamomi da yawa cewani fa son ki nakeyi amman sai ki mai da abin irin ke fa baki gane ba alhalin nasan kin fahimci abinda nake nufi ya fada ya dan hararar ta tasa dariya

To yanzu dai duk mu bar  wannan tashin tashin din ga dare yana yi idan kin bani dama dad yana dawowa zan ga yawa abban mu ya zo ya nema min auren ki plss ya hade hannayen sa yana kallon idanun ta tace to Allah ya tabbatar da alkhairi na baka dama ya amir

Yauwa lil sis nagode sosai kin ji yanzu shiga gida dare yayi sai na zo goben ko i love you tayi murmushi ta ce to au ba zaki ce i love you too ba kai ya amir kawai sai ta falfala a guje yasa dariya yana zamu hadu gobe ne sai kin bani amsa ita ko ko sauraran sa bata karayi ba har ta shige cikin falon ya shafa kan sa hmmm har yanzu lil sis baki ga ma girma ba in ba haka ba ina ke ina gudu ya shiga motar sa ya tafi maigadi yna daga mkshi hannu yana cewa Allah ya kareka ranka shi dade amin ya Allah kawai ya ciro kudi da yawa ya danka wa maigadin ya ce yau ina cikin farin ciki kai ma ga rabon ka Allah ya kara dawwamar da kai cikin farin ciki ranaka ya dade yana karbar kudin yana kara masa addu'a daga nan ya rufe gate din gidan.

Aleena ko sai da ta tsaya a cikin soro ta tattara nutsuwar ta sannan ta shiga ciki gidan da sallama ta iske su har sun shige falo ta karasa falon ta ce ummi zan jena kwanta to yayi ba damuwa ko ba bu komai ummi to Allah ya shi albarka ya tashe mu lafiya amin abba sai da safe

Har ta kai kofa ta ji muryar abban na ta yana cewa aleena na Allah dai ya karbi addu'ar ki ya kawo mana masu taimaka mana gobe ashfaq yace zai zo muje asibiti ya duba ni da kyau a can fuskar sa dauke da jin dadi sai itama ta tsinci kan ta tana mai jin dadin ta ce an gode masa Abba Allah ya kai mu goben Allah kuma ya kara maka lafiya abba amin aleena je ki kwanta saboda kada ki makara  gobe ko to sannan ta fita sai da tayi alwala sannan ta shive dakin su ta rufe musu kofa ta kwanta tayi addu'ar barci

To nan kuma barcin ya ce bai san zancen ba sai abinda ya faru dazu tsakanin ta da ashfaq ya shiga dawo mata tana mmakin yanayin da yarinka yi mata magana da shi wai har yana bata hakuri sai kace wani saurayin ta

To ko ma dai menene sai fa ta rama abinda yayi mata ba zai ci 'bagas ba wallahi tab tayi kwafa sai wani sashin na zuciyarta ya ke tunasar da ita cewa fa ga fa irin taimakon da zai yiwa abban su fa gobe zai zo ya kai shi asibiti da kansa sannan ya duba shi haba aleena ai ko don  saboda wannan ai kya rangwan ta masa mana ki kyale shi tun da ya nemi sulhuya kuma baki hakuri ko ehhto kuma fa hakane  amman dai sai ta rama sau daya shi ke nan sai ta nemi ya fiyarsa ta kuma yi masa godiyan abinda zai yi wa abban su final duk ta gama zancen zucin da takeyi sannan a rufe idanun ta kawai sai taji kamar numfashin sa kusa da fuskar ta ai a firgice ta bude ido tana sauke numfashi da ta ga babu kowa sai tayi ajiyar zuciya kawai ta kara kwanciyasai ta shiga karanta suratul muluk a zuciyar ta a haka har barci barawo ya sace ta ni ko nace oh su aleena ba zaki hakura haka nan ba na ga komai ya wuce😛

Ashfaq yana shiga daki direct toilet ya nufa ya watsa ruwa yayi brush ya daura alwala sannan ya fito dakin nan ya dauki sanyi AC ga wani kamshi mai dadi da yake tashi  ya fada kan katafaren gadon sa ya saki ajiyar zuciya shi kan hi ya ji dadin moment din can ya ce aleena aleena yana daukar matashi ya rungume a jikin sa

Yace she is beautiful and young da ganinta tana da kunya amman fa akwai tsiwa idan an tabota sannan yadda ya fahimce ta ajiya lswai tana da tsoro sosai sai ya tuno lokacin da ya ke matsowa wajenta tana matsawa baya tana zaro ido tana cewa wai menene haka kawai sai ya kyalkyale da dariya har da dukan filo hajiya aleena ikon Allah

I like this girl she can fight for her right hahhhhh kai ashfaq meye kakeyi haka ne me yake damunka ne kana ta wani faman tunanin yarinyar nan kana wani jin dadi yaji wani sashe na zuciyar shi na gaya mishi haka sai yaji wani bangaren yace to ai yarinyar ta cancanci a yabe ta na don yarinyar tana da kamun kai  da wata ce yadda yayi kissing dinta a kitchen da ko uffan ba za ta ce ba sai dai ma ta bashi dama ya cigaba da yin abinda ya ke yi mata din

Gaskiya she is different ya lashi lips din sa don shi har yanzu yana jin 'dan'danon
Bakin ta a bakin sa hmmmm to wai meye yame faruwa da nine mtsss ya ja tsaki anyway in sha Allah zan nemi na zama abokin ta murinka mutunci kawai kafin lokacin da zanyi aure auu yau kai kai kake cewa zakayi aure har ka sami matar kenan wani bangare na zuciyar sa yake fada masa

Ina fa na sami mata ni har yanzu banga wacce tayi mini ba balle n aure ta ina son mace mai addini mai kamun kai mai kunya da kyau wacce bata da tsoro ta zama na tana da dan tsiwa kadan amman ba na rashin kunya ba wacce zata jira har sai ni na furta mata da kai na ina son ta tukun na sannan zan yi aure hmmm to ga aleena sai ya tashi a firgice ya ce what a fili ya fada da dan karfi

What is wrong with you ashfaq mtsss sai kawai ya tashi ya shinfida sallaya ya tada sallah ko da ya idar nan ya zauna yana cigaba da addu'o'i har barci ya sace  shi
***********

Tun da asubah aleena ta tashi tayi sallah sannan tayi wanka ta zauna tana karatun kur'ani kafin shidda tayi ta fita zuwa wajen aikin ta wato gidan su ashfaq shidda tanayi agogonta ya buga ta tashi ta fito tayiwa iyayenta sallama tayiwa abbanta fatan alkhairi sannan ta wuce gidan su ashfaq
********
07038185042

Comment
Comment

Pls a tayani sharing in kun karanta kuyi sharing pls

Nagode sosai fans din soyayya ko sha'awa whatsapp group ina jin gaisuwar ku sosai musamman my besty khaery and amina muhammad da mummy shukura

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now