page 48

1.2K 78 16
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA

ALLAH YA KARA MANA LAFIYA DA ZAMA LAFIYA

AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION I LOVE YOU ALL.

INA TAYA HAFSAT GARKUWA MURNA NA SAMUN KA RUWA DA TAYI ALLAH YA RAYA AKAN SUNNAH YA BADA LAFIYAR SHAYARWA

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
*******************

🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗🍗💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
**ina taya daukacin Al'ummar musulmai barka da sallah, especially my fans😘Allah ya maimaita mana**
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

P48

......Umma ta Kara na na ta sunan Aleena Kuma? Eh umma ai tunda na sa wasu yara suka shigo da kaya cikin gidan nace a fara kirawo min ita mu fara magana in ya so ita tayi min jagaba zuwa cikin gidan to Kuma Sai hira ta dauke Mana hankali har muka da'de haka,Yana Kara sunkuyar da Kai wai shi irin kunyar nan ta surukai.

Aleena dai bala'in mamakine ya daure ta da haryanzu ta kasa cewa komai Sai kallon shi da take yi da jin irin yadda yake son ya Murda zancen wajen umman ta a matsayin ai sun Dade tare ma ke nan,lallai wannan mutumin Dan rainin hankali ne.

Umma tace"to masha Allah hakan ai yayi kyau,ke Kuma kin tsaya Mana haka 'kerere aka,maimakon tuntuni ki shigo dashi kika bar shi a can waje,ni da na dauka ma doctor ne ya zo shi ya aiko yaran ya kiraki tunda yau baya son shigowa ashe ba shi ba ne Annur ne"ta Dan sa dariya kadan.

"Umma ni zan je na kwanta barci ina so na tashi da wuri gobe in Allah ya Kai mu,tun da zamu je bikin binta"

Za ta Wuce yayi Saurin cewa "to madam sai da safe Sai na zo goben
In Sha Allah"

Umma dai ba tace komai ba har Aleena ta wuce dakin ta,sannan ta dawo da kallon ta ga Annur din ,tana kokarin yin magana riga ta da cewa

"To umma ni zan wuce dare Yana yi Sai,Allah ya kawo ni goben ma zan shigo mu Kara gaisawa da yawa"

"To to to Allah ya nuna Mana goben da rai da lafiya,ka gaishe da momin ta ka"

*****
Annur na isa gida direct wajen momi ya wuce zuwa dakin ta,Yana zuwa ya rungumeta Yana doka murmushi

Momi tace "ya akayi shalelen Alhaji (ta kan kirashi da wannan sunan idan ta ga Yana cikin annashuwa)naga Sai fara'a kake ba ni labari na Sha"

"Momi yau Ina cikin farin ciki sosai don na kusa samun abinda nake ta nema Wanda na wahala akan shi,to abin ma Sai ya Kuma zuwar mun da sauki Kuma"

"Uhummm Ina jin ka,ka gayamin direct Sai kwana kwana kake min"

"Kiyi hakuri momi da ban abi umarnin ki ba da farko wallahi bansan haka yarinyar ta ke Sai da muka ha'du da ita, da na je gidan su yau Kuma na tabbatar da cewa ita ce wacce kika zaba min naki yarda,momi kin tuno wacce wani ya mare ni akan ta da na zo in gaya muku?"
Momi ta gya'da kan ta alamar eh.

"Yawwa to ba kowa bace wannan yarinyar Sai Aleena yar gidan kawarki ta unguwar tudun yola,wallahi momi da gaske Ina son yarinyar nan,da na bi ta maganar ki tuntuni da yanzu na San an da'de da gama Shan bikin mu da ita,ko momi"
Ya karshe maganar Yana 'yar dariya

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now