page 36

1.2K 82 43
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION

ALLAH KA BAWA MAHAIFINA LAFIYA KA SAUKAKA MASA

ALLAH KA JIKAN MAHAIFIYA TA KAYI MATA RAHAMA DA YAN'UWANA KAYI GAFARA GARESU

MALLAKAR JAMILA (Maman amir)

WATTPAD jami1020

P36

....Dad yana gama cin abincin sa ya tashi yace wa Mom"bari naje na kira Ashfaq muje gidan can ayi komai a gama kawai" .."to bangane me kake nufi ba fa? " Mom ta tambaye shi.idan muka dawo zaki ji,but first let me get to my son,ya hau sama wajen Ashfaq.

Ashfaq ko Yana baron falon zuwa yayi kawai ya kwanta a kan gadon sa ya wani bararraje  akai ya rufe idon sa Yana karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil,bai dai na karantawa ba har Sai da yaji zuciyar sa ta yi masa sanyi sannan ya bari,Sai Kuma Aleena ta fa'do masa a zuciyar sa,Yana tunanin abinda ya faru a kitchen Yana Kara jin wani sanyi da wani irin yanayi Yana ta so masa,Kuma shi da ma ga irin yanayin sa don Yana da karfin sha'awa shi ya sa ma yake Shan magani da yawan azumi saboda gujewa Sharrin shaidan.

To amman abin Yana Dan kwana biyu bai ta yar masa ba,saboda magani da yake Sha da azumi da take kan yi(don baya mantawa lokacin da Yana daukar karatu a wajen malamin su can America da yayi magana akan cewa idan mutum Yana da karfin sha'awa to ya yawaita yin azumi Allah zai kare shi,Kuma wannan fadar Manzon Allah ce sallallahu alaihi wa sallam) Yana cikin tunanin nan ya ji marar sa ta kulle don Yana daga kwance Sai da ya tashi ya zaune tare da rike marar sa,yayi tsaki yace.." Kai Allah ya sauwake shi yasa ba a son ka kallo abinda ya ke haramun ne a gareka ko ka kusanci abin,ni me ma ya Kai ni tsayawa kuwa da ita da har Kuma na tsaya Ina karewa kirjin ta kallo,ai gashi nan na jawowa Kai na,ita ko tana can lafiyar ta kalau mtssss.." ya mike ya dauko maganin sa ya Sha sannan ya kwanta rub da ciki a kasa kan lallausan carpet din sa ya rufe idon sa kamar me barci don ya samu ciwon ya lafa masa.(Ina Kira ga samari da 'yan mata don Allah ku rinka kiyayewa wajen yadda zakuyi mu'amala a tsakanin ku, duk wani kama hannu da wani hugging duk al'ada ce yahudawa,Kuma daga Sai kuga Kuma an Fara tunanin ya za ayi ayi romancing juna,Sai Kuma a tafi mai gaba 'daya.Allah ya shirya mana 'yanuwa musulmai.)

Bai da'de  da kwanciyar ba Dad ya shigo cikin 'dakin,ya same shi kwance rubda ciki ga magani kusa da shi.ya 'dauki maganin ya duba maganin Sai ya rumtse idanuwan sa,yace a zuciyar sa "ya akayi har mai sakaci yaro na yana cikin irin wannan yanayi amman bansani oh Allah help me and my son,I think abinda zanyi 'din shine abu mafi alkhairi garemu in Sha Allah". Ashfaq da bai San ma Dad ya shigo ba sai dai kawai ya ji ajikin sa kamar akwai wani kusa da shi,Sai ya 'dan bu'de idon sa kadan Sai ganin Dad yayi kusa da shi ga Kuma maganin sa a hannun sa nan Kuma da alama ya karanta,to amma meyasa ya rumtse idanuwan sa, yace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,yanzu me zancewa Dad me zai dauke ni?Kai wannan ma abin kunya ne ma wallahi su Dad su san ga irin yanayin na"

"Ashfaq are you alright now?" Dad ya tambaye shi.sai kawai ya 'gya'da kanshi because he can't say anything woo saboda wata azabar kunya da ta kama shi,"tun yaushe ka Fara Shan wannan maganin?" Na da'de Ina Sha Dad,am sorry... shiiii ! don't say that since you're ok shike nan, tashi ka rakani muje naga mahaifin yarinyar nan na duba jikin sa,ok Dad.

Suka sauko kasa  tare da yiwa Mom sallama,suka nufi fita.sai ga mota ta kunno Kai ciki, Ashfaq yasa tsaki yace Dad ga maganannan nan ya zo,Dad dai bai ce komai ba sai murmushi da yayi.

Amir Yana yin parking ya fito Yana gaisar da Dad yana wani sussunkuyar Kai kasa.Dad yace" to yau Kuma ni ake jin kunya? yaushe na Zama sirikin ka?". 'kyale shi Dad munafunci ne kawai ba komai ba,"malam babu ruwanka da ni Dad kayi mishi magana" Dad yace "to ku dai ba zaku daina wannan abun 'yan yara ba?ku baku San kun girma ba?ko da yake baku sani ba sai kunyi aure sannan zaku San kun girma,saboda haka ku shirya nan da wata biyar zan aurar da ku dukkan ku" Amir yayi tsalle tare dan sa ihu wuuuuu! Thank you Dad, ya wani rungume Dad can Kuma Sai ya sake shi Yana 'dan sosa 'keyar sa tare da nuna jin kunyar sa.

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now