page 7

1.5K 85 4
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka haskaka kabarin mahaifiya ta Allah kasa mu cika da imani idan ta mu ta zo

Godiya ta gareku mai dambu Allah ya biya da duk fans din SOYAYYA ko SHA'AWA group

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
*****************
P7

Ashfaq dai abin ya bashi mamaki me yasa zuciyarsa take ta bugawa da sauri da sauri haka ya kurawa aleena ido da kanta ke sunkuye ita bata masan Allah yayi halitta a wajen ba a hankali yake kara sowa cikin falon cikin sanda kamar baya so yarinyar dake zaune a wajen ta ganshi yana duba Inda wayar take can ya hango ta kusa da yarinyar saura kadan ta zauna mishi akan wayar ya zaro ido yace ke tana dago da fuskarta shi kuma yana juyawa sakamakon taba shin da mom tayi tare da cewa ya akayi son ya danyi tsaki yace nothing mom I just want pick my phone yana wani ya tsina fuska ita kuma aleena ganin ba da ita ake ba sai ta sake sunkuyar da kanta kasa tana murxa hannunta mom tace OK let me get it to you ko ta Shafa kan sa OK mom sai hate sama kawai

Mom ta kara so falon tana cewa sorry aleena na barki kina jirana ko tayi murmushi tace ba komai mom ta zauna tace ummin ki ta gaya miki yadda mukayi ko eh to dafatan zaki daukeni a matsayin uwa kinji ko tunda na ganki Allah ya samin kunar Ku a cikin raina aleena ki daukeni kamar mahaifiyarki kuma ba wani aiki za kirinkayi min ba kawai girki ne sai kuma Dan abinda ba a rasa ba shi ma don sabida ashfaq ne baya son cin abincin masu aiki sai dai amira ta rinka girka masa to kinga sai Ku rinka yimasa tare da amira tana raya ki shi ma daddy ku next month zai dawo in sha Allah to mom Allah ya dawo da shi lafiya amin bari na kira amira Ku gaisa don Ku saba ko ta dauki waya yayi dialing number amira ki sauko yanzu kasa ina jiran ki OK mom tace

Ta sauko ta zo ta zauna ajikin mom ke ta shi ni bana son San jikin nan naki haba yarinya sai kace mage amira yayi dariya to mom in ban kwanta wajenki ba wajen wa zan kwanata mom tace to Ga yar uwa nan na samo miki sunan ta aleena makociyar mu ce kinji treat her with respect don jinta nakeyi kamar ni na haife ta kinji my girl in sha Allah mom nan taje kusa da aleena ta zauna I am amira ta mika mata hannu am aleena itama ta mika Mara hannu sukayi shaking hope zaki dauke ni kamar sister din ki in sha Allah sai suka rungume juna mom tace ni ma azo a bani hug din mana suka ta so suna murmushi suka rugumeta har cikin ranta mom taji dadi tace to Allah ya shi muku albarka amin mom bari na wuce to zanje na shirya lokacin Islamiyya yayi to sai kin dawo ko kema amira kwanan nan sai zan saki a islamiyyar nan dai gwanda a samu ilimin muhammadiyan ba boko ba kawai.
************

Bayan aleena ta koma gida tayi wanka tayi sallah sannan taci abinci ta dauko gogeggen hijib dinta do aleena akwai tsabta duk da su talakawa ne Amman komai nasu tsaf ba ta yarda ta sa kaya har said ta goge su sannan tasa turaren ta mai sanyi kamshi ba zaka tabajin kamshin ba har sai in ka matso kusa da ita gab sannan zaka ji sassanyan kamshin da takeyi bayan ta gama tace ummi baki tashi afnan din ba mu wuce lokaci fa yayi kyaleta kawai kiyi wuce warki bata Dade da kwantawa ba fa Allah ummi ke kike daure mata gindi tana yin fashi a Islamiyya duk karatufa yana wuce ta sai dai nayi ta wahalar yi mata kari a gida tadan turo bakin ta kadan yar gidan Abba za fa ki makara in kika biye ta su ki wuce kinji Allah ya shi albarka ya ba da ilmi mai amfani amin Abba nagode kaima Allah ya baka lafiya ummi tace amin ta fita zuwa Islamiyya tana jin wani farin ciki a zuciyar ta na idan wata ya kare aka bata albashinta sai aje a siyawa mahaifinta magungunan sa

A daya bangaren ma ashfaq ya fito zai je unguwa yana tafe yana tunanin yarinyar nan da tayi masa wulakancin nan bai aune ba yaji ya shiga cikin wani rami da ke cike da ruwa da ya zama kamar kawata facal facal sai yaji kamar ihu a kusa da shi ya duba ta mirror din shi sai ya ba ya wata yarinya sanye da hijab Amman duk hijabin ya baci da kwatamin nan yace subhanallahi na bata mata jiki bari name na bata hakuri yayi parking gefe ya dauko robar faro gida biyu da niyyar ya bata hakuri ya kuma bata ruwan ta wanke in da ya bata ta ita kuma a lokacin kawai aleena ta sunkuyar da kanta tana ta kallon hijabinta da ya sha guga amman yanzu duk ya ba ci da kwatami sai hawaye share share ya fara zuba sai ji tayi ana cewa baiwar Allah kiyi hakuri don Allah bansani ba wallahi Ga ruwa ki dauraye hijab din ki tace ba komai ta dago zata karbi ruwan kawai suka hada ido suka tsaya kallon kallo ita tana kallon shi kamar tasan fuskar to ina tasan fuskar nan shi ma ya tsira mata ido ai kawai sai yayi jifa da robar faron

Da ma kece mahaukaciyar nan da ta mareni amman har na zo nake baki hakuri ohoo my God am fool wallahi na dade ina nemanki don na rama abinda kikayi min ban ganki ba sai a sannan ta gane in da tasan fuskar sa ta kalle shi kallon raini ta ja tsaki mtsssss ta kara Jan wani mtsss Tana turo baki sai yanzu na gane da mahaukaci nake magana ma Ashe ba cikakken hankali ne da kai ba ke ni kike gayawa haka an gaya maka din sai kawai ya koma mota ya dauko wani cup ya dawo yana zuwa ya sun kuya ya debo kwatamin nan kawai ya watsa mata ya kara debowa ya watsa mata yana cewa zaki Ga rashin hankali aleena ta rinka hawaye na tana karewa da hijab din ta da zai watsa mata sai ta kare da hijab din ta yana gama yace shashasha kawai mahaukaciya ya yar da cup din ya juya zai koma mortar sa da sauri kawai itama ta dauko cup din ta debo kwatamin tace kaiii da babbar murya ya jiyo facalya ji saukar wani wari a fuskar sa ya tsaya yana goge idonsa yaji saukar wani a ajikin sa sai amai shaaaa ba ta samu da aman da yake yi ba ta kara debowa ta kara watsama sa Tana cewa ka ba Dan iska ba baka San darajar mace ba sai da yayi mass cups biyar sannan ta tsaya Tana huci ta kwada masa cup din

Ya dago ya kalli jikin sa yaga yadda farin kayan sa haba daya sun rine da kwatami sai ya yiyo kanta a guje yana huci aleena dai da taga yadda take hucin nan idan ya rike ta na karamin illa zai mata ba kuma ya taba jikin ta a ba za ai sai ta kwasa aguje ya rufa mata baya Tana guda yana bin ta hahhhhh
**********

07038185042

Comment
Comment

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now