page 22

1.2K 72 8
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Daga jarumai writers association

Allah ka haskaka kabarin mahaifiyata ka bawa mahaifina lafiya

Allah ka bawa yara na lafiya da duk marasa lafiya

Allah  ka kawo zaman lafiya a kasar nan ka kawo mana karshen abin nan

Mallakar jamila(maman amir)

Wattpad jami1020
************************

P22

Ita dai ko kula shi ba tayi ta matso ya bar cikin kitchen din ta kara yin tsaki da sauri ya kalle ta ke meyasa bakya jin magana ne wallahi tsaki yana daya daga cikin abinda na tsana a duniyar nan na tsani ayimin tsaki shi yasa ni ma banayi kuma na gaya miki ya kamata ki kiyaye ki kuma san abubuwan da nake so da bana so in kika sake yimin kuwa you will receive your punishment wai tasan abinda ya ke so da wanda ba ya so to ni ina ruwa na kawai sai ta sake yin tsakin 'dal ta ji ya make bakin ta da yatsun sa guda biyu

Da sauri ta rike bakin ta don har ga Allah ta ji zafin abin nan ni ka 'dalli baki na ko akan me to me nayi maka ai ba dole bane nasan abinda kake so da wanda baka so meye hadi na da kai sai ga kwalla tab a idanun ta yan ganin haka ya ce am sorry ke ce ba kya jin magana ai kuma sanin abubuwan da na lissafo miki ya zame miki dole saboda gaba to me zai faru a gaba din dana bar aiki a nan ai shike nan ko

Gaban sa ya fadi ai wallahi in sha Allah kin zo ke nan ba wani barin aiki da zaki yi to me za kayi mata da har zaka rike ta ba zata bar aiki a gidan ku basai kuma ya kasa samun amsar da zuciyarsa take  tambayar sa ya 'dago ya kalle ta am sorry ba zan sake ba ya wani langwabar da kansa ya marairai ce idanuwan sa kamar wani wanda yake cikin shaukin so ta harare shi kawai to ka fita ka ba ni waje gashi na gama ko no dan karamin guda biyu wadannan sunyi mini kadan don na ji dadin sa sosai fa ke bari na gaya miki gaskiya ni fa ina da ci idan naji abincin yayi mini dadi fa to kinga da alama ke kin iya girki kinga kin haye a wannan don yanzu 'yan matan yanzu basu fiye mai da hankali su koyi girki ba kafin suyi aure ko da yake bari nayi shuru ke fa yarinya ce da har nake miki zancen aure don nasan ba ganewa zakiyi ba

Aleena ko mamakin yadda yake ta zuba take yi saboda amira ta ce mata bashi da yawan magana sai in yana tare da mom ko abokin sa amir amman ji yadda yake ta faman yi mata surutu haka rututu tayi kwafa kawai a ranta tace nasan maganin ka wallahi duk ka zo ka ishe ni da surutu na gama yi maka abinda kake so ka ce sai na kara maka wani wai wannan ba zai ishe ka ba kawai tayi 'kwafa

Me ya faru na ji kinyi 'kwafa n dai ce kiyi hakuri ko ai shi ke nan ya wuce na san ki da kullatar mutum  ba ta dai ce mi shi komai ba tana ta tunanin me za tayi masa ta kalli kayan sa ta ga farare ne sai tayi murmushi kawai shi kuwa a tunanin sa ko ta hakura ne sai ya kara wani washe baki sai  'debo mai da yawa cikin wata 'yar bowl ta dawo in da take da nufin tsayawa shi kuwa dama yana kusa da ita ne jingine da drawer din kitchen din sai tayi kamar santsi ya kwashe ta kawai ta juye man nan a jikin sa sai ta danyi baya tana cewa subhanalillahi kamar ba da ganga  tayi ba tace masa sorry ya ashfaq kaje ka canza kayan ka am sorry

Shi kuwa mutuwar tsaye yayi don a rayuwar sa baya son wani abu ya taba jikin sa ko dana don yana da mugun 'kyankyami a rayuwar sa ya kalleta ya kalli jikin sa ya kara kollon ta ita kuma dai dai lokcin ta dan dariya don btayi tunanin zai 'dago ba lokacin karaf  suka hada ido sai tayi sauri ta gumtse dariyar ta ta nan ya gane lallai ta na sane tayi masa  haka ke nan bai ce da ita komai ba ya juya ya fara tafiya sai ji kake karar abu ya fadi tum a kasa ta jiyo da sauri sai ta ga ashfaq a kasa ai kuwa me zatayi in ba dariya kyal..kyal...kyal ta rinka dariya har da rike ciki kawai sai yayi kwafa ya kada kan sa ya mike da kyar ya dawo baya man da hannuwan sa kawai ya sai ta fuskar ta ya mulka mata akai zata fasa ihu ta tuno su mom suna nan wajen dinning bai ce mata komai ba ya  fita daga kitchen din  a naji din  ai dai gashi ka fi ka bar min kitchen din ba don Allah ba haba mutum sai surutu wai kuma ace bashi da magana ta kara sa dariya ta kunna famfo ta wanke fuskar ta amman bai fita ba saboda bata sa sabulu ba kuma bata so ta sa omo a fuskar ta

Mom ko mamaki ta ke me ya ashfaq ya keyi haka a kitchen din har ya dauki lokaci bai fito ba tana wannan tunanin kawai ta gan shi ya fito ta kalli kayan sa ta ga duk mai ne a jiki ta ganshi ya dan rike bayan sa in da ya dan bugu ta tashi da sauri son me ya sameka haka ne garin yaya haka ya faru babu komai mom no gayamin gaskiya dai to shi kam me zai ce mata ne zai ce aleena ce a watsa masa mai da gangan ko ko yaya na dauko man ne shine ya subuce daga hannu na ya zube min ajiki na yana fada yana inda inda don ahi bai iya karya ba  don da yayi mom taje gane wa mom tayi shuru can tace to kaje ka can za kaya ko kasan a na ta jirank abban su aleena ko ok mom ya fada da sauri ya hau sama  mom ta koma can kan kujera ta zauna tana tunanin ya akayi hakan ta same shi bari zan tambayi aleena ai zata gayamin gaskiya

Yana shiga daki ya wuce bandakin sa da ke ta tashin kamshi kai baka ce bandaki bane ya cire kayan sa ya sake yin wani wanka ya fito ya kara shirya wa cikin wasu fararen kayan again riga da wando duk fari ya fesa turare ya fito don hankalin sa yanzu yana can wajen abban su aleena do  yasan suna nan suna jiran sa zai fara tunanin aleena da abinda tayi masa ya ce not now Allah ya shirye ta ya sauko kasa wajen mom ni zan wuce mom to abincin fa na koshi to ai baka karbi bread din ba ba zan ci ya fada ransa a dan bace kadan to ka dan jira ni son sai ta kwalla wa akeena kira da ke kitchen tana goge goge ta fita ki kawowa yayan ki bread din zai fita office ta ce to mom ta dawo dauke da cooler da kuma wayar sa da ya manta ta a can tace gashi mom, mom ta kalli fuskar ta taga gaba daya mai ne a fuskar ta ta suk da da alama an goge amman bai fita ba tace to ke kuma me yafaru da fuskar ta ki naga mai sgi ma kuma naga mai a jikin sada sauri aleena ta dago ta kalle shi shi ma sai aka ci sa'a ita din yake kallo ta sunkuyar da kanta kasa ta ce uhh hmm mom ina ina cikin aiki ne na manta na sa na goge fuska ta da hannu na mom ta ce wannan ba gaskiya ba ne sai kuma tayi wani tunani tace to shi ke nan ba shi cooler ta kara so wajensa ta mika masa ya dauke kan sa t ce ya ashfaq gashi am sorry ta fada yadda mom ba za ta ji ba idanun ta ya kawo kwalla ya kalle ta kawai ya finciki cooler da wayar sa yayi gaba yau ko addua ma bai tsaya mom tayi masa ba ita kuwa mom ta ji abinda aleena tace masa to me ya faru tsakanin su kawai sai abin ya bata dariya tace to ke kam bazaki je ki karya ba ne kin bawa wasu abinci ke kin hana kan ki  tace to mom  duk abin nan da akeyi amatullah tana kan dining tana iya jiyo komai don duk hankalinta ya na wajen hmmm idan na fuskan ta na kuma gane akwai abinda ke faruwa a tsakanin wadannan mtss# yarinyar nan fa kar tayi min shigar sauri fa amira kuwa sam hankalin ta bya wajen tana ta faman chart da amir

Yana fita daga falon ya shiga motar sa ya zauna memakon ya tada motar kawai sai ya kwantar da kujerar baya yakwanta ya rufe idanun sa yayi shuru yana ta tunanin duk abinda ya faru a tsakanin su da aleena har ya kawo lokacin da ta narke masa idanu tana ce masa sorry sai kawai ya yi murmushi ya ce hmmm yarinyar nan na fuskance ta bata barin ta kwana hahhhh ya dauko cooler ya bude ya dauko guda daya ya sa a bakin sa ya lumshe idanun sa ya hadiyae ya kara wani a fili yace kai wallahi ta iya girki fa mijin ta ya huta kam  sai da yaci wajen guda uku sannan ya mayar da cooler ya rufe ya tada motar maigadi ya bude masa ya fita daga gidan sai yayi parking a waje ya fito ya tsaya a kofar gidan su aleena
*********

07038185042

Comment
Comment

Pls share and follow me on my wattpad

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now