page 40

1.2K 73 21
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA.

SAKON GAISUWA TA GA DUKKA FANS DINA NIMA INA YIN KU BA IYAKA,MASU KIRA DA MASU TEXT😘

DAGA KUNGIYAR AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA KARA DAUKAKA.

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
*******************

P40

      ......"idan Allah ya so ya yarda Ina son in yi bikin yara na da zarar su Amira sun gama makaranta,yanzu kawai iyayen Aleena na ke jira, su turo da sakon amincewar su Kinga shi ke nan,don ni haka kawai zuciya ta ta amince da su especially da na gansu,suma yaran akwai tarbiyya,ko ba haka ba my love"Dad ya gama fa'da wa mom tare da zungurar ta don tsokana."

Mom tayi murmushi don har cikin ranta taji da'di,"to Allah ya nuna mana yasa muna raye,Sai dai Kuma akwai wani abu fa na daban kaga ga yarinyar nan Amatullah tana zaune wai zaman jiran Ashfaq takeyi dani ban ma San abinda zanyi ba fa!!" To shi dai ya gaya miki ya Kuma rantse duk ranar da aka saura mishi aure da Amatullah a take zai yi mata saki uku, to Kinga me akayi ke nan Sai zumunci ya lalace ai,ki bari kawai Allah zai zaba mata nafi alkhairi agareta.don gaskiya Ashfaq ba karamin so ya ke yiwa Aleena ba amman saboda shakiyanci wai bai so ya nuna mata don kada ta raina shi. Sai duk suka sa dariya.

Dad ya Kara cewa "na ma Kira santa na gaya mishi yayi farin ciki sosai yace duk abinda na yanke shi kawai za ayi in tsara komai na game da namu bangaren ku Kuma kwayi naku"

To Allah ya Kai mu anjima zan Kira Umman na ji muma yadda za muyi.
*********
Ashfaq ya kalli Aleena da ido can kasa kasa yace "Mom da Dad suna so Su ga nayi aure sun matsu sosai mutuka don ko da yaushe hankalin su a tashe yake akan batun auren nan wai ace ni Ashfaq ko budurwa ma bani da ita balle har a zo maganar biki,ni Kuma bana so na rinka ganin su cikin wannan halin"ya karasa tare da langwabar da kansa yayi kalar tausayi.

"To Kai ba sai ka nemi wata budurwa kuyi soyayya Sai kuyi aure"ta fa'da tana hararar sa.oh lallai mayarinyar nan ni kike hararar ko,tunda na hanaki da baki bari kiyi da ido ko?to in baki sani ba Shima Ina da maganin sa idan kika Kara zaki ga abinda zanyi masa.

"Bari dai ki ji yanzu taimakon da nake so kiyi mini shine,so nake yi murinka pretending a gaban kowa da sunan soyayya muke yi ni da ke,ki rinka nuna min kina so na irin sosai din nan,nina zan rika nuwa Ina sonki ninkin baninkin akan san da zaki nunamin,domin da gaske INA SON KI SOSAI ALEENA"ya kare sa fada tare da shigar da idanun sa cikin idanunta. Aleena Sai da ta ji ragagagaaaaa gaban ta ya fa'di jin kalmar da Ashfaq ya gaya mata bata san lokacin da tace mishi da gaske kake kana so na ya Ashfaq?

Ya 'dan Kara gyara rike hannun ta yace "yes Aleena na da'de Ina son ki Aleena son da nake miki bazan iya kwatanta miki shi ba,ya ja hannun ta ya dora a daidai saitin zuciyar shi babu wata 'ya mace acikin nan Sai ke,ke ce farin cikina da nake mafarkin na rayu da ke ki haifar min yara na kyawawa kamar ki,I hope zaki amince dani a matsayin abokin rayuwarki?,sannan yace Ina so idan kin je gida idan su abba sun tambaye ki kina so na don Allah ki amsa musu da cewa eh kina sona pls🙏 don komai ya zo cikin sauki har zuwa lokacin da gaskiya zata bayyana ,in ba haka ba su mom din ki sun rinka shiga cikin damuwa ke nan har ta zo ta samu blood pressure kin ga ai ba zakiyi fatan haka ba ko?" Ta dan daure tace yanzu wadannan abubuwan da ka gayamin da gaske kake ko duk acikin pretending din ne?

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now