page 35

1.2K 70 9
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA


BISMILLAHI RAHMANU RAHIM


AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION


ALLAH KA JIKAN MAHAIFIYA TA DA SAURAN 'YAN'UWA MUSULMAI BAKI DAYA.

ALLAH KA BAWA MAHAIFINA LAFIYA KA SAUKAKA MASA.

ALLAH KA RAYA MINI YARA NAKA BASU ILMI MAI AMFANI.

MALLAKAR JAMILA (maman amir)

WATTPAD jami1020
******************

P35

.....Aleena tana sandare 'kyam yadda Ashfaq ya tafi ya barta a wajen,tama rasa a wani yanayi take ciki,ga wata irin kunya da ta kamata,Kar dai ace tayi staining ne shine shi Kuma wannan 'dan sa idon ya gani mtssss! Tayi tsaki.sai Kuma tayi sauri ta zabura ta kwance zanin ta,Sai kuwa gashi tayi staining Amman 'dan ka'danne fa,shine don mugun sa ido Sai da ya gani,"oh na shiga uku ni Aleena yanzu ya zanyi?"ta fa'da a fili.don a yanzu haka ko pad babu ajikin ta saboda tasan a ranar da ya zo mata,batayin rushing Kai ko pad bata sawa amman yau Sai gashi ya bata kunya.(ni ko nace in banda abinki Aleena ko da kinsan baya zubowa da yawa tunda dai fita zakiyi wani waje ai 'kya saka pad saboda baki sani ba ko a ranar a Sami akasin haka, to gashi kuwa).

Mom dai tags shurun yayi yawa,ga yunwar da suke ji.  "Ke Amira je ki dubo min 'diyata me ya same ta ne,me ya ke faruwa? Amatullah ta saki tsaki tare da cewa " Wai duk kun bi kun damu da wata bakuwar yarinyar,daga zuwan ta gida dik ta bi ta shi ranku,ni bansani ba ma ko asiri tayi muku don ni dai bai kama ni ba "

Ashfaq da ya ke cin abinci ya daka ta da cin abincin da yake,ya kalle ta tare da ha'de fuska kamar bai ta'ba murmushi ba yace"ke ji nan wannan shine na farko Kuma na karshe da zaki yiwa mahaifiya ta tsaki,ita ba sa'arki bace, wallahi wallahi kinji na rantse da Allah idan kika Kara yi mata mai kwatar ki a wannan rana Sai Allah don Sai na lahira ya fiki jin fa'di" ya buga tsaki ya tashi ya bar wajen,saboda abun ya zafafe sa ba ka'dan ba,don shi Bai yarda ko da wasa a ta'ba iyayen sa ba balle har ranshi ya 'baci.don ya san muhimmancin su.

Dad dai bai ce komai ba sai Shan tea din sa yake yi but cikin zuciyar sa Yana Kara son yaron shi,don Yana mutukar girmama su da yi musu biyayya dukka da cewa suna sakar masa fuska tamkar wasu abokanan shi Amman hakan bai sa ya rena su ba sai ma kara girmamawa a tsakanin su.(a nan Ina Kara janyo hankalin iyaye da su rinka Jan yaran su a jikin su,su rinka nuna musu abubuwa masu kyau da marasa kyau,sannan Kuma su rinka aikata abu Mai kyau a gaban yaran su Kai ko da a bayan idan su ne ta haka ne suma yaran za su saki jikin su a wajen iyayen su,su rinka daukar kyawawan halin iyayen su  suyi kiyi da su,su Kuma rinka fadawa iyaye damuwar su.Allah ka bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya ka Kuma bamu yaran da za su yi mana biyayya mu ma).

"Gaskiya anti Amatullah abinda kikayi Bai dace ba fa"in ji Amira. "Ke wannan a yayarki a ce Zaki gaya mara magana,tunda dai yayan ku yayi mata fa'da ba shike nan ba,ki wuce ki kirawo Aleena ta zo mukarya ji yadda lokaci ya ja amman har yanzu ba a yi breakfast ba a gidan nan." Sumi Sumi Amira ta wuce kitchen don ta kira Aleena.

Aleena dai tana nan a yadda ya tafi ya bar ta domin ta rasa abinyi, "sis Aleena me kike yi ne a kitchen ne har yanzu"  ....hmmm bakomai kawai.ya Zaki ce ba komai fun muna can muna ta jiran ki ki kawo ruwan wanke hannu,har dad ya Fara Shan tea.

"Amira dauki ruwan nan ki Kai musu don bazan iya fitowa ba fa." to saboda me? Nan ta bawa Amira labari cewa tayi staining Kuma tana jin kunya shi yasa. me Amira zatayi kuwa Sai dariya 'kyal...'kyal...  Oh Yanzu abinda zakiyi min ke nan sis Amira dariya ko? To nagode. Ok am sorry ai ke 'din ce wallahi fillon ki ya yi yawa,let's go to go to my room ki 'dan kim tsa Sai mu je mi ci na mu.

"Tab wallahi ba zan iya fita falo ba,Wai kinsan waye ya gayamin cewa nayi staining hmmm ya Ashfaq ne fa Kuma nasan Yana falon yanzu mtss" "..oh kice soyayya ku ka Sha ke dashi a kitchen din shiyasa ya da'de Mana lokacin da ya shigo,pls ki gayamin sirrin soyayyar nan ta ku mana nima na koya da nawa mutumin".

Aleena ta kawo mata dukan wasa ta goce tana dariya tare da daukar kwanu ta zuba ruwan tace Ina zuwa,bari na Kai musu yanzu zan dawo.ta karasa falon ta ajiye musu ruwan zata juya ke nan mom tace "tana Ina ne ita?" Hmm kin San ta mom da son aiki wannan ta ganin fa bamu Kara sa ba shi ne Wai Sai ta karasa sannan zata fito bari naje na taya ta don muyi Saurin gamawa.mom zata Kara magana amman tuni tayi sauri ta juya har da 'dan gudunta don kasa Mom ta tsayar da ita,sai ta yi murmushi kawai tace yaran yanzu Allah ya shirya mana amin.nan tayi serving dad da Amatullah ita ma tasa na ta suka Fara cin abincin,Dad yace " bari nayi Sauri na gama na Ashfaq ya rakani wajen abokina mugaisa " ok inji mom, Dad yace "ke ba fa sanata ba wajen sabon abokina Kuma suriki na zan je" oh to Allah ya taimaka.

Tana isa kitchen din tace oya juya in gani,Aleena ta juya bayan ta. Mtssss "wallahi na dauka ma irin staining 'din nan da ya maybe miki zani,'dan ka'dan ne fa,lallai ya Ashfaq to ya akayi ya gani? Amman ko ba karamin sa miki ido yayi ba ta karasa wata dariya " Aleena tace mata ke Kika sani kije ki tambaye shi Mana da Zaki kama kina tambaya ta.
*******
To ko ina labarin ashfaq,ya Kuma zata Kaya In sunje wajen Abba,shi a matsayin suriki zai je ko Kuma 'da ?

******

07038185042

Comment

Comment

Pls share,vote and follow me on my wattpad

Sorry for the late and short update,am very busy fans

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now