Page 17

1.1K 78 5
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Daga kungiyar jarumai writers association

Ya Allah ka haskaka kabarin mahaifiyata ka ba wa mahaifina lafiya

Allah ka daukaka musulunci da musulmi a duk in da suka ka kawo mana karshen Wannan hali da ake ciki

Sakon gaisuwa ta gareku masoyana both Whatsapp da wattpad ina jin dadi sosai

Mallakar Jamila(Maman amir)

Wattpad jami1020

P17

Bayan sallah isha'i ashafaq da amir suna kasa a falo gaba daya ana ta hira Wanda sai jefi jefi ashfaq ya ke sa baki a cikin hirar da sun hada ido da amir sai ya harare shi amir ya dauke idon sa yana murmushi sarai ya gano abokin nasa so yake ya tashi suje gidan su aleena ban hakuri yaki sai ja masa rai yakeyi amatullah kuwa sai kara shishshige masa takeyi yana amsawa da kyar don sai da mom tayi masa fada kwanaki akan yadda yake wulakan ta su Tana cewa menene laifi don suna son ka a hankali sai ka ganar da su tunda ba ka son su amman wulakanci bashi da kyau to shi ya sa dai yake ta daurewa yayi wa Amina magana ta kuma fahimta ta hakura amman ba wai don bata son sa ba ita amatullah ce dai take ta na ci

Zai tsaki ya keyi akai akai amir dai sai murmushi ya keyi da ya gama tsokanar ta sa sannan yace mom bari muje mu kara duba jikin Abban su aleena kai amman kuwa kun kyauta Allah ya shi muku albarka kuce ina yi masa sannu ina gaida hajiya Zainab din a kagauce ashfaq ya tashi mom sai mun dawo to Allah ya kiyaye amin ni daga can zan wuce gida na dauka nan zaka kwana ai yayi dariya kawai to ina gaida Umma OK mom

Suna fitowa waje ashfaq ya kai wa amir duka Dan iska ka na sane ai ka rinka bata lokaci sai ka jawo har sai sun rufe gidan wai  don Allah son yarinyar nan ka keyi ne ka gaya min gaskiya kai ni fa bansani ba fa ni bance ina son ta ba to me ya sa ka ke ke ta zumudin zuwa gidan su don kawai Na duba Abban su don ya bani tausayi wallahi hmmm in tayi wari ma ji idan na kira aleena waje sai Na Baku waje ka bata hakuri pls ban da wani fadan kuma naji amman kasan me wallahi gabana faduwa yake tayi fa wai me ke faruwa da ni ne amir shi dai amir kawai murmushi yayi don da alama ashfaq ya fara fadawa cikin soyayya soyayyar ma da alama mai zafi ce

Suna isa kofar gidan sukayi sallama daya suka kara yin sallama ummin su kamar sallama akeyi fa eh nima kamar naji haka bari naje na duba afnan kawo min hijabi na Tana kawo mata ta sa ta fita kofar gida ta leka a a su ashfaq ne ashe sannunku da zuwa sannu ummi ina wuni suka wani zube  a a Ku shigo daga ciki mana sai kace baki suna wani Dan sosa keya suka ce to ummi ta wuce ciki bayan kamar minti daya suka bi bayanta

Abban su ashe su ashfaq ne ma  a to maraba sannunku da zuwa suka kara so Abba ya nuna musu taburma kusa da su yace su zauna suka zauna ashfaq ko sai sunkuyar da kansa ya keyi kamar sun zo gaida surukai afnan kawo musu ruwa ko ta fito daga daki da pure water a plate ai tana ganin ashfaq ta sa ihu lahh ga mai kyau a gidan mu ga mai kyau a gidan mu kawai take gaban su ta ajiye ruwan ta wuce gaban sa ta zauna ta juya wajen amir ta gaishe shi sannan ta juya ta gaida mai kyau tace tun ranan banganka ba sai yau kai da kace zaka shigo gidan mu to kawata ai na shigo dazu fa kina barci kai haba amman tana ji dadi yau ga mai kyau a gidan mu ya aiki yasa dariya sosai yace lafiya shi har cikin ransa yana son afnan to aku tashin ki koma Ku kara sa karatun sai ki dawo hmm ai kusa bari na gashi nasan yanzu ya aleena zata fara kwalla min kira sai na zo munyi karatu ita ko gajiya da karatun ba tayi afnan afnan ta zaro ido kunji ko hmm bari nayi Sauri naje mu kara sa shi kusa ashfaq har wani lumshe ido yayi jin muryar ta

Can dai ya dan nutsu ya dubi ummi yace wai menene yake damun Abba ne ummi ta danyi shuru tace tundai daga lokacin da ya fadi ya suma da aka ce shagon shi ya kama da Wuta ya sami hawan jini don min dade aasibiti ma to run sannan jiki ya ki dadi yana ta shan magani karshe dai wani likita ya taimaka mana ya rubuta mana wasu magunguna to kuma bamu samu mun siya ba to ummi ai da an siya din karshen ta a dace ta danyi murmushi tace maganin ne kudin su kam sai a hankali tayi shuru sai duk suma sukayi shurun don sun gano dalilin da yasa ba su siya ba babu kudin ke nan sai yace ba damuwa ummi Allah ya rufa asiri dukkan mu nan likitoci ne saboda haka gobe zan zo Na tafi da Abba asibitin mu ayi masa gwaje gwaje sannan mu San abinyi kai masha Allah mungode sosai Allah ya kara arziki Abba ma yace angode sosai Allah ya shi albarka don baya iya yin magana sosai can dai kuka ce to zasu tafi ashfaq sai zuba ido take aleena ta fito bata fito ba amir dai ya daure cikin wasa ya ce wai ina yaya aleena ne har zamu tafi bamu gaisa ba ko ba a gama karatun ba ne ummi tace hmm in dai aleena ce sai ta kai large goma tana karatun na. Bari na kira ta Ku gaisa to ummi bari mu kara sa wajen sai ta fito mu gaisa tace to badamuwa said da safen Ku

Bayan sun amsa da Allah ya kaimu ta shiga dakin ita kuwa aleena tanajin duk abun da ke faruwa taji dadi sosai da za a kai abban su asibiti sai dai kuma mamaki ne ya ishe ta na abinda taji daga karshe na tafita waje su gaisa a can da ta sa wa ranta ba Indi zata to kuma sai tayi tunanin kara ummi ta zargi wani abun shigowar ummi ta katse mata tunanin da takeyi aleena kije waje Ku gaisa da su ashfaq sauri sukeyi zasu tafi to ummi amman karki Dade kinji ki dawo na baki wani labari abinda kike a mafarki dai Zai faru in sha Allah to ummi ta gashi ta fita dama akwai hijab a jikinta

A can waje kuwa ashfaq ya matsu ta fito sai wani tsaki yake tayi kai don Allah ka dame ni da tsaki sai ka ce tsaka in ka kwantar da hankalinka yanzu zata fito sai sukaji alamar tahowa to ga tanan Ma sai ka nutsu ta fito da sallamarta cikin muryar ta mai dadi amir ya amsa yana cewa mu har mun gaji da jiranki sai kace wadanda suka zo zance ya fada yana dariya itama dariyar tayi don ta fahimci yana da tsokana da son barkwanci sabanin Wannan miskilin sai yace kai na manta bari na dauka Abu a cikin motata yayi gaba da sauri kamar gaske yana cewa kijirani fa ina zuwa ta ce to

Bayan ya tafi ya bar su shuru ba Wanda yayi magana shi yana jira ta fara gaishe shi don ta bude hangar hira tsakanin su ita kuwa tayi shuru tana ta sake sake a ranta ta ga mai shurun yayi yawa ta ja tsaki zata koma cikin gida yayi sauri ya rike gefen hijabinta cikin sanyi murya yace am sorry idan ba kya son na rike hannunki to ki tsaya plssss ya ja kalmar sai da taji gabanta ya dadi
***********

07038185042

Comment
Comment

Follow and vote for me on my wattpad

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now