page 18

1.1K 93 2
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

Bismillahir Rahmanur Rahim

Allah ka jikan mahaifiya ta da yanuwana da sukara su Allah ka haskaka kabarin su ka bawa mahaifina lafiya

Allah mun tuba ka yafe mana kurakuren mu da laifukan mu kasa mu cika da imani

Sakon gaisuwa gareku Khadija Khalid da sis ramlat mai dambu da mummyn shukura

Mallakar Jamila(Maman amir)

Wattpad jami1020

P18

Pls kar ki tafi ya kara maimaita mata gaban ta ya sake faduwa amman ta dake ta juyo ta kalle shi sannan ta kalli in da ya rike mata gefen hijab da sauri ya saki hijab din kiyi hakuri ya langwabar da kansa nasan tafiya zakiyi ne ni kuma bana so ki tafi har sai mun gama magana ita dai kawai kallon shi take tayi tana mamakin Wannan arrogant din ne yake cema ta tayi hakuri tab kai ka sani ramuwa ta zama dole ba ma sau daya ba

Kiyi hakuri da abinda ya faru tsakanin mu dazu wato kissing dinki da nayi wallahi ba da niyyar hakan nai ba kawai don na ji kin ce hakan shi ne ya fi bata miki rai ne shi yasa nayi miki haka kuma a karshe  akarshe ya dan tsaya nan inda inda saboda shi kan shi kunyar karasawa yakeyi hmmm a karshe na kasa controlling kai na saboda wasu abubuwa da na dinka ji ita kuwa tayi sauri ta sunkuyar da kanta wallahi tunda nake ban taba aikata irin haka ba akan kowa ko rike hannun mace ban taba yi ba sai ko patients dina da niyyar duba su to sai ko akan ki

Kiyi hakuri don Allah na tuba kan ta a sunkuye dai ba ta ce komai ba ita duk kunya ma take ji ta  matsu amir ya dawo don kawai saboda shi ta tsaya har Wannan yake ta wani zubar karya ita fa sai ta rama ko da sau daya ne,yanzu dai ta dan hakura kadan saboda  hakurin da yayi ta bata tace to zan iya tafiya ya matso gaf da ita ta dan matsa kadan ya kara matsowa to wai meye haka kakeyi ne ba komai kawai kar ki ta fi sai kin ce kin hakura kin yafe mini mtsss ta matsa har bayan ta ya taba bangon gidan su ta tsaya ya kara matsowa to kice kin hakura har tana jin iskar ba kinsa a fuskar ta yau na shiga uku da Wannan mutumin ina ga in bance na hakura ba ba zai bar ni ba ta fada a zuciyarta a fili kuwa cewa tayi na ji ta kau da kan ta na ji ba amsa bace kice kin hakura naji na hakura ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi har ta waigo ta kalle shi suka hada ido tayi sauri ta kau da kan ta to ka matsa daga kusa dani bai ce komai ba sai kallon ta yakeyi yau ni naji maye kawai sai ta sami kafarta ta daga ta taka kafar sa da karfi ai ko yasa kara ya matsa tare da sunkuya wa yana dafe kafar a guje ta wuce shi ta shige soron su ta rude kofa garam yasa sakata sannan ta jin gina da kofar tana mai da numfashi shi kuwa sai kawai ya kama murmushi har ya koma dariya saboda shi abin ma dariya ta bashi tace ga tsiwa ga tsoro ya rinka shafa kanshi yana dariya sai ya sami kansa cikin an nashuwa ya koma gida yana ta murmurshi shi kawai dadi ya keji

Nan ya iske amir da amira suna ta hira a jikin mota shi dai Wannan abun nasu yana bashi mamaki to ko dai ita ce wacce yake cewa yana so ne in tayi wari naji

Amir yana ganin shi ya kalli fuskar sa yaga sai washe baki ya keyi yace munafuki na tabbata son yarinyar nan yakeyi amman na tabbata ba zai yarda da hakan ba kai tsaye ya dai Romeo ina kabar Juliet din yayi murmushi ta shige gida sai kuma ya tsaya ya dan bata rai mai kake nufi da Juliet bana son haka fa a haf sai da ka riga ka amsa sannan zama wani fara borin kunya amira dai sai dariya takeyi kasa kasa don ka da ya ji ta ke shige ciki zamuyi magana da shi ba ka isa ba fa yadda kaje ka gama baka zancen da aleena ni ma ka bari sai na gama mtsss ya wuce cikin gida kawai ba zai biya ta tashi ba

Amira tayi sororo jin abinda amir yace wai zance to ko dai abinda take zargi cewa ya amir Santa yake yi haka ne ai kuwa da ta fi kowa farin ciki ya dai lil sis na ga kin shiga tunani sai ta dan wayance tace naji ai ka ce da ya ashfaq wai wai sai ka gama zance ni kuma nasan saurayi da budurwa ne kawai su keyin zance ko ya kura mata ido wato yar yarinyar nan so take takure ni ke nan wai nan wayo take son yi min don na fadama ta abinda ke zuciya ta hmmmm

Amira kalle ni nan kalli cikin ido na ta kalli idanun sa sai tai sauri ta sunkuyar da kan ta saboda wasu abubuwa da ta karanto a idanun na sa har wani lumshe su yake yi amira ina son ki ina kaunar ki bansani tun lokacin da na fara sonki ba kawai na tsinci kai tsindim cikin soyayyar ki na kasa gaya miki ne saboda gani nakeyi kinyi kankanta to yanzu kam lokaci yayi da ya kamata ki sani I LOVE YOU LIL SIS

Kasa tayi da kanta tana sakin murmushi finally dai na Furta da ake tayi mini wayyo and I hope you will not reject your brother ta kara sakin wani murmushin kiyi magana mana pls kuma ina so ayi komai da sauri pls kina gama secondary tunda saura 6 months ko ta daga kai sai wasa take da hannunta yayi murmushi yace Ga dukkan alamu dai nasa mu karbuwa ko ta daga kai toh na shiga uku ni amir yau kuma an koma mini maganar kurame ya rike kugu kamar mace tace kai ya amir suka sa dariya dukkan su
*********
07038185042

Comment
Comment


Kuyi hakuri na jina da ba kuyi ba bana dan jin dadi ne sannan ma da kyar nayi

Nagode da masu kira da texts tanks

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now