page41

1.2K 70 21
                                    

SOYAYYA KO SHA'AWA

BISMILLAHI RAHMANU RAHIM

ALLAH KA JIKAN IYAYENA KA GAFARTA MUSU KURAKURAN SU KASA ALJANNA CE MAKOMAR SU TARE DA YAN'UWANA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA.

SAKON GAISUWA TA GA DUKKA FANS DINA NIMA INA YIN KU BA IYAKA,MASU KIRA DA MASU TEXT😘

DAGA KUNGIYAR AL'UMMA WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA KARA DAUKAKA.

MALLAKAR JAMILA (Maman Amir)

WATTPAD jami1020
******************
Ban manta da ku ba Rashida bello,Maman Aslam,my besty, Aishatummulkhairi,Hafsat,comments dinku na girgizani❤️😘

P41

....... Alhamdulillah mintina sun wuce awanni sun wuce ranaku sun wuce,watanni sun wuce.gashi dai har an ci wajen wata biyar da da haduwar su,abubuwan sun faru acikin abubuwan da suka faru har da sa ranar bikin mutane hadun nan wato Ashfaq da Aleena,Amir da Amira.iyaye Sai shirye shirye bikin suke yi ta kowanne bangaren ba gidan su Ashfaq ba,ba gidan su Aleena ba,ba Kuma gidan su Amir ba.

Abindai gwanin ban sha'awa abin farin ciki,yadda iyayen nan suka hada kan su suke abu kamar 'yanuwan juna idan na kalle su Sai naji wani farin ciki na kama ni har nayi ta tunanin dama a wannan zamanin akwai wata alaka mai kyau tsakanin talaka da masu kudi,Sai kuma na tuna duniya tana da fa'di,akwai mutanen kirki da baza a rasa ba cikin su har da irin su Dad da Mom,da Kuma umma.

Don yanzu Mom ta sa Umman su Aleena da Umman su Amir suna zumunci duk da dai Umman su Aleena bata gama dakin jiki da Umman su Amir duba ga halin ki na ce matsayin su na talaka,duk da dai Alhamdulillah yanzu basa cikin wannan halin suna samun taimakon da yawa ta kowanne bangaren,kuma yanzu Abba ya Sami sauki sosai har yana fita kasuwa saboda Dad ya Kara bu'de masa wani shagon,kuma Sai Allah ya sawa abin albarka ga shagon yana ta cika.

Lokacin da zai bu'de masa Abba ya gardama ya ki yarda  da haka,a cewar sa taimakon ma da suka yi masa a rayuwar sa shi da iyalina sa ma ya wadatar Allah ya saka da alkhairi ya biya da jannatul firdausi.sai da aka haha wahala sannan aka shawo kansa ya yarda.gashi kam yanzu sun faso gari suma akwai rufin asirin,gidan su ma duk an gyara shi sosai don Sai da aka rushe wajen nan aka sake sa blocks a Kara ginawa kai ba dai abinda zance Sai Masha Allah.

Bakuma kowa ne solar wannan abun ba sai Mom,domin ita tayi tsaye akan komai(Ina Kira ga matan masu kudin mu da surinka taimako a ko da yaushe,in ma ke baki da hali to ki lurar da mijinki da yaranki,don da ana samun haka a unguwa da wasu yalakawanbasu kwana da yunwa ba,kuma Allah ne kawai yasan iya ladan da mutum zai samu anan gaba🙏)

nace kai Mom 'yar Aljanna ce.

Wata yarinya na gani kyakykyawa hadaddiya fara ce tas sanye da doguwar riga fara tas da Wando blue rataye da school bag da kaga shigar ta dai kasan tar makaranta ce.yanayun fuskar ta na kalla nasan cewa a gajiye take kuma da alama akwai abinda take jira,ga yara Sai tafiya suke yi ita tana tsaye har ya rage Sai Yan kadan a cikin su.

Sai ga wata far mota galleliya ta zo tayi parking kusa da ita,kai motar nan ta hadu wallahi dama Wanda yake ciki zai fito ya ce tana sona da naji da'di,ta ji wasu duba fa'da daga bayan ta,a zuciyar ta tace jarababbu masu son maza kawai tayi tsaki Sai ta dan matsa Baya kadan ta Kara kau da kanta.

Shi kuwa Annur ga ba daya Aleena ta tafi da imanin sa,gata kyakykyawa kuma yarinya,ya bi jikin ta da kallo yadda surar ta ta bayyana cikin uniform din nan tunda riga ce ko gwiwa bata kai ba sai wandon hijab din na irin dan karamin nan nebai rufe kirjinta da kyau ba

SOYAYYA KO SHA'AWAWhere stories live. Discover now